Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426
Bugu na 690
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Babi na uku:
Ma'asumancin Manzon Allah (SAWA)
Ba shakka idan muka karanta irin wadannan Hadisan da ke cikin littafan Sahih, wadanda suka dushe darajar Manzon Allah (SAWA), za mu fahimci irin mummunar akidar da Banu Umayya suka dasa wa musulmi a kan Manzon Allah (SAWA), sannan suka yi ta gadar da shi, daga al'umma zuwa al'umma, har zuwa gyauronsu na wannan zamanin. Idan muka yi bincike a kan manufar wannan akidar tasu, za mu yi bakin ciki matuka, da tofin Allah-tsine a kan wadanda suka yi mulki a kan musulmi a zamanin mulkin Umayyawa. Mafi shahara a cikinsu, kuma Shugabansu shi ne Mu'awiyah Bin Abu Sufyan. Abubuwan da Mu'awiyah ya aikata, sun tabbatar da cewa, daidai da rana daya, bai taba yarda cewa an aiko Muhammad Bin Abdullahi, (SAWA) da sako daga Allah ba. Imaninsa, da sauran ire-irensa Umayyawa, kallon da suka yi wa Manzon Allah (SAWA) shi ne a matsayin wani mai sihiri, wanda ya yaudari jama'a har ya kafa daula, tare da taimakon talakawan da suka ba shi goyon baya. Za mu tabbatar da haka ne, idan muka yi dubi ga tarihi na gaskiya, da irin halayyar Mu'awiya, da sauran na tare da shi, da irin aika-aikar da ya yi a lokacin rayuwarsa, musamman a lokacin da yake kan mulki. Na tabbata dukkaninmu mun san ko wanene Mu'awiya, mun kuma san Mahaifinsa, Abu Sufyan, da Mahaifiyarsa, Hindu. Amma ga wadanda ba su sani ba, Mu'awiya, shi ne 'yantaccen bawa, dan 'yantacciyar baiwa, wanda ya bata kuruciyarsa a karkashin rundunar Mahaifinsa, yana tattara dakarun da za su yaki Annabin Allah (SAWA). Amma a lokacin da wannan aniya tasa da shi da Mahaifinsa ta kasa yin nasara, kuma suka kwashi kashinsu a hannu, babu shiri suka shiga Musulunci, domin gudun kada su sha kaifin takobi. Daga nan saboda tausayi da jinkai na Manzon Allah (SAWA), sai ya yafe musu, kuma ya kira shi da 'Yantaccen Mutum." Amma kuma, bayan wafatin Manzon Allah (SAWA), sai wannan hali nasu ya soma fitowa fili, musamman saboda yadda Abu Sufyanu, ya soma shirya wa addinin Allah makarkashiya, da kokarin ganin ya bice hasken da Manzon Allah (SAWA) ya kawo wa al'umma. A cikin littafin Tarikh na Tabari, juzu'i na 11, shafi na 357, da kuma littafin Muruj-Al-Dhahabi na Mas'udi, juzu'i na 1, shafi na 440, sun fallasa irin makirce-makircen Mu'awiya, da Mahaifinsa Abu Sufyan a kan Manzon (SAWA) da addinin Musulunci. Akwai wata rana da Abu Sufyanu ya saci jiki a cikin dare, ya je wurin Imam Ali (AS), ya same shi, inda ya soma ingiza shi cewa, ya kamata ya tashi tsaye ya yaki Abubakar da Umar, wadanda suka haye kan hakkinsa da Allah da Manzonsa suka ba shi, sannan kuma ya yi masa alkawarin cewa, idan har ya yarda zai yake su, to shi kuma zai ba shi taimakon dukiya da sojoji. Amma kuma saboda sanin makirci irin na Abu Sufyanu, sai Imam Ali ya yi watsi da wannan tayi da ya yi masa, domin ya san manufarsa wargaza kan musulmi ne. Haka nan Abu Sufyanu ya ci gaba da shirya wa addinin Musulunci makarkashiya da gadar zare, har zuwa lokacin da Dan Amminsa, Usman ya haye kan karagar shugabancin musulmi. Kuma a wannan lokaci ne kiyayyarsa, munafuncinsa, da rashin yin imaninsa da Musulunci suka sake fitowa fili. Har da akwai lokacin da (Abu Sufyanu) yake cewa: "Ku kwace, kuma ku sake kwacewa! Na rantse da abin da Abu Sufyanu ya saba rantsewa, babu wuta, kuma babu Aljanna!" Ibn Asakir ma ya ruwaito a cikin littafinsa na tarihi, a juzu'i na 6, shafi na 407. An samo daga Anas cewa: Abu Sufyanu ya ziyarci Usman, a lokacin ma ya makance. Yana zuwa gare shi, sai ya