Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426
Bugu na 690
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
INA MALAM BABAYO MUSA?Malam Babayo Musa Jos NNPC Depot Makurdi, na ji kana cewa ku IZALATUL BIDI'A WA IKAMATUS SUNNA ce jirgin tsiranku, amma na ga a jikin jirgin da ka ce ba ruwanka da shi, akwai kalmar La'illaha illallahu Muhammadu Rasullulahi a kansa. To naka jirgin tsiran, wace kalma ce a kansa? Kuma ai ga shi nan ma an rusa naka jirgin tsiran. To ya kamata ka zo ka hau wanda yake babu wanda ya isa ya ruwa shi. Daga Mustafa Usman Kaduna 0803 637 6252 MALAM FADA ALLAH YA ISABa kowa ne ba ya jefa kasar nan a cikin kangin da take ciki ba, sai Malam fada. Gaskiya kun ci amanar Shehu Danfodiyo. Daga Bashir Ustz Unguwar Kanawa Minna jihar Neja 0802 787 1944 EDITA INA NEMAN KARIN BAYANIAssalamu alaikum. Edita ina neman karin bayani game ga jawabin watan Ramadan da kuka sa a makonni hudu da suka gabata. Shin jawabin na bana ne, ko kuwa ? Daga Yusuf Mai gyran Rediyo Bici jihar Kano 0803 637 1635 Malam Yusuf ba mu sa jawabin Ramadan ba, sai dai mun sa hudubar Manzon Allah da ya yi shekaru fiye da 1400 da suka gabata.HABA SHAIKH DAHIRU USMAN BAUCIAssalamu alaikum. Shaikh Dahiru Bauci ka san fa kai Shehi ne, ya kamata ka ji tsoron Allah ka daina zigza da kalankuwa a kan cancantar khalifancin Imam Ali (AS) da sauran Sahabbai a tafsirinka na ran 21 ga watan Ramadan 1426 alhali ka san komai. Daga Adamu Zawal 0803 538 7890 INA ABOKINA HORSE POWER?Assalamu alaikum. Ina abokina Muhammad Horse Power Almizan ba ta aiki da jita-jita, idan da gaske ne ba ka sani ba, Allah ya ganar da kai. Daga 0806 532 2274 INA GAI DA JAGORANAAssalamu alaikum. Ku mika min gaisuwata ga Imamul bara'a Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). allah ya ja zamin Malam, amin. Daga Safiyanu Aliyu Tanko 0803 538 7890 SHEKARAU KWANAKA NAWA?Assalamu alaikum. Haba Shekarau kwanaka nawa? Saura kwana nawa ka sauka? Da me za ka je wa Allah idan ka yi fada da shi. Ya kamata dai ka sani ba a fada da Allah a ci riba. Daga Tahir Ibrahim T/Wada Zariya 0806 532 2274 ALLAH YA JA ZAMIN ALMIZANAssalamu alaikum. Allah ya ja zamanin Almizan. Allah ya saka maku da alherinsa. Mu kam a Adamawa kowanne mako muna samun Almizan. Daga Abubakar AMB Yola 0803 451 4631 GWAMNAN ZAMFARA YAYA DAI?Assalamu alaikum. Gwamnan Zamfara Alhaji Ahmad Sani yaya dai, don na ga da da wuya ka share sati biyu fita kasashen waje ba, amma sai na ji yanzu ka daina fita ko dai kana jin tsorn irin abin da ya faru ga Gwamnan Bayelsa ya faru gare ka ne? Daga Shehu Kaurar Namoda jihar Zamfara mazaunin Kormo Abuja 0804 337 3137 MUTUWAR STELLA OBASANJO MA AYA CEZuwa ga ''yan uwa Musulmi na Nijeriya musamman masu kokarin yin fada da Harkar Musulmi a Nijeriya karkashin jagorancin Malam Ibraheem Zakzaky don giyar dimokradiyya tana kwasarku, ya kamata dai su sani Stella Obasanjo ta fi ku shan giyar dimokradiyya, amma yanzu ina