Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426
Bugu na 690
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Kasar Iraki:Fagen jihadi ko dandalin wasan kwaikwayon siyasa? (3)
Daga Mujtaba Adam Tehran, Iran, (nigeria3000@yahoo.com)
TAbin da ya fi komai ban mamaki shi ne yadda a daidai lokacin da kogin jinin wadanda ba su ji ba su gani ba ke gudana a kan kasar Iraki, sai ga Ministan harkokin wajen Saudiyya, Sa'ud Al-Faisal ya tsaya a cikin ofishin harkokin waje na Amurka a birin New York ranar 4/09/2005 yana shelanta cewa; "kurakuren Amurka a Iraki sun sa Iran ta mallaki kasar Iraki alhali a baya mun yi aiki tare da Amurka domin mu hana Iran shiga Iraki.!" Kare al'adun Larabcin Iraki -Hawiyyatul-Arabiyya- shi ne abin da ke gaban Saudiyya da sauran kasashen Larabawa, ba rayukan al'ummar Iraki ba. A kansa ne suke yi wa Iraki kuka, ba a kan mutanenta da ake yi wa kisan kiyashi ba dare da rana ba! Mamayar da Amurkan ta yi wa Irakin ma ba ta dame su ba domin kuwa sune suka sa mata albarka. Abin da ya dame su shi ne tsoron tasirin da suke cewa wai kasar Iran tana yi a tsakanin al'ummar Iraki! Dama tsohuwar kiyayyar Larabawa ga Iraniyawa ba boyayya ce, kuma dadaddiya ce, tun kafin bayyanar addinin Musulunci. Ba ta taba gushewa ba sai dai ta sauya kamanni daga lokaci zuwa lokaci. Iran ta zamar wa Larabawa wani bakin mafarki mai ban tsoro da firgitarwa ta yadda ba za su iya daurewa ganin tana ci gaba ba, 'sawa'un' tana bisa turbar Musulunci ne, ko kuwa wani tsari daban da ba Musulunci ba! Dakta Faisal Kasim (Mai gabatar da shirin Ittijahul mu'akis na tashar telabijin din ALJAZEERA) ya yi daidai a cikin martanin da ya mai da wa Ministan harkokin wajen na Saudiyya inda ya ce; "a fili yake cewa Saudiyya ta yi rafkanuwa da ba ta fahimci cewa bayan faduwar gwamnatin Saddam rawar da Iran take takawa a Iraki da kuma yankin Tekun Fasha za ta kara girma ba. Ban san wane dalili ne ya sa Saudiyya da kasashen Larabawan Tekun Fasha suka mance cewa sune suka taimaka wa Saddam da makudan kudin yaki da Iran saboda su hana juyin-juya-hailin Iran isa ga kasashensu, domin gwamnatin Saddam tana da akidar kiyayyar tarihi da Farisawa ba…" "Saudiyya ta rafkana da babban bala'in da zai biyo baya yayin da ta taimaka wa Amurka da dukkan abin da ta mallaka wajen yakin Iraki. Tabbas Iraniyawa sun yi galaba a cikin wannan "wasan kwaikwayon!" Me kuwa zai hana su yi nasara alhali sune suka kirkiro wasan dara (Chess) a duniya? Wasan da mai yin sa yake farawa da cinye mayaka sannan ya kai ga Waziri, a karshe kuma ya rutsa da Sarki ya kas shi!" haka jaridar WATAN ta 29/09/2005 ta ce. Furucin da Ministan harkokin wajen Saudiyya ya yi da bakinsa na cewa; "mun yi aiki tare da Amurka domin mu hana Iran shiga Iraki!" Shi ne babban dalili a kan cewa mamayar da Amurka ta yi wa Iraki ba ta dami Saudiyya kamar tasirin da Iran ke yi a tsakanin Irakawa ba. Kai ka ce mahukuntan Saudiyya sun mance da cewa Kurdawa da 'yan Shi'ar Iraki da ke kan karangar mulki yanzu ba su da wata kasa daya da ta agaza musu a lokacin da Saddam ke yi musu kisan kiyashi in ba Iran ba. A asibitin garin Kermansha na Iran aka yi wa Kurdawan garin Halabja magani bayan da Saddam Husain ya watsa musu makami mai guba. Bilhasali ma, kasashen Larabawa suna yi wa Saddam Husain tafi ne da jinjina masa a lokacin da yake watsa wa Kurdawa makami mai guba, yake kuma binne dubban 'yan Shi'a a cikin manyan kabarurruka. Kurdawa da 'yan Shi'a miliyan biyu ne suka yi zaman gudun hijira a Iran a lokacin da kasashen Larabawa suka rufe iyakokinsu suka hana su shiga ciki. "Shugaban Iraki na yanzu Jalal Talibani (wanda Sunni ne ba dan Shi'a ba. Domin Kuradawa da adadinsu ya kai miliyan shida a Iraki mafi yawan su Sunni ne), ba shi da abokai a Gabas ta Tsakiya idan ba Iraniyawa ba a lokacin da yake dan hamayya. "Shi kuwa Firaministan Iraki, Ibrahim Ja'afari da Saddam Husaini ya yanke masa hukuncin kisa, sannan ya shiga Iran da kafa, ya rayu a kasar Iran fiye da yadda ya rayu a cikin kasarsa ta haihuwa, Iraki," in ji Abdul-Bary Adhwan, Editan Jaridar Qudsul-Araby. Ko kuma Kungiyar 'Majlisul-A'ala Lis Thauratul-islamiyya' ta Sayyid Bakir Hakim, wacce aka kafa ta a Tehran a cikin shekarun tamaninoni. Babbar Kungiyar adawa da Saddam Husain ce, wacce take da karbuwa a tsakanin 'yan Shi'ar Iraki da sune mafi rinjaye a Iraki. Me zai hana Iran ta yi tasiri a cikin Iraki bayan faduwar gwamnatin Saddam Husini alhali mutanen da ta taimakawa ne a lokacin da suke cikin wahala ke tafiyar da mulki a yanzu? Larabawa da a tsakaninsu ba su da siyasar waje ta bai daya a kan komai. Ba za su tsammaci Iran ta zama kamar su ba alhali tana fuskantar barazana daga Amurka da ta jibge sojojinta a dukkan kusurwowinta hudu. Lokacin da Goerge Bush ya shelanta yakinsa mai tsarki na Salibu ya sanya Iran a cikin kasashen da ya kira "Gungun Shaidanu." Sannan kuma ga shi ya kifar da daya daga cikin gwamnatocin, ta Saddam Husaini, wacce ita ce kadai kasar Larabawa da ta shiga cikin wannan lissafin nasa. Duk wata kasa da ta damu da kare 'yancinta da cin gashin kanta, to dole ne ta shata katangar tsaron kanta nesa da iyakokinta na kasa. Ko dai ta hanyar soja, ko kuma ta hanyar tattalin arziki, ko kuma ta hanyar al'adu a cikin kasashen da ke makwabtaka da ita. Syria ba ta shiga cikin kasar Lebanon ba a cikin shekarun saba'inoni, sai saboda ta hana Isra'ila isowa gare ta bayan da ta mamaye kudancin Lebanon. Pakistan ba ta damu da kasar Afghanistan ba, sai saboda ta san cewa duk abin da ya faru a ciknta zai iya yin tasiri a cikinta. Ta goyi bayan Mujahidun da Taliban da kuma gwamnatin Hamid Karza'i ne bisa dalili daya; shi ne kuwa tsaron kasarta. Dole ne ta tabbatar da cewa wadanda ke mulki a birnin Kabul ba su adawa da Islambad. Me zai hana Iran ta tabbatar da cewa sababbin masu mulki a kasar Iraki ba wadanda za su sake kulla gaba da ita bane kamar Saddam Husaini? Ta kuma tabbatar da cewa ba za su ba da dama Amurka ta yi amfani da wannan kasa ba domin kawo mata hari? Editan jaridar Al-Qudsul-Araby, da yake mai da wa Ministan harkokin wajen Saudiyya martani ya fadi cewa; "Iran, kasa ce da take dogara da kwararru da masana wajen shata siyasarta da kuma kare 'yancinta da kasarta. Saboda haka ne ta wayi gari tana da siyasa mai karfi a Gabas ta Tsakiya. Da sojoji masu karfi da shirin makamashin nukilya mai girma. Ta wayi gari tana kalubalantar siyasar Amurka a Gabas ta Tsakiya ne saboda ta taka dutse. Tambayar da ya kamata Larabawa su yi wa kawunansu shi ne; me ya sa kasashen Masar da Saudiya da Syria ba su da ta cewa a cikin siyasar Iraki? Ba neman dalilin da ya sa Iran ke shiga cikin siyasar Iraki ba…. Iran ta wayi gari tana rike da sojojin Amurka da ke Iraki a matsayin fursonuni.. Ina yi wa Iran murna, sannan kuma ba na taya Larabawa juyayi…" Jaridar Alqudsul-Arabi ta ranar 9/9/2005. Za mu ci gaba insha Allah.
|
Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |