Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426
Bugu na 690
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Yau ce ranar Kudus ta Duniya:
Za a yi muzahara
|
A nan dai Nijeriya za a yi muzaharar a kusan dukkan manyan da'irori (birane) da suka hada da Kano, Zariya, Kaduna, Katsina, Bauchi, Gombe da sauransu a karkashin Wakilan Malam Zakzaky na garuruwan. Kamar dai yadda akan yi muzaharar a nan gida Nijeriya, haka ma ake yi a sauran manyan biranen duniya, inda akan yi jerin gwano na dimbin jama'a ana ba da take na nuna manufar muzaharar ta yin tir da Yahudawa da Sahanyoniyanci da rarraba kasidu da gangami da kona tutocin Isra'ila da Amerika. Imam Khomaini, Jagoran juyin-juya-halin Musulunci na Iran (KS) ne ya ware wannan Juma'a ta karshe a watan Ramadan da ta zama Ranar Kudus a wata sanarwa da ya fitar da ita a ranar 7 ga Agustan 1979. Kamar yadda sanarwar ta fito a Sahifa-yi Nur, sifili na 8, shafi na 229, ga abin da Imam Khomaini ya ce wa al'ummar musulmin duniya: "Da sunan Allah Mai rahama, Mai jin kai. Tun shekaru da dama da suka shude nake ta tunatar da musulmi kan hadarin da ke tattare da kasar mamaya, Isra'ila, wacce yau ta tsananta munanan hare-harenta kan 'yan uwa Palasdinawa maza da mata, wanda kuma musamman a kudancin Labanon, ta ci gaba da kai harin bamabamai kan gidajen Palasdinawa da fatan murkushe gwagwarmayar Palasdinu. Don haka ina kira ga musulmin duniya da gwamnatocinsu da su hada karfi da karfe don gutsire hannun 'yar mamayar nan da masu mara mata baya. Ina kira ga dukkanin musulmin duniya da su mai da Juma'ar karshe na watan Ramadan mai alfarma ta zama Ranar Kudus - da ma kuma lokaci ne na yanke shawara, kuma zai iya zama mai yanke shawarar makomar Palasdinawa - wani gangami da ke nuna hadin kan musulmin duk duniya, inda za su shelanta goyon bayansu ga hakkin 'yan uwansu musulmi. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya bai wa musulmi nasara a kan kafirai." Har ila yau a wani sakon na Imam Khomain, kwana daya kafin wannan sanarwar ayyana Ranar Kudus, ya yi karin haske kan manufar ware wannan Rana, kamar yadda ya zo a Sahifa-yi Nur, sifili na 12, shafi na 275 mai take 'Ku raya Ranar Kudus'. Imam Khomaini (KS) ya ce: Mutanen kirki su saurara, dukkan musulmi su saurara, Ranar Kudus rana ce da dukkan al'ummar musulmi ya kamata su tattaru gu guda su mai da hankali a kanta, su raya ta. Idan dukkan musulmi za su daga murya a Juma'ar karshe na watan alfarma na Ramadan, wacce ita ce Ranar Kudus, in duk jama'a suka mike suka yi jerin gwano kamar yadda suke yi a yanzu, wannan shi ne mafari da izinin Allah na taka burki ga wadannan lalatattun da kuma korar su daga kasashen musulmi. Amma musulmi akwai su da nuna halin ko-in-kula, mutane ba su son daukar matsaya, ba sa iya tashi su mike tsaye ko su yi jerin gwano (muzahara) kan wannan al'amari. Yayin da Isra'ila ta ga cewa kasashen musulmi kowacce kanta ta sani, Misira kanta ta sani, Irak kanta ta sani, sai ta rika fadada sannu a hankali. Kuma ku tabbata idan kuka ci gaba da nuna irin wannan hali na ko-in-kula, to kuwa Isra'ila sai ta dangana da kogin Euphrates, don kuwa Yahudawan Sahayoniya suna ikirarin cewa dukkan wannan yanki nasu ne. Dole ku dauki kwakkwarar matsaya a kansu. Idan kuma ya zamana al'ummar musulmi sun dauki matsaya a kan Yahudawan Sahayoniya, amma gwamnatocinsu sun yi hannun riga da su a kan haka, to dole su mauje bakunansu, kamar yadda al'ummar Iran suka mauje bakin Muhammad Riza (Sha). Shi kuwa Muhammad Riza ya fi karfin dukkan gwamnatocin kasashen musulmi, ya kuma fi su samun goyon bayan manyan kasashen duniya, amma duk da haka al'ummarmu ta mike tsaye, ta mai da Musulunci manufarta, tana daga muryar Allahu akbar, har ta kada gwamnatin da kuma iyayengidanta na waje. Kuma ko da wadannan iyayengidan sun hada karfinsu, ba za su iya cutar da wannan kasa da komai ba." Haka Imam Khomaini (KS) ya fada yau shekaru 26 da suka wuce, kuma ga shi hasashensa ya zama gaskiya, inda Yahudawa da sunan Amerika suka dangana har zuwa kogin Euphrates da ke Iraki. Ta daya bangaren kuma, ashe kenan gangamin Amerika da kawayenta da ake ta kulle-kullen yin sa, ba zai iya yi wa Iran komai ba. A wannan nahiya dai, wannan muzahara ta dauki wani sabon salo, inda maimakon a taru daga ko'ina a Zariya a yi ta, ana yi a kowace babbar da'ira, abin da ke nuni da cewa, da yake kowace shekara ana samun karin jama'a da ke shiga muzaharar, to watan wata rana irin wannan muzaharar ita za ta mauje bakunan azzaluman gwamnatocin wannan nahiya, kamar yadda Imam Khomaini ya yi ishara. Komawa babban shafinmu Komawa saman wannan shafin
| |
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International
|