tambaye shi ya ce; "da akwai wani ne a kusa da mu?" Su kuma suka amsa masa da cewa "babu kowa." Daga nan sai Abu Sufyanu ya ce; "Allah ka mayar da wannan daular kamar yadda take a lokacin Jahiliyya, kuma ka sanya Banu Umayya su mallaki kasa." Idan kuma muka waiwaya ga dan Abu Sufyanu, wato Mu'awiyah, irin aika-aikar da ya aikata ga al'ummar Annabi Muhammad (SAWA) a lokacin da ya dare karagar mulki da karfin tuwo ba za su misaltu ba, da kuma lokacin da yake Gwamna a Siriya. Tarihi na gaskiya, ya ruwaito yadda Mu'awiyah ya keta alfarmar Alkur'ani da Sunnar Manzon Allah (SAWA), sannan kuma ya ketare iyakokin shari'ar Musulunci. Ba shakka munanan ayyukan da ya yi wa Musulunci, sun fi gaban alkaluma su rubuta, haka nan sun fi karfin harsuna su yi bayani. (A saboda yadda 'yan uwanmu musulmi Ahlus Sunna Wal Jama'a suke da tsananin kauna ga Mu'awiya, har suna ba shi kariya, da neman Allah ya yarda da shi, mun ware shafuka na musamman a nan gaba domin yin bayani a kansa. Shi Mu'awiyah Dan Abu Sufyanu, imaninsa a kan adddinin Musulunci, da Manzon Allah, (SAWA) iri daya ne da na Mahaifinsa. Mahaifiyarsa Hindu kuma, kamar yadda Zamkhashari ya ruwaito a cikin littafinsa mai suna Rabi-Al-Abrar, juzu'i na 3, da kuma littafin Bab-Al-Qarabat-Wal-Ansab, cewa, ita sananniyar wadda ta shahara ce a fagen sabon Allah. Haka nan kuma, Mu'awiyah, ya yi gadon halayyar fuska biyu, irin na Mahaifinsa. Sannan ayyukansa daga baya, sun tabbatar da cewa bai taba yarda cewa shi musulmi bane ko daidai da rana daya, kamar yadda shi ma ayyukan Mahaifinsa suka nuna a zahiri. A cikin littafin Al-Mufaqqiyat, shafi na 576, da littafin Muruj-Al-Dhahab na Al-Mas'udi, juzu'i na 2, shafi na 341, da littafin Nahjul-Balgha, juzu'i na 5, shafi na 130, da kuma littafin Al-Ghadir, na Allama-Al-Amini, juzu'i na 10, shafi na 283, duk sun kawo cewa; Al-Zubair Bin Bakar ya ruwaito cewa, wani bawan Allah mai suna Mutawwaf Bin Al-Mughira, Bin Al-Thaqafi, ya ce: "Nakan ziyarci Mu'awiyah tare da Mahaifina, sannan kuma wasu lokutan yakan je shi kadai, kuma idan ya dawo yakan gaya min abin da ya ji daga gare shi. A lokuta da yawa, yakan gaya min irin girman kan Mu'awiyah, da kuma yin mamakin abin da yake ji, kuma yake gani a duk lokacin da ya kai m asa ziyara. "Wata rana, a lokacin da Mahaifina ya dawo daga wurin Mu'awiyah kamar yadda ya saba, sai na ga ransa bace, har ya kasa cin abincin dare. Daga nan sai na yi jinkiri, ina tsammanin ko nine na yi masa wani laifi da ban sani ba. Daga nan na tambaye shi na ce 'ya Mahaifina, menene ya faru a gare ka na ga tunda da yamma hankalinka yake a tashe?' Sai ya amsa min da cewa 'ya dana, hakika na dawo ne daga mafi sharrin al'umma, wato Mu'awiyah.' "Na tambaye shi abin da ya sa ya gaya min haka. Ya amsa min da cewa; 'a lokacin da nake tare da Mu'awiyah, daga ni sai shi, na ce masa, ya Shugaban muminai, tunda ka cimma burinka na shugabancin al'ummar musulmi, to ya kamata ka yi adalci, sannan ga shi ka tsufa, ya kamata ka kula da Banu Hashim, kuma ka sake karfafa zumunta a tsakaninku. Na rantse da Allah, ba su da wani abu da za ka kyamata daga gare su, sai dai abin da za ka rika tunawa, sannan kuma ka sami lada.' "Ko da na gayawa Mu'awiyah wannan zance, sai kuma ya ce: 'Na fi gaban haka, na fi gaban haka. Wani abu ni zan bari da za a rika tunawa da ni?' Mu'awiyah ya ci gaba da cewa; 'Dan uwanmu Abubakar ya yi mulki, ya shuka adalci, kuma ya aikata abin da ya aikata, amma yana mutuwa aka manta da shi, sai wadanda idan suka tuna da shi sai su ce Abubakar. Haka nan kuma dan uwanmu Umar ya yi mulki mai tsanani na shekaru goma, amma yana mutuwa aka manta da shi, sai idan an tuna da shi ake cewa Umar. Sai kuma dan uwanmu Usman ya yi mulki, ya aikata abin da ya aikata, shi ma sun aikata masa abin da suka aikata, amma yana mutuwa suka manta da shi, da abin da aka yi masa. "Mu'awiyah ya kammala da cewa; 'amma su kuwa 'yan uwan Hashim, a kullum suna kururuwa sau biyar a rana suna cewa, 'mun shaida Muhammad Manzon Allah ne.' To, wani tunawa za a yi wa mutum kamar haka? Sai dai kawai idan ya mutu a turbude shi a cikin kasa." Hakika Allah ya kunyata Mu'awiyah Bin Abu Sufyanu, domin dukkan kokarin da ya yi na ganin an manta da ambaton Manzon Allah (SAWA) bai yi nasara ba. Ya yi amfani da duk wani abin da yake da shi domin samun wannan dama, amma duk bai yi nasara ba. Mu'awiyah, Allah yana kallon dukkan abin da ka aikata, domin shi ne ya gaya wa Manzonsa (SAWA) cewa; "MUN DAUKAKA AMBATONKA." Allah ya cika haskensa duk kuwa da irin makarkashiya da munafunci, da kuma cogen da ka yi a cikin addininsa. Ka yi mulkin yammaci da gabashi, amma kana mutuwa aka manta da kai. Duk wanda ya tuna da kai, idan har ya san gaskiyar abin da ka aikata, yana tunawa da irin aika-aikar da ka aikata ne domin ka ruguza Musulunci. Za a rika tunawa da Muhammad Dan Abdullahi (SAWA), kuma dan uwa ga Banu Hashim, daga karnoni zuwa karnoni, daga al'umma zuwa al'umma, har lokacin da Allah zai tabbatar da addininsa a bayan kasa, da mutanen da za su gaje ta. A duk lokacin da aka ambace shi, za ka ji ana yi masa salati, tare da Iyalan gidansa tsarkaka. Wannan abu ya tabbata, kuma zai ci gaba da tabbata har karshen duniya, duk kuwa da makarkashiyar Mu'awiyah, da 'yan uwansa Banu Umayya. Maimakon makircinsu ya rage wa Manzon Allah da Iyalan gidansa daraja, sai ma darajarsu ta kara daukaka. Tabbas Mu'awiya za ka gamu da Allah a ranar kiyama, dangane da abubuwan da ka kirkira a cikin addininsa, kuma zai yi maka hukuncin da ya dace kai. Idan kuma muka waiwayi dansa, Yazidu Bin Mu'awiyah, mai abin kunya, mashayin giya, wanda ke takama da sabon Allah a fili, za mu ga cewa ya yi gadon halayya irin na Mahaifinsa Mu'awiyah, da Kakansa Abu Sufyanu. Da a ce bai yi gadon wadannan munanan halaye ba, da Mahaifinsa Mu'awiyah bai dora shi a kan shugabancin musulmi ba. Dukkaninsu, sun san halayensa a lokacin da yake raye, musamman dan Husaini Bin Ali, Shugaban Samarin Aljanna (AS). Babu kokwanto cewa, Mu'awiyah ya tafiyar da rayuwarsa, sannan ya karar da dukiyar da ya tara wajen kokarin rusa Musulunci. Mun ji yadda ya yi kokarin binne ambaton Manzon Allah (SAWA). Da bai yi nasara ba kuma ya shirya yaki da dan uwan Manzon Allah, Ali Bin Abi Talib. Sannan kuma ya sunnata wata tsinanniyar sunna ta la'antar Ali Dan Abi Talib, har ma ya umurci gwamnoninsa na kowane sashe, su rika la'antar Ali da sauran Iyalan gidan Manzon Allah (SAWA) a kan mumbarorin salla. Ya yi haka ne a kokarinsa na la'antar Manzon Allah (SAWA). A cikin littafin Al-Aqd-Al-Farid, juzu'i na 2, shafi na 301, Ibn Abd Rabbih ya ruwaito cewa, Mu'awiyah ya sunnata la'antar Imam Ali a kan mumbarorin salla, kuma ya rubuta wa dukkanin gwamnoninsa a lokacin, ya ba su umurnin su ma su rika la'antar Imam Ali a lokacin salla, kuma suka yi hakan. Har Ummul Salama, matar Manzon Allah, ta rubuta wa Mu'awiya wasika, tana ce masa; "Kana la'antar Allah da Manzonsa a kan mumbarorin salla, domin kana la'antar Ali da masoyansa! Na rantse da Allah, kuma na shaida cewa Allah da Manzonsa suna kaunar Ali." Amma duk da wannan wasika da ta aika masa, bai daina la'antar Ali ba. Za mu ci gaba insha Allah. |
Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |