Almizan :Illar karya alkawari a ddinin Musulunci ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426                 Bugu na 690                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Hantsi:

Illar karya alkawari a ddinin Musulunci

AYYUKA

M utum yakan gane ayyukan da suka doru a kansa ne kawai idan ya kai matsayin bambance tsakanin kyakkyawan abu da mummuna. Daga nan ne zai yarda ya kiyaye dokokin tsarin rayuwa, ya kuma yi riko da kwararan ra'ayoyin da farin ciki da karkon bil Adama ya ta'allaka a kansu. A wani kaulin kuma mu ce yayin nan ne zai haifar da jituwa tsakanin halayyarsa da dabi'ar jikinsa da bukatun zuciyarsa.

Zartar da ayyukan jiki da na ruhi abu ne wanda hankali da hikima duk sun yi na'am da su. Hankali da hikima sun bukaci mutum da ya zage damtse ya tsaya daidai wajen neman abubuwan da ke jawo ci gaba, tare da yin Allah wadai da duk wani abu da ka jawo birkicewar tsarin rayuwa. Gudanar da aikin da ya doru a wuyan mutum yana matukar taka rawa wajen kyautata halayya da zuciya. Sabanin wasu akidodi, da suka ce aiki don sauke nauyin da ya doru a kan mutum ba bauta bane, bilhasali ma shi ne ainihin 'yanci. Aikata aiki kan jawo wa mutum tsarin halayya wanda ya daidaita da tsarin rayuwa mafi dacewa. Matukar mutum yana raye, to kuwa ayyukan da suka doru a wuyansa suna nan tare da shi, ko da kuwa ta fuskoki daban-daban ne. Abu mafi dacewa da ake bukata ga mutum kawai shi ne ya sauke nauyin da ya doru a kansa matukar yana da ikon saukewa, kuma yana kaunar ya aikata hakan.

Zaman kashe wando da saba wa ka'idar rayuwa, jahiltar asasin rayuwa ne da bude kofar rowa da halaka. Babu kuskuren da ya fi yi wa al'umma rikon sakainar kashi komar sa. Don haka tilas ne mu daina kawo wa jama'a cikas wajen sauke nauyin da ke kansu don kawai son zuciyarmu. Mutanen da suka zamo bayin son ransu suka gwammaci ayyukan da ke hannunsu wannan shi ne tushen rashin cin nasararsu da kuma gazawarsu su kai ko'ina a kamalar 'yan Adamtaka kwata-kwata.

Dokta Carl yana cewa: "Duk mutumin da ya dauki kansa a matsayin mai zaman kashe wando, to bai kai mikiya wadda da'iman take shawagi a sararin samaniya ba. Shi tamkar gujajjen kare ne wanda ya tsinci kansa a kan titi cike da motoci bai san inda zai nufa ba, ko kuma bai san yadda zai kubutar da kansa daga hatsarin da ke kewaye shi ba."

Ya ci gaba da cewa; "dukanmu mun san cewa halitta tana da wasu ka'idodi da take gudana a kansu. Lalle ne kuma mu gane cewa rayuwar mutum ma dole ne ta zamanto tana da ka'idodi da dokoki. Tsammani muke yi mu babu abin da ya hada mu da dabi'a, mu dai kawai muna aikata abin da muke so ne. Mun ki yarda cewa gudanar da rayuwa ba ta da wani bambanci da tuka motoci ta fuskar kasancewar dukkansu biyun suna bukatar a kiyaye wadansu dokoki. Gani muke tamkar cewa manufar mutum ita ce ya ci ya sha, ya yi barci, ya yi jima'i, ya mallaki mota da rediyo da dai sauransu…."

Kiyaye ka'idodi tilas ne a al'ummar dan Adam, kuma haka zai yiwu ne ta hanyar bin doka a kowane lokaci. Wadanda suka dogara a kan kokarin kansu za su dubi rayuwa da hasken idon basira da hikima, don haka za su iya jurewa su dauki nauyin da ya doru a wuyansu, sukan tsara rayuwarsu daidai da ka'idodi da hakkoki da kuma gaskiya, kuma suna sauke nauyin da ya doru a kansu ba tare da sun koka ba. Ko da mutum ya gaza a wani bangare, duk da haka zai yi alfahari domin wannan faduwar ba ta zo ba sai bayan ya jarraba sauke aikin da ya doru a kansa.

Tilas ne mu nemi farin ciki a cikin alheri na gaskiya. Sa'ada da kwanciyar hankali kan wadata masu bin shiryarwar hankalinsu da cin nasara. Sakayyar wadanda suka sauke nauyin da ya doru a kansu ita ce wadatar zuci da daidaituwa tsakanin hankalinsu da zuciyarsu. Wannan irin jin dadi kan tsiro ne daga zukatan wadanda suka gudanar da ayyukan da ke kansu suka sauke nauyin da ya rataya a wuyansu a rayuwa.

MUHIMMANCIN ALKAWARI DA ILLOLIN KARYA SHI

Cika alkawari yana daya daga cikin muhimman al'umuran rayuwa da ya doru a wuyan mutum. Dabi'ar mutum ne ko da wane addini yake bi ya ji bacin rai idan ya karya alkawari, murna da farin ciki kuma sukan lullube shi idan har ya cika alkawarinsa, sawa'un wani mutum kwara daya tal ya cika wa alkawarin, ko kuma al'umma baki dayanta. Irin tarbiyyar da aka taso da mutum a cikinta tana taka rawar a-zo-a-gani a halayyarsa da za su biyo baya. Don haka ne wajibcin yin taribiyya ta gari da kiyaye dorewarta da nisantar abubuwan da za su lalata halin mutum ya zama abu ne da babu ka-ce-na-ce a kai. Kyakkyawar tarbiyya ita ce mabudin kamalar halayen kwarai.

Mutunci ya wajabta cika alkawari ko da kuwa na baki ne wanda aka kulla tsakanin bangarori biyu, ko da kuwa babu wata rubutacciyar hujja. Karya alkawari yana jawo ficewa daga da'irar daraja da mutunci. Ketare haddin wa'adin da aka yi alkawari shi ma rashin mutunci ne.

Buzarjumehr yana cewa: "Karya alkawari yana matukar nisanta tsakanin mutum da mutunci."

Duk wanda ke kauce hanya madaidaiciya, ta hanyar karya alkawari cikin sauki, to, yana shuka kangarewa ne da kyama a zukatan wasu. Sannu-sannu mai karya alkawari zai kunyata ya yi kokarin nade tabarmar kunyarsa ta hanyar kame-kamen dalilai da warware tukkar da ya yi, har daga karshe mutane su gane cewa dai shi dama mutum ne batacce, munafuki.

Babu shakka karya alkawari yana daga cikin abubuwa mafiya saurin kawo tangarda a al'umma da raunana dangantaka a tsakanin jama'a. Tabbatacce ne al'ummar da ke cike da gardandami da rashin yarda za ta sukurkuce a tsarin zaman jama'arta, kuma sakamakon haka mutane ba za su taba yarda su amince da kowa ba hatta danginsu na kusa.

Akwai wasu irin mutane da ba wai kawai suna yi wa alkawari rikon sakainar kashi bane, a'a, har ma tsammani suke yi karya alkawari wayo ne da iya shirya bilhu. Bilhasali ma har alfahari suke yi da aikinsu.

Cika alkawari yana da muhimmanci ga wanda yake kaunar ya zauna a cikin jama'a, shi ne kuma tushen farin cikin zaman tare da ci gaba da cin nasara.

An ruwaito cewa an kamo wasu jama'ar Hawarijawa a zamanin Hajjaj Ibinu Yusufus Sakafi aka kai su gurinsa don ya duba al'amarinsu. Sai Hajjaj ya hukunta su yadda ya so. Yayin da mutum na karshe ya gurfana a gaban Hajjaj don ya saurari hukuncin da za a yanke masa, sai lokacin salla ya yi. Da Hajjaj ya ji an kwala kiran salla sai ya danka mutumin ga wani na hannun damansa ya ce masa ya kawo shi da safe.

Sai mutumin ya fita daga fadar tare da fursunan. Suna cikin tafiya sai fursunan ya ce; "Ni fa ba ni daga cikin Hawarijawa kuma ina rokon Allah cikin rahamarsa ya bayyana rashin laifina a sarari domin an tsare ni ne ba laifin tsaye ba na zaune." Sai ya ce "ina rokon ka don ka ba ni izinin in je in kwana a tsakanin iyalina, matata da 'ya'yana ko na samu na ba su wasiyyata. Na yi alkawarin cewa zan dawo da asubar fari kafin zakara ya yi cara."

Bayan mutumin ya yi shiru na dan lokaci, sai ya amince da bukatar fursunan saboda tsanantawar da ya yi, ya sallame shi ya tafi na tsawon wannan daren. Jim kadan sai mutumin ya fara fargaba yana jimamin cewa Hajjaj zai huce haushinsa a kansa. Can tsakar dare sai mutumin ya farka yana ta jin tsoro, amma abin al'ajabi sai ya ji fursunan nan da ya ba wa izinin ya tafi gida ya komo yana kwankwasa kyauren kofar gidansa. Sai mamaki ya cika shi, kuma bai iya gimtsewa ba.

Sai ya ce: "Me ya kawo ka kofar gidana?" Sai fursunan ya ce: "Duk wanda ya yi imani da girman Allah da kurdurarsa, kuma ya sanya shi shaida a kan alkawarinsa, to, dole ne ya cika alkawarinsa."

Sai mutumin ya wuce da fursunan kai tsaye zuwa fadar Hajjaj, kuma ya fade masa labarin abin da ya gudana. Duk da cewa Hajjaj ya shahara wajen rashin tausayi, sai da gaskiyar wannan mutum ta yi tasiri a kansa, har ya sake shawara. Ya kuduri aniyar zai sake shi, can sai ya juya ga mutumin nan da ya kawo shi ya ce; "kana so in ba ka kyautar wannan kamammen?" Sai mutumin ya ce; "idan ka yi haka kuwa ai da na so kwarai." Sai ya ba shi kyautar sa. Shi kuma yana fita daga fada sai ya sake shi ya yi tafiyarsa.

Mu kaddara cewa akwai wani kamfani na kasuwanci wanda ba ya kiyaye ka'idodinsa, wannan babu inda zai kai shi illa ga rashin amincewa a gurin mutane da kuma karyewar kamfanin.

Babu wani abu da zai karfafa al'mma ta kankama gargar kamar amincewa da juna a tsakanin jama'a. Alaka tsakanin mutane ba za ta kankama ba, zukata ma ba za su amince da juna ba sai har idan kowane mutum ya dauki maganarsa da muhimmanci, kamar yadda yake ba wa ka'idodi da dokokin hukumar kasa muhimmanci, kamar yadda tajiri zai damka kayansa ga abokin cinikinsa, mabaraci kuma zai biya kudinsa ga wanda ya ba shi bashi da dai sauransu. To haka ne kawai za a warware rikice-rikice, kuma rayuwa ta mike yadda ya dace.

Don haka abin da ya fi dacewa ga mutum shi ne ya jinjina karfinsa tukuna kafin ya kulla wani alkawari, kuma ya nesanci kudura duk wata yarjejeniyar da ba shi da ikon zartarwa. Idan mutum ya yi alkawari ya zo bai cika ba, ko da a sakamakon gazawarsa ne, duk da haka shi nauyin a wuyansa ya rataya. A bisa dabi'a shi za a zarga, a soka.

MUSULUNCI YA HANA KARYA ALKAWARI

Ya kamata mutum ya tsara shigi-da-ficensa ya zama ya dace da hankali domin sauran jama'a su sanya shi a sahun masu hankali. Muwafakar al'umma ta dogara ne kacokaf a kan hadin kan dai-daikun mutanenta. Don haka tilas ne kowa ya tsara rayuwarsa ta dace da gaskiya da hakika. Sa'an nan ya guje wa abin da zai haifar da rashin hadin kai da munafurci matukar iyawarsa. Idan har aka kulla alkawari da kiyaye shi a bisa asasin imani da halayyar kwarai da karimci, to shi ne mafi dorewa kuma mafi karfi.

Addinin Musulunci ya kushe karya alkawari matuka yadda bai yi sassauci ba ko kadan ga mabiyansa da su karya alkawari, ko da kuwa tsakaninsu da fasikai ne fajirai.

Imam Bakir (AS) ya ce:

"Abubuwa uku Allah bai yi sassauci ga kowa ba a kansu: Kiyaye amana ga mutumin kirki da fajiri, da cika alkawari ga na kirki da fajiri, da bin iyaye na kirki ne su ko fajirai."

Littafin Alkafi Juzu'I na 2 shafi na 169

Alkur'ani kuma ya siffanta masu imani da cewa:

" …… Wadanda su masu kiyaye amanarsu ne da alkawarinsu…." (Surar muminoon: 8).

Kazalika ya yi kira ga musulmi da su cika alkawarinsu, ya ce: "Kuma ku cika alkawari, lalle alkawari abin tambaya ne a gare shi."

(Surar Isra'ila: 244)

Manzon Allah (SAW) kuma ya kidaya alkawari daga cikin alamun munafurci, yana cewa:

"Akwai abubuwa hudu, duk wanda yake da su, to munafuki ne. Idan kuwa yana da daya daga cikinsu, to yana da alamar munafunci, har sai ya rabu da shi. Wato idan ya yi magana sai ya tsuga karya, idan ya yi yarjejeniya sai ya saba, idan ya kulla alkawari sai ya karya, idan kuma ya yi husuma da wani sai ya zake."

Imam Aliyu (AS) ya rubuta a cikin wasiyyar da ya yi wa Malik Ashtar cewa: "Ka kiyayi gori ga talakawanka, saboda alherin da ka yi musu, ko kuma ganin yawan abin da ka aikata, ko kuma ka yi musu alkawari, sa'annan ka biyo bayan alkawarin naka da sabawarka, domin gori yana bata kyakkyawan aiki, ganin yawan aikinka kuma yana dushe hasken gaskiya, sabawar kuma yana jawo kyama daga Allah da mutane. Allah subhanahu wata'ala yana cewa: "Babban abin kkama ne a gurin Allah ku fadi abin da ba kwa aikatawa."

Aliyu (AS) ya kara da cewa: "Cika alkawari dan tagwayen gaskiya ne. ni ban san wata garkuwa fiye da shi ba."

Addinin Musulunci ya ba da muhimmanci matuka ga tarbiyyar yara. Ya bayyana wa iyaye tilashinsu na halayyar kwarai filla-filla ta hanyar kwararan tafarkuna masu gamsarwa. Matukar iyaye ba sa kiyaye abin da ya kamace su dangane da halayen kwarai, to ba za su iya koya wa yaransu riko da halayen kwarai ba. Domin aiki ya dara batun baka. Saboda haka ne Manzon Allah (SAW) ya hana iyaye karya alkawarinsu ga 'ya'yansu. Ya ce: "Kada wani mutum ya yi wa dansa alkawari sa'annan ya karya."

Dakta Alindi kuma ya ce: "An kawo mini wani saurayi dan shekara goma sha shida da yakan yi sata kulluyaumin don in yi masa magani. Sai na gano cewa a lokacin da yaron yake da kimanin shekara bakwai ko takwas, babansa ya taba tilasta shi ya ba wa 'yar tajirin da yake masa aiki abin wasansa. Wannan abin wasa kuwa a gurin wannan yaro shi ne abu mafi kima da daraja, domin sai da ya kare dukkan kokarinsa ya wahala sa'annan ya same shi. Mahaifin yaron ya yi alkawarin zai saya masa wani ya ba shi a madadin wancan, amma sai ya manta ba da nufinsa ba. Don haka yaron bai ga mafita ba illa ya saci 'yar cakuleti daga aljihun babansa ya dau fansa. Daga nan bayan kwana daya, sai ya kurda gidan makwabta ya fasa gilashi ya sato wani abu. Don haka warkar da wannan yaro ba ta yi mini wahala ba, na ci nasara a kan haka. Uban wannan yaro shi ne ya shigar da shi wannan hanya sabili da ya yi wa dansa ba daidai ba. Kuma idan da ba don an magance al'amarin sosai ba, har ya ci gaba da yin haka, to da yaron yana iya zamowa wani rikakken mabarnaci mai hatsari, alhali yana da damar wata rana ya zamanto babban mutum mai hankali da karfin himma."

Imam Aliyu yana cewa: "Idan ka sami amini, to ka zama bawa gare shi, kuma ka tabbatar masa da cika alkawari da gaskiya tare da yarda."

Mutanen kawai da suka cancanci zaman tare da samun kaunar jama'a sune masu kyawawan siffofi da falalar 'yan Adamtaka. Manzon Allah (SAW) yana cewa:

"Mafi alherin mutane shi ne wanda ya shaku da mutane masu daraja, wanda ya yi mu'amala da mutane bai zalunce su ba, wanda ya yi magana da su bai musu karya ba, wanda ya musu alkawari bai saba musu ba, to shi yana da ga cikin wadanda darajarsa ta kammala, adalcinsa kuma ya bayyana, kuma ya wajaba a yi 'yan uwantaka da shi."

Dokta Smiles yana cewa: "Idan kuka zauna tare da mutane masu tsarkin ruhi da halayyar kwarai za ku ji wani abu yana jan zukatanku da halayenku zuwa ga kyautatuwa da daukaka. Zama da mutanen da ke da kakkarfan hankali masu falala gogayya ce babba wadda ta dara komai kima da tsada. Domin zama da su irin wadannan mutane yakan ba mu sabon karfin ruhi, ya koya mana hanyoyin rayuwa da ladubbanta, ya gyara ra'ayoyinmu da tunaninmu dangane da wasu. Tunda yake su sun fi mu karfin ruhi da tsarkin zukata, sai mu amfana da zama tare da su mu kyautata halayyarmu. Manufofin rayuwarmu kuma su daukaka su taimake mu a ayyukanmu wajen tamaka wa sauran jama'a. Zama da mutanen kwarai na cusa mana alheri da kyautatuwa. Halin kwarai tamkar haske ne, yana haskaka duk abin da ke gewayensa da wanda ke kusa da shi."

Abubuwan da muka ambata can baya sun tabbatar mana kenan cewa ya kamata kowane mutum ya san nauyin da ya rataya a wuyansa dangane da alkawari da rantsuwa.

Mun ciro wannan bayani ne daga littafin KYAUTATA DABI'U na Sidi Mujtaba Musawi Lari, fassarar Yakubu Abdu Ningi

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International