Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426
Bugu na 690
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
|
![]() Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky H. a F.I.C. Zaria |
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam mutum zai iya shiga i'itikafi a ran 19 ga watan Ramadan, kuma ya fito a ran 29 ga watan Ramadan?
Daga Saleh Shehu Yadin Lere, jihar Kaduna.
SHAIKH ZAKZAKY: Ka'idar i'itikafi dai shi ne, duk lokacin da ya kwana biyu, to kwana na uku zai ayyanu, saboda haka yana iya yin kwana 10 kenan, amma in har ya yi na 11, to na 12 zai zama lazim. Duk lokacin da ya yi kwana biyu, sai ya kawo na ukun. Wannan kuma bayan ukun farko kenan, tunda a wurinmu ba zai iya yin i'itikafi kasa da kwana uku ba. Bayan kwana ukun farko, duk lokacin da yi kwana biyu, to na uku ya ayyana. Nan kamar yadda ya ce, ya shiga 19 ya fita 29, ka ga ba ya sami kwana 10 ba? Ka ga zai iya yin kwana 10. Amma da zai yi 11 ne, da sai ya zama sai ya kara na 12. Da takwas ya yi, da dole sai ya yi na tara. Ka fahimta ai? Amma in ya yi 10 ba a ce sai ya yi na 12 ba. Duk lokacin da ya yi biyu, sai ya yi na uku.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ina hukuncin mutumin da ya yi rihi (tusa) a cikin salla, amma sai ya ki ya fita daga masallacin, sai ya ci gaba da kwatanta kamar yana salla saboda kada ya fita ya bar mutane cikin shakku?
Daga Abdurasheed Daudawa jihar Katsina
SHAIKH ZAKZAKY: Ba haka nan zai yi ba. Tunda ita salla ba ta inganta ba alwala, saboda haka bai halatta masa ya ci gaba da kwatanta salla, alhali ba salla yake yi ba. Abin da ya kamata ya yi shi ne, ya fita. Akwai wasu 'Fukaha' da suka ba da wata dabara ta cewa; sai ya kama hancinsa kamar ya yi habo ne. Kuma shi ma wannan dai hikima ce. Wato kenan sai mutane su dauka jini ne ya shiga gangaro masa, shi ya sa ya fita waje. Kodayake ba haka bane, sai ya je ya sake alwalarsa ya dawo, in ya samu ma ana nan ana salla din, sai ya bi ya samu jam'i na dan abin da ya saura, in ya samu kamar ko da raka'ar karshe ne, misali. Amma batun cewa in ya fita zai sa wa mutane shakku, wannan bai taso ba. Shakku na mene? Saboda sallarsa ai ba ta shafi wani ba, ballantana a ce… Yana shakkun mene da zai faru? Lalle wannan dai ba daidai ne ba, ya yi salla ba shi da alwala. Bilhasali ma ya haramta masa ya yi salla ba alwala. Saboda haka wajibinsa ne ya yanke sallar ya fita, sai dai wannan dabara din ta toshe hanci, za ta nuna cewa ba wani abin kunya bane, habo ne ya gangaro. Kodayake bai zama dole ba, ko da ya fita, ai mutum yake shi, kuma abin da ke bijiro wa dan Adam, yana iya bijiro masa.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam wasu suna cewa idan mutum ya tara da matarsa a dakin da yake akwai yaro karami ko da yana barci ne, sai yaron ya zama fasiki. Ya wannan yake a mazhabar Ahlul Baiti? Idan kuma haka ne, ya mutum zai yi kenan da yake ana cikin wani hali a wannan kasar ta yadda mutum yake kwana da matarsa a daki daya da kuma yara da yawa.
Daga Abdulrasheed Daudawa Katsina 0805 471 0211
SHAIKH ZAKZAKY: Abin da dai aka sani haramun ne yin jima'i tare da yaron da yake iya hankalta, ko da kuwa yana barci ne. Yaron kuma ana cewa kamar daga dan shekara biyu zuwa sama, in zai iya fahimtar abubuwa, amma idan kamar mai shan nono ne, babu laifi da wannan.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ana neman taimako ne na gina masallacin Juma'a sai kwamitin neman taimakon ya ce mutum zai iya ba da zakkar amfanin gonarsa ga masallacin. Shin Malam hakan yana iya halatta?
Daga Hamza Idiris Iliya Gombe
SHAIKH ZAKZAKY: Ana iya cewa eh, ta fuskacin fisabilillah, don ana cewa kason fisabilillah yana zama duk wani abu domin amfanin al'umma. Amma wannan sai idan babu fakirai mabukata, sannan za a je ga haka nan. Amma idan akwai fakirai mabukata, sune suka fi cancanta, fiye da gina masallaci, ko makaranta, ko abin da ya yi kama da haka nan.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Da yake Malam ya fadi hukuncin yadda za a yi idan mutum ya tafi ya bar gida bai dawo ba har na wani lokaci. To Malam idan mutum din ya tafi kuma sai aka fid da ran ba zai dawo ba, sai bayan matarsa ta auri wani, 'ya'yansa sun raba gado har ma wasu sun sayar wa wasu nasu kason da suka samu, sai kuma wannan mutumin ya dawo. Ya za a yi kenan?
Daga Muhammad Ango Dosara jihar Zamfara
SHAIKH ZAKZAKY: Ban san ko har na ba shi labarin rabon gado ba? Kila shi ne ya kara da rabon gado, domin kuwa hukuncin 'mafkudi' daban yake kuma da rabon gado. Batun hukuncin aure na hukuncin 'mafkudi' daban yake da rabon gado. Na aure ana cewa bayan shekara hudu ne ana cigiya, to sannan za a yarje mata ta yi idda, idan ta gama idda, sannan tana iya aure. Shi kuwa rabon gado ba a ce za a yi shi nan take ba. Sai an masa mikidarin shekara 70 daga lokacin haihuwarsa, to sannan ne ake iya raba gado. Saboda haka ka ga hukuncin aure ya bambanta da na gado. Kuma in ya zama duk an yi wadannan, sai mutum ya dawo, falillahilhamdu, amma waccan maganar an riga an gama. Matar ta riga ra yi aurenta, shi kenan alhamdulillahi ba wata magana. Kuma gadonsa an riga an ci alhamdulillahi, kuma alhamdulillahi yanzu da ya dawo.
Don haka idan an ce ta yi aure, ba ana nufin kuma a raba gado bane. Shi rabon gadon hukuncinsa daban ne. Shi sai an kiyasta ya shekara 70 daga lokacin da aka haife shi, ba daga lokacin da ya bar gida ba, in an ga cewa bayan shekara 70, to shi kenan ana iya raba gadonsa. In ya dawo kuma falillahilhamdu. Amma dai wannan ya riga ya wuce, ba sai a dawo masa da kayansa, ko a dawo masa da matarsa ba, yanzu ya riga ya wuce.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam idan za a kai gawa makabarta a gaban mutane ya kamata ta kasance, ko kuwa a baya?
Daga Ashiru Salisu Babbar Riga
SHAIKH ZAKZAKY: Wasu suna cewa ya kamata wasu su yi gaba ne kadan, wasu kuma su yi baya. Sai ya zama akwai mutane a baya, akwai kuma mutane a gaba. Amma abin sani dai ana sa shi a gaba ne. Sai dai akwai masu cewa ya kamata wasu su riga shi zuwa kabari din, don ya zama kamar ba an kai shi da sigar girmamawa bane, an je da shi ne da sigar ana nema masa rahama ne. A cikin 'adab' ladubban raka gawa kabari, akwai cewa ana sa gawar a gaba ne a bi ta. Amma akwai masu cewa tunda ana nema masa rahama ne, kar a nuna shi a gaba tamkar ana girmama shi, sai wasu su riga shi zuwa kabarin, su wuce gaba kenan, da fatan su je su fara addu'a kafin a iso da shi.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam wani dan uwa ne yake da 'ya da ta isa aure, sai wani dan uwan ya nuna yana son ta zai aura, bayan an yi duk binciken da ya kamata, an gamsu da shi, ita ma yariyar ta amince da shi, sai uban wannan dan uwan (Mahaifin yarinyar) ya ce, bai yarda wannan dan uwan ya auri wannan 'yar ba, saboda ya bincika ya gano shi dan Shi'a ne, amma sai uban yarinyar ya yi kokarin ya gamsar da shi, amma ya ki gamsuwa, wannan ya kai ga ya haifar da sabani a tsakaninsu. Aka yi auren ba tare da amincewar uban wannan dan uwan ba. Har ta kai ma sun kore shi daga gidan da suke zaune da shi. Me ya kamata wannan dan uwan ya yi kenan? A nan ya saba wa iyayensa ne da ya zama wajibi ya nemi gafararsu, ku kuwa ya abin yake?
Daga Muhammad Abuja
SHAIKH ZAKZAKY: Idan karama ce wadda ba ta balaga ba, waliccinta yana wajen ubanta da kakanta, kuma a wajenmu duk cikar su ikonsu daya a kan walicci din. Amma a bayanin da ya yi, ya ce ta isa aure, za mu kaddara yana nufin ta balaga ne, to a nan ita ce ta fi hakki fiye Mahaifinta da kuma Kakanta. Saboda haka zabinta za a fifita, har ma in ma su biyun duk suka ki, ta samu ma ta wakilta wani ya daura mata aure, kuma auren ya yi. Illa iyaka in ta ba su waliccin din ta girmama su ne.
Amma tunda akwai rashin fahimta tsakanin uba da da a nan kamar yadda ya fadi, to sai shi dan ya yi kokari ya sasanta da Mahaifinsa, ya nuna masa cewa wannan a shari'ar Musulunci ma dai ita yarinyar ita take da hakki ba su ba, kuma bai kamata wannan ya zama sanadiyyar sabani a tsakaninsu ba, har dai ya shawo kansa su ci gaba da zumunci. Amma dai auren da ya yi, ya yi daidai.
Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |