Almiza:Ba don raba kan musulmi muka bude masallacin Juma'a ba ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426                 Bugu na 690                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rahotanni

Ba don raba kan musulmi muka bude masallacin Juma'a ba

In ji Shaikh Yahya Musa Kaduna

H

Limamin sabon masallacin Juma'ar da aka bude a baya-bayan nan a mahadar hanyar Karaye da College Road U/Dosa Kaduna, Shaikh Yahya Musa, ya tabbatar da cewa; "ba don raba kan musulmi muka bude sabon masallacin Juma'a ba."

Shaikh Yahya Musa, wanda yake ganawa da ALMIZAN a gidansa bayan nada shi sabon Limamin sabon masallacin Juma'ar da Hakimin Kawo ya yi, ya bayyana mana cewa, sun bude wannan masallacin ne domin su yalwata wa al'ummar musulmi da suke cike da tsananin bukatuwa ga samuwar masallacin Juma'a a yankin.

Bude wannan masallacin da aka yi a farkon wannan watan ya jawo hayaniya da kuma cece-kuce a tsakanin 'yan Izala da 'yan Darika da ke Unguwar, sakamakon yadda wasu mutane da ake jin 'yan Izala ne suka nuna kin amincewarsu da samar da masallaci a wajen, ta hanyar rubutar takardar kokensu ga hukumomin garin Kaduna don a dakatar da budewa da kuma yin salla a wannan sabon masallacin Juma'ar.

A wata takarda da suka rubuta mai shafi uku, Izalawan sun koka da cewa bude wannan masallacin zai kawo rikici a yankin wanda ba a san iya inda zai tsaya ba kasancewar masallacin ya yi kan hanya, zai hana wa mutanen da suke Unguwar walwala.

A cewar takardar, wacce suka aika har gidan Gwamnan Kaduna, Alhaji Ahmad Makarfi, ofishin babban Sakataren Hukumar kula da harkokin addini, Alhaji Idris Balarabe Jigo da kuma ofisoshin 'yan sanda da ke yankin, ta nuna hadarin da ke tattare da bari a ci gaba da yin salla a wannan sabon masallacin Juma'ar da aka bude.

Takardar koken, ta nuna tsoron kada a samu rikici shigen wanda ya faru a garin Jos na jihar Filato sakamakon toshe manyan hanyoyin da ake yi a lokacin sallar Juma'a.

Majiya mai tushe ta bayyana mana cewa, masu koken sun nuna damuwarsu matuka a kan cewa wannan masallacin zai iya kawo koma baya ga wani masallaci da ke dab da wanda aka bude wanda kuma Izalawa suke jagoranta da ke makarantar tunawa da Sardauna, (SMC).

Sai dai bayan da Kwamitin Malamai da Dattawan Unguwar ya rubuta takardar da ke dauke da bayanin irin shiri da tsarin da suka yi don kauce wa kawo cikas ga masu wucewa ta hanyoyin da suka sa masallacin a tsakiya, gwamnatin jihar Kaduna ta yi watsi da wancan koken, ta bari an bude wannan masallacin an ci gaba da yin sallar Juma'a a cikinsa.

Shaikh Yahya, wanda babban Malamin Darika ne, ya nanata cewa su dai a wajensu ba saboda bambancin akida ko fahimta ne ya sa suka bude sabon masallacin a U/Dosa ba, "ai mu kowa namu ne. Idan ana maganar musulmi mu duk a wajenmu musulmi daya ne. Allah ya ce mu yi riko da igiyar Allah kar mu rarraba. Mu duk wanda ya yi kalmar shahada dan uwanmu ne," ya jadadda.

Ya zuwa yau Juma'a dai sati bakwai kenan ana yin salla a wannan sabon masallacin Juma'ar, kuma har ya zuwa lokacin da muke rubuta wannan labarin komai yana tafiya daidai, jama'a kuma suna ta yin tururuwa zuwa yin salla a wannan masallacin Juma'ar da ake takaddama a kansa.

Waki'ar Sakkwato:
Kulen da ke gaban 'yan uwa Musulmi

Daga Muhammad Ahmad (sonsofmuk@yahoo.co.uk)

Assalamu Alaikum. Zuwa ga 'yan uwa musulmi na Nijeriya. Ya ayyuka da hakuri, tare da juriya a kan tafarkin Harka Islamiyya? Kafin in yi nisa bari in fara da bayanin kaina. Da farko dai ina zaune ne a kasar waje a can Gabas Mai Nisa, amma daga Nijeriya nake, amma duk da haka ina lura tare da sa ido a kan Harka Islamiyya tun ina sakandare, kamar shekaru 13 da suka gabata. Kuma tun daga lokacin ina bin Harka daki-daki, duk da yake ba na halartar tarurruka ko wa'azozin da ake gabatarwa, amma duk sati ba ALMIZAN din da ke wuce ni. Ko ba na Nijeriya sai na karance ta kakaf a Intanet, (Sakar Sama), kuma duk wani kaset ba ya wuce ni, musamman na Malam Zakzaky, domin ko yanzu ba zan rasa kasakasan Harka Islamiyya akalla 200 ko ma fiye da haka ba a yanzu.

Waki'ar da ta faru a Sakkwato, wadda aka kira wai SHIA-SUNNA ce ta janyo hankalina kan wannan rubutun. Kamar yadda 'yan uwa suka sani an yi kimanin watanni hudu cikin mawuyacin hali a Sakkwato, tun daga watan Al-Muharram har zuwa Rabi'ul Thani. A cikin tsawon wadannan watanin na koma Sakkwato kusan sau uku, kuma ma daga inda nake ina matukar lura da abin da ke faruwa a Sakkwato.

Ba sai na kawo wani dogon tarihi ba kan abin da ya faru, wanda kowa ma ya riga ya san su sarai, amma ina so ne in kawo wasu darussa da na koya, wadanda kuma a iya fahimtata da wannan Harkar, yana da kyau 'yan uwa da ma sauran al'umma su ji su yi tunani da nazari a kai.

Na daya. Kamar yadda na ambata a baya, wannan matsalar ta faro ne ranar da aka yi muzaharar Ashura a Sakkwato, inda aka yi gayyar 'yan tauri da zauna-gari-banza, wadanda ke dauke da muggan makamai, suka auka wa 'yan uwa da nufin su kashe su, wadanda a lokacin 'yan uwan ba su tare da ko tsinke, amma cikin iyawar Allah mutum daya ne kawai suka iya kashewa a lokacin.

Bayan kwanaki hudu da yin wannan kuma, sai suka far wa 'yan uwa a cikin masallaci, wanda a lokacin 'yan uwan yawansu kadan ne, amma zauna-gari-banza da 'yan tauri sun kai 1,000, kuma sun zagaye dukkan masallacin dauke da muggan makamai. A lokacin ba wanda ya yi tsammanin wani zai tsira da ransa, amma duk da haka, mutum uku suka iya kashewa a 'yan uwan.

Bayan wannan waki'ar ne kuma aka sake yin shirin auka wa gidajen 'yan uwa daya-baya-daya da nufin yi masu kisan kare-dangi, tare da rusa ko kona gidajensu, wanda sun riga sun shirya tsaf, domin har ma na ji mutumin da ke kan gaba wurin tafi da wannan ta'asar (Wazirin Sakkwato) na cewa; sai sun kori dukkan 'yan uwa da ya kira 'yan Shi'a daga Sakkwato. Wanda ya zuwa karshen matsalar sun yi nasarar kashe 'yan uwa shida, tare da rusa gidajensu kimanin 60.

DARASIN DA KE CIKI

Duk da yake an shirya ne tsaf da nufin yi wa wata al'umma('yan uwa) kisan kare-dangi, (wanda da ba 'yan uwa ne ba) hakika da ba na tsamanin wani daga cikinsu zai saura a garin Sakkwato, saboda irin yadda aka tsara shirin, kuma aka tafi da shi daki-daki. Ina da tabbaccin da ba 'yan uwa ne ba, da cikin watanin nan hudu da aka yi ana kai masu miyagun hare-hare, da watakila an kashe dubun-dubatarsu ne, amma saboda abin na Allah ne, sai ya zabi wadanda ya so su koma wurinsa.

Misali a nan shi ne, tun bayan komawar Nijeriya mulkin da suke kira na farar hula, an samu rikice-rikicen siyasa da na kabilanci, a kusan duk fadin kasar, wanda idan an kwashe kwana biyu ko uku kawai ana rikici, sai ka ji an kashe mutane dubbai. Amma a waki'ar Sakkwato, ba fada ne ake yi ba, tsakanin wani bangare da wani bangare ba, a'a, ana auka wa wata al'umma ne da kisa da nufin kawar da su, amma duk da haka mutane shida ne aka yi nasarar kashewa!!!

SAKAMAKO

Kamar yadda aka sani, bala'i na sauka sannu a hankali kan wadanda suka yi wannan aika-aikar. Misali, akwai wani da Babansa da suka taka rawa a rusa gidajen mutane, wani lokaci a baya haka kawai gidansu ya kama da wuta ya kone kurmus, bayan dan wani lokaci ma suka yi hadarin mota suka mutu.

Akwai wani da ya soki wani dan uwa da wuka, shi ma wasu barayi suka hau babur dinsa suka kai shi bayan gari suka kwace babur dinsa suka kuma kashe shi.

Ina kan hanya daga Nijeriya zuwa nan inda nake, nake jin labarin cewa shi ma wani da shi ne ya saka wuta a gidan wani dan uwa, shi ma yana daki wuta ta kama dakin ya kone gaba daya, sai dai ban san ko ya mutu ba. Wannan wasu daga cikin abubuwan da suka bayyana kenan na bala'in da ke fada wa wadanda suka yi ta'addancin na Sakkwato.

A nan ya kamata duk wani wanda ke da hannu a cikin wannan ta'addancin ya sani, ya kulla gaba ne da Allah (T), kuma da sannu zai ga abin da zai faru a kansa, (matukar bai tuba ba).

A nan ina son in yi kira ga al'umma wadanda ba su fahimci Harka (kiran Malam Zakzaky) ba, da cewa idan ma mutum ba ya yi, to don Allah ya kyale masu yi kada ya shiga cikin masu gaba ko fada da abin. Domin tarihi ya nuna duk wanda ya yi fada da wannan Harka, sai ya wulakanta tun nan duniya, kafin ya je gaban Allah, ya gaya masa dalilinsa na yin fada da bayinsa.

Ya ishe mu ishara, kullum ana kawo misalin tsohon Sarkin Sakkwato, Alhaji Ibrahim Dasuki, wanda ya yi fada da Harka Islamiyya, a kan idonmu mun ga yadda ta faru da shi. Haka ma Janaral Sani Abacha, mun ga yadda ta kasance da shi. Ga ma na baya-bayan nan, tsohon Sarkin Gwandu, Alhaji Mustapha Haruna Jokolo, wanda a lokacinsa har 'yar uwa mace ya daure a kurkuku. Mun ga yadda ta kasance da shi.

Ga Mataimakin Gwamnan Sakkwato, Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko, wanda ake zargin ya taimaka da kudi a sayi makamai don a kashe 'yan uwa Musulmi da suke kira 'yan Shi'a, (duk da yake na ga ya fara 'yan kame-kame wai ba shi da hannu a ciki).

Sai manyan iyayen tafiya, Sarki mai ci yanzu, Alhaji Muhammad Maccido Abubakar, da Wazirinsa, Alhaji Usman Junaidu, wadanda suka jagoranci rikicin suka kuma tafi da shi tare da sama wa rikicin kudade da makamai domin a kashe al'ummar Musulmi. Wadanda kullum mutane ke addu'ar Allah don Manzonka, ka yi hukunci tsakanin wadannan mutane da 'yan uwa musulmi. Ka yi masu irin yadda suka yi wa al'ummar Musulmi.

Daga karshe zan so in yi kira ga 'yan uwa da duk masu tafiyar Harka Islamiyya a garuruwansu cewa suna da 'challenges' (kule) babba, na wayawar da kan jama'a a kan wannan Harka, tare da yin kyakkyawar mu'amala da mutanen da ba su fafimci Harka ba, domin makiya Harkar nan sun tashi haikan wurin ganin bayanta, suna antaya sharri, tare da yin kazafi iri-iri ga ma'abota Harka din. Ba zan manta ba, a kwanan baya mun yada zango a wata kasa kusa da Tekun Medetereniyan, ina tare da wasu mutane 'yan Nijeriya da muke tafiya tare, mu maza uku da macce daya, muna magana kan Nijeriya, muna magana kan addini a Nijeriya, abin da na fafimta daga wadannan mutane shi ne, suna da masaniya kan Harka, amma kuma an bata kwakwalensu da ganin cewa Harka ba abar kwarai bace. A lokacin ban ma yi kokarin nunasshe su ba, saboda na ga sun yi nisa. Illa iyaka na yi masu nasihar cewa, ya kamata dan Adam ya sa a ransa cewa gaskiya yake son ya gani ya gane don ya bi, kuma ya yi ta addu'a kan wannan bukatar gaskiyar da yake.

Zan tsaya a nan sai wani lokacin.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International