take. Hattara dai musulmi! Daga Aliyu Musa, ali Yamalti 0803 678 8569 INA YI WA MALAM ZAKZAKY FATAN ALHERIAssalamu alaikum. Ina fatan alheri ga Malam Zakzaky saboda kokarin da yake yi na fadakar da jama'a da yake yi. Ina fatan an yi muzaharar Kudus lafiya. Ina Allah ya so kwanan nan zan kawo wa Malam Zakzkay ziyara. Daga Nasiru Ibrahim Shehizzaman Jagoran Palasdinawa koki Kano 0802 358 9589 ALLAH YA JI KAN MUSULMIN DA SUKA RASU A PAKISTANAssalamu alaikum. Girgizar kasar da aka yi a kudancin Asiya babbar musiba ce a duniya. Allah ya ji kan musulmin da suka rasu. Mu kuma Allah ya kare mu Daga 0806 541 8587 INA MUSULMIN NIJERIYA?Assalamu alaikum. Musulmin ya rage naku? Kusan shekaru bakwai kenan ana dimokradiyya da sunan za a gyaran da soja suka yi. To yanzu wane sauyi aka samu? Ya kamata dai mu san cewa wallahi adlaci da sauyi na alheri yana cikin kiran Malam Ibraheem Zakzaky. Mai rabon rabon shan romo a duniya da lahira shi ne zai shigo cikin da'awar Malam Zakzaky (H) a yi gwagwarmaya da shi. Daga Muhammad Aruwa K/Guga Katsina 0803 692 0810 KU SAMAR DA FILIN GIRKE-GIRKEAssalamu alaikum. Kira ga ALMIZAN, ya kamata ku samar da filin girke-girke a wannan jarida mai albarka domin amfanarwa ga mata da kuma ba su dama su dinga rubuce-rubuce. Daga Abdullahi Sufi Kano 0802 331 5987 Malam Abdullahi ai dama wannan filin a bude yake. Kuma muna maraba da duk wasu rubuce-rubuce makamantan haka. Mun gode.- Edita Shafi AMURKA WANNAN SHI NE SAKAMAKON FADA DA MUSULUNCIAmurka karshenki ne ya zo, kuma wannan shi ne sakamakon fada da Musulunci. Wanda duk ya debo da zafi bakinsa. Sauran Arna kuma sai ku dauki darasi. Daga Abba Isma'il Kano 0805 741 4201 INA MALAM KABIR ALKANAWIY NE?Salawat! Kwana biyu Malam Kabir Alkanawiy shiru, muna kishin ruwan rubutunsa. Allah (T) ya kara masa basira, hikima da juriyar isar da sako, don alfarmar Sultanil Anbiya (S). Daga Dalhatu Ibrahim Zariya 0806 572 1110 JINJINA TA MUSAMMAN GARE KUJinjina ta musamman gare ku baraden Musulunci da Manzon Tsira (SAW) da Imam Ali (AS) da Sayyida Fatima (AS) da Imam Husan (A) da Imam Husaini (AS) da sauran Imamai. Daga Abdullahi Gambo Marna Katsina 0802 737 6318 abdullahigambomarna@yahoo.com ALMIZAN ME YA SA KUKE YIN KARYA NE?Salamu alaikum. ALMIZAN me ya sa kuke yin karya ne? Kun ce Obasanjo na neman ganin bayan Masari, amma ba mu ga labarin ba. Daga Naku Adamu 'Yar Fagge 0803 685 9089 Malam Adamu ka mai da wukar! Sai bayan mun gama hada jaridar ne muka lura ba mu sa labarin ba, amma dai a makon da ya gabata mun zo maku da shi kamar yadda yake. Amma da kana duba sauran jaridu, da ka gane ba mu kadai ne ajizancin dan Adamtaka yake sa wa su yi kuskure ba.ALMIZAN TA SHEKARA 15Assalamu alaikum. Ina taya Maulanmu Malam Ibraheem Zakzaky (H), Hukumar I.M. Publications da daukacin al'ummar duniya masu amfana daga wannan muhimmiyar kafa ta ALMIZAN murnar cikarta shekara 15 cur tana fitowa. Zakaran da Allah ya nufa da cara... Ubangiji ya kara tallafi, amin. Daga Awwal Sulaiman G. Dutse Kano ALLAH YA SAKA WA MALAM TURIAssalamu alaikum. Edita ina ba da shawara da a duba batun mai da hirar da kuke yi da Malam Muhummmad Turi ta Tuna Baya, wacce yake bayyana mana abubuwan da bai manta da su ba a shekaru 25 na ayyana Hakar Musulunci littafi, don zai amfanar sosai. Bissalam. Daga Mulammad Jalam Maigado da Kafita Potiskum 0803 970 3978 GASKIYA KUN CANCANCI YABOALMIZAN gaskiya kun cancanci a yaba maku. Kuma muna gode maku. Allah ya ja zamanin Malam Zakzaky (H), amin. Allah ya ja zamanin ALMIZAN, tare da ma'aikatanta, amin. Daga Abba Umar Katsina 0802 423 0269 BUSH DA BLAIRBush da Blair in dai dimokradiyya ita ce ra'ayin jama'a, to talakawan kasashenku, sun ce ku fice daga Iraki. Daga Muhammad Bello Maiduniya lafiya jihar Nasarawa 0806 245 0055 ALMIZAN KU JE WAJEN MALAM YA YI MAKU ADDU'A MANAAssalamu alaikum. ALMIZAN na lura kuna fuskantar matsaloli. Ya kamata ku je wajen Abba (Malam Zakzaky) ya yi maku addu'a mana kamar yadda ya yi maku a lokacin da yake tsare a Kaduna. Daga Sulaiman Damagari jihar Kano AZZALUMAI GA DAMA TA SAMUAssalamu alaikum. Ya ku makiya ga dama ta samu na tuba, sai ku tuba. In kun ki za ku sha wahala a hannunmu. Kuma Sarkin Sakkwato ka sami damar tuba, sai ka hanzarta ka tuba. Daga Murtadha Unguwar Rimi Kaduna 0802 572 9175 JA'AFAR ADAM KA AMSA KIRAN ABDULJABBAR MANAAssalamu alaikum. Haba Malam Ja'afar Adam, idan dai ilimin naka da gaske ne, to ka amsa kiran Malam Abduljabbar da yake yawan yi maka mana na ku je ku yi mukabala mana. Daga 0802 841 5135 ALLAH YA RABA MU DA BIYU BABUAssalamu alaikum. Allah ya raba mu da biyu babu. Musulmin Nijeriya ku tanadi uzurin da za ku bai wa Ubangiji ranar gobe kiyama idan Allah ya tashe ku da azzalumai ranar kiyama babu mafita a tare da ku. Don haka ya zama dole ku yi tawaye ga azzalumai ku daina biyayya gare su domin tsira duniya da lahira. Daga Adam 0802 841 5135 'YAN NIJERIYA ALLAH YA YI MAKU MAFITA'Yan Nijeriya ku ji tsoron Allah ku gode masa domin ya yi maku babbar mafita, wannan mafitar kuwa ita ce Malam Zakzaky (H). Daga Kasimu Kalmalo Ilela 0805 476 5866 KIRANA GA MASU KARANTA ALMIZANAssalamu alaikum. Ina kira ga masu karanta ALMIZAN cewa don Allah in an gama karanta ta kar a yarda a kunsa wani abu da ita, saboda akwai ayoyi da hadisai a ciki. Daga Idris Maifaci Lakwaja Road Rigasa Kaduna 0802 853 6859 TARIHI NE KE MAIMATA KANSAAssalamu alaikum. A gaskiya mun tabbata tarihi yana maimaita kansa. Abin da ya faru da bayin Allah nagari shi ne yake faruwa ga Malam Zakzaky. Daga Aminat Medicine Store Nyanya Village Abuja 0802 890 2301 LALLE NI NA YARDA CEWA ANA ZABE NEAssalamu alaikum. Ni ma na bi sahun masu cewa ana zaben wadanda za a karanta wa Malam tambayar su don amsawa, da kuma buga ra'ayoyinsu, ko kuwa ana biya ne? Ba a taba amsa mani tambaya ta ba. Kuma na aiko da ra'ayina a kan al'amura da dama, amma ba a buga ba. Daga Bilyaminu Kiru 0802 309 7766 Malam Bilyaminu a gaskiya ya kamata ka yi mana adalci domin ni na san cewa duk mai karanta shafin nan ya sha karanta sakonnin Bilyaminu Kiru. Babu mamaki wadanda ba ka gani ba kila ba su iske mu bane, ko kuma ba su da muhimmanci ne a wajenmu da masu karatun jaridar ALMIZAN. Game da tambaya zuwa ga Malam kuwa, muna da tambayoyi bila adadin a ofis dinmu, kuma muna bi ne daya bayan daya. In har taka ta zo wajenmu insha Allah wata ran za ka gan ta.- Editan shafi MARTANI: LALLE EDITAN SHAFI KA IYA KARYANa yi mamakin ganin sako daga wani da bai sa sunansa ba. Ina ganin yana bukatar ya yi karatu da kuma bincike a addini domin sanin Musulunci, kuma yana da bukatar ya karanta wasikar da aka rubuta wa Shekarau, idan ba haka ba kuwa, zai zama cikin yaran Yahudu. Daga 0803 821 4717 NA GODE ALLAH DA NIJERIYA TA KASA ZUWA WORLD CUPNa yi matukar godiya ga Allah da ya amsa addu'ar talakawan kasar nan na hana Nijeriya damar zuwa World Cup, domin babu abin da za a yi sai barnata kudin talakawa a kan abin da ba shi da wani alfanu gare su. Daga Salisu Sani Romi Rigasa Kaduna 0802 310 4109 MUSULMI MU GANE BA SHI'A-SUNNA BANEAssalamu alaikum. Kirana ga al'umma musulmi na wannan kasa shi ne mu gane cewa miyagun Malamai na neman hada fadan addini wai da sunan Shi'a da Sunna ne kawai. To mu gane ba wata nasara da za mu samu domin Allah ya umurce mu da mu yi riko da igiyarsa guda daya, kuma kada mu rarraba. Daga Sanusi Ya'u Siya-siya 0803 286 8800 ABUBAKAR RIMI KA GANE WANNANAlhaji Abubakar Rimi ka sani fa Sarki goma zamani goma. Ba za ka ci naka zamanin sannan ka ci na wasu ba. Saboda haka ko ka bi a yi da kai a yanzu, ko kuma ka koma gefe ka zura wa 'yan zamani ido a siyasar jihar Kano ta yanzu. In ka ki kuma ka yi ta ganin abin da ka yi wa wasu. Daga Idris Adamu Bajoga 0802 469 5099 WANNAN WATA NE NA NEMAN LADAAssalamu alaikum. Ina kira ga 'yan uwana musulmi mu guji abubuwa marasa kyau a cikin wannan watan na Ramadan, domin wannan watan riba ne ga musulmi. Daga Hasan Abba Potiskum 0803 839 9915 ALMIZAN: RASHIN FITOWARKI MATSALA CE A GARE MUAssalamu alaikum. ALMIZAN kin fahimci matsayinki a cikin al'ummar nan kuwa? Gaskiya rashin fitowarki rashin madogara ce ga wadanda ake zalunta, kuma hutu ne ga azzalumai mashaya jini. Allah ya kare ki ALMIZAN. Daga Abu Mahdi Kujama 0805 374 4301 BUKAR ABBA INA KUDIN SCHOLARSHIP DINMUHaba gwamnatin jihar Yobe wai me ya sa ba za ku biya mu 'scholarship' dinmu bane? To wallahi ku hanzarta ku biya mu. In ba haka ba mun san matakin da za mu dauka a kanku. Daga Ibrahim El-Fafsir Potiskum 0803 207 6472 WANI AIKI SAI MAI FITSARI A TSAYEWani aiki sai mai fitsari a tsaye, ga tsadar abinci, ga karin kudin fetur, ga rashin aikin yi, ga magudin zabe, cin hanci da rashawa sune aikin Obasanjo. To 'yan Nijeriya wane jirgi za a hau gobe, jirgin Neja ko jirgin Daura ko dan Adamawa? Ka yi ta kanka! Wallahi da bakin kashi da jan kashi, duk sunansu kazanta. Daga Abdullahi Gambo Marna Katsina 0802 737 6318 INA MASU TANTAMAR KIRAN MALAM ZAKZAKY?Ina masu cewa kiran Malam Zakzaky ana halakar da matasa ne? Kuna cewa ana nuna masu son Ahlul Baiti, ko kuma ana tura su cikin Shi'a. To a zahiri dai maganar ta nuna jahilcin masu fadar haka. To mun ji da son Ahlul Baiti ake tura mu Shi'a, to kai kuma jahili da menene ake mai da kai makiyin Ahlul Baiti? Daga Abdullahi Gambo Marna Katsina 0802 737 6318 SANNU BARADEN YAKI DA JAHILCIIna mika gaisuwata da jinjinata ga Baraden Madakin Kano, kuma Shugaban makarantar yaki da jahilci ta Shahuci Kano, Alhaji Garba Danladi Satatima Kano. Allah ya yi taimako, amin. Daga Ado NEPA Kofar Wambai Kano 0802 872 5131 SHAWARA GA 'YAN UWA A WATAN RAMADANAssalamu alaikum. Shawarata ga 'yan uwa a kan wata mai daraja na Ramadan shi ne, ya kamata su sani Allah (T) ya yi magana a kan wannan wata, inda yake cewa 'shaharu Ramadanal lazi unzila fihil Kur'an..' Kuma ya zo a cikin wani hadisi, Manzon Allah yana bayyana darajar wannan watan na Ramadan. Har ma yake cewa duk wanda Ramadan ya zo ya wuce bai samu gafarar Allah ba ya isa la'ananne. Abin da nake so in ganar da 'yan uwa shi ne kada su gafala domin yanzu rige-rige ake yi wajen aikin alheri. Daga Mansir Sadi Tudun Iya Funtuwa, Katsina (mansirsadi@yahoo.co.uk) EDITAN SHAFI YA HAKA?Assalamu alaikum. Editan Shafi, me ya sa ba ka mayar wa da Malam Babbayo martani ba a kan sakonsa kan labarin wasannin kwallon kafa, alhali nakan ga wani lokacin kana yin haka ga iri-iren sakon da aka aiko? Ko kuwa dai haramun din ne? Daga Ahmad Sa'eed Ahmad Hizbullah Chemist Potiskum jihar Yobe 0803 469 0159 Malam Ahmad, ai na bar shi ne da ku masu karatu sai ku mayar masa da martani.-Editan Shafi. MUN JI DADIN LABARINMU DA KUKA BUGAAssalamu alaikum. Mu 'yan uwa na garin Bici mun ji dadin labarin muzaharar da muka yi a Bici da kuka buga a ALMIZAN, muna fatan za ku ci gaba da halartar abubuwan da muke yi kuna bugawa. Daga Abubakar Bici Malam Abubakar idan dai an sanar da mu ba yadda za a yi ba za mu je ba, kuma mu buga, amma idan kuka yi abinku daga ku sai ku, ba wanda zai ji.-Editan Shafi ALMIZAN BAN JI DADIN ABIN DA KUKA YI MIN BAAssalamu alaikum. ALMIZAN ban ji dadin abin da kuka yi min ba. Na aiko da sakonni a kan Wamakko, amma ban ga kun buga ko daya ba. Ku huta lafiya. Daga Arma gindin gida Singa Kano 0805 547 4697 Malam Arma ba mu samu wani sakonka da ka aiko ba, amma wannan da yake mun samu ga shi mun buga.-Editan shafi HABA MUTANEN KATSINA!Assalamu alaikum. Haba mutanen Katsina! Yaya za ku yarda wasu 'yan tsirarun mutane su rinka ba ku bashin babura da tsada, sannan daga baya su saye a wulakance, su bar ku cikin talauci da wahala? Daga Tukur Halilu K/Marusa Katsina 0802 794 4026 MUNA GODIYA GA GWAMNATIN JIHAR BAUCIAssalamu alaikum. Muna godiya ga Gwamnan jihar Bauci, Alhaji Adamu Mu'azu da Shugaban Majalisar dokokin jihar Bauci, Alhaji Tanko Jalam, sakamakon fara yi mana aikin hanya wadda ta taso daga Lanzai zuwa Jalam ta nufi Dambam. Allah ya saka da alherinsa. Daga Muhammad Jalam mai gado da katifa Potiskum jihar Yobe 0803 970 3978 ALLAH YA NUNA MANA AYAAssalamu alaikum. Allah ya nuna mana jarumtakar Kwamandan dakarun Musulunci, Imam Ali (AS) a yakin Badar a gaban Manzon Allah. Yaya mu muke a gaban Wakilin Manzon Allah, Malam Ibraheem Zakzaky (H)? Daga 0803 657 4322 ALLAH YA KARE MANA KUAssalamu alaikum. Ina so ne na mika gaisuwata mai yawa da fatan alheri ga daukacin ma'aikatan wannan jaridar ta Musulunci ALMIZAN. Allah Madaukakin Sarki ya kara kare mana ku, amin. Daga 0803 287 3662 TO JAMA'A MUSULMI MU DUBA MU GANITo, musulmi idan da ba ku gane ba da cewa masu fadin suna yaki da ta'addanci suna kokarin ruguje Musulunci ne da musulmi, to yanzu sun fitowa karara. Don kun ji tsinanne Salman Rushdie yana cewa ya kamata a ajiye Alkur'ani waje daya. Idan za a dauke shi ma, a dauke shi a matsayin tarihi kawai. Wai domin yana koyar da tsattsauran ra'ayi, wanda bai dace da zamani ba. Daga A.A. Mara 0803 688 3377 HABA MATAR EL-RUFA'IUwar gidan El-Rufa'i kin ba ni kunya, a matsayinki na musulma bai dace ki sha hannu da Tonnie Eredia ba. Kodayake Nijeriyanci ne. To amma dai ki ji tsoron Allah. Wannan kuma nasiha ce, Allah Ya sa a amfana. Daga Adamu Garba Zawal 0803 538 7890 ABIN DA YA BAMBANTA MUSULUNCI DA SIYASABabu bambanci tsakanin addini da siyasa a Musulunci. Amma ba ina nufin siyasa irin ta su Bush ba masu fassara addinin Musulunci a matsayin ta'addanci ba. To wannan shi ne kawai dan bambancin da ke tsakaninsu, kamar dai bambancin da ke tsakanin wutar jahannama da Aljanna, siradi ne kurum ya raba su. Daga Prof Nomagic (profnomagic@yahoo.com) MU KARA KAIMI GA NEMAN ILIMIBabu shakka Amurka, Yahudawa da Birtaniya da sauran kafiran duniya makiya addinin Musulunci duk sun hadu sun hada karfi da karfe waje daya don yakar musulmi da addinin Musulunci. Amma maimakon musulmin su farka su tunkari wannan babbar barazanar da ke fuskantar su, sai kara gafala suke yi, da son nuna ragwanci a duk wani bangare na ci gaba, musamman a kan ilmomin ci gaba na zamani, wanda da ire-iren su ne su wadannan makiya namu suke ci gaba da yakar mu dare da rana. Don haka shawarar da zan ba 'yan uwana musulmi, musamman matasa shi ne; mu kara dagewa wajen neman ilimi na addini da na boko don tunkarar makiyanmu kuma makiya addininmu. Daga Hamza M. Djibo Bakin Babban Masallacin Babbar Kasuwa Niyame, Jamhuriyyar Nijar (djibohamza@yahoo.fr) GAISUWA DA FATAN ALHERIAssalamu alaikum. Gaisuwa mai yawa da fatan alheri ga daliban da suka kammla karatun share fagen shiga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, wato SBRS Funtuwa; da fatan kowa ya koma gida lafiya. Allah ya sa mu samu sakamako mai kyau, amin. Daga Umar Abbas No 18 Gidan Dogo U/Bashir Zariya jihar Kaduna 0803 360 7068 |
Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |