Almizan :Dole ya zama muna da kumajin kwatar masallacin Kudus ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426                 Bugu na 690                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tunatarwa:Tare da Shaikh Ibrahim Zakzaky

Dole ya zama muna da kumajin kwatar masallacin Kudus

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.

Mai karatu yau mun shiga kundin Almizan ne muka dauko sashen wa'azin Juma'a na Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky, wanda ya yi ranar Juma'a 10 ga Shawwal 1413, a masallacin Juma'a na Jami'ar Ahmadu Bello Zariya, a inda ya yi magana kan Ranar Kudus. Muna fata za ka ji dadin wannan tuna baya da muka yi don ya dace da wannan muhimmiyar rana ta Kudus. Ibrahim Musa ne ya rubuta mana.

To dama akwai wata rana da aka ware ake kira Ranar Kudus, wato ranar Juma'ar karshe na watan Ramadana. Kuma Juma'ar kashe din ta fado mana, kusan da yawa duk muna i'itikafi. Da ma wannan ranar ne aka kebance don ta zama ranar juyayin Kudus.

Kudus wani birni ne mai tsarki, wanda a cikinsa akwai Masjidil Akasa, wanda Allah Ta'ala ya ambace shi a cikin Alkur'ani, yana cewa: "Tsarki ya tabbatar ma wannan da ya yi tafiyar dare da bawansa daga masallaci mai alfarma (shi ne masallacin Makka - Ka'aba) ya zuwa masallaci manisanci (Masjidil Aksa din da yake birnin Kudus)." Ya kuma bayyana cewa: "Hakika masallaci ne manisanci da muka yi albarka gare shi da abin da ya kewaye shi." Wato abin da ya kewaye shi, shi ne birnin mai tsarki.

Sannan kuma Allah ya ce, "don mu nuna masa ayoyinmu." Wannan bawa na Allah shi ne Manzo, mai tsira da aminci, wanda Allah Ta'ala ya dauke shi daga Ka'aba zuwa Masjidil Aksa, daga nan kuma ya yi mi'iraji da shi, ya hau sama har saman bakwai.

To wannan masallaci mai tsarki da kuma wannan wuri da Allah Ta'ala ya ce ya albarkaci kewaye da shi, yau din nan shekara 45 cur kenan da ya fada hannun Yahudawa, tunda suka kafa haramtacciyar kasar nan wadda suka kira Isra'ila. Kuma tun daga lokacin da suka kama wurin ya zuwa yau din nan, ba a taba samun wata rana da ta bullo kuma ta fada ba tare da sun zubar da jinin musulmi akalla kwara daya ba. To, zubar da wannan jini ba kawai a gefen wannan wuri mai alfarma ba, har ma a cikin masallacin kansa. An taba samun wani lokaci da wani soja Bayahude ya shiga cikin masallacin ana salla, bayan da aka yi sujada ya bude bindiga mai sarrafa kanta ya kashe adadin mutane masu yawan gaske. Amma ko da aka kama shi, sai aka ce wai batsa-batsa ne, bai cika hankali ba. Shi kenan sai aka sake shi.

Kuma an samu lokacin da ma ainihin aka dasa bam a cikin wannan masallaci ya tashi ya lalata wani bangare nasa, bangare da ma aka fi darajtawa. Ko ma a cikin wannan masallaci, an fi ganin nan daidai mumbarin Liman da girma, to a Masjidil Aksa bayan mumbarin Liman akwai wani abu wanda ake girmamawa kamar shigen wanda ake hawa a yi huduba, wanda aka yi da katako a zamani mai tsawo, wanda yake ko tun dama can a zamanin Annabawa na da shi ne tamkar Hajral Aswad a wurinsu. Kamar yadda Hajral Aswad yake a masallacin Ka'aba, to haka nan shi wannan mumbari yake. Wanda yake ko Annabawa a da suna jin tsoron taban sa saboda gudun kar ya zama Allah ya kama su da laifi. A sanadiyyar taban wurin ya zama wani abu ya same su. Wato sukan je da ladabi ne kan su iya taban shi. Kuma akwai wata kissa tana nuna mana cewa wani yana kusa da wurin ya taba yin kallon sha'awa, sai Allah ya dauke idon ya zama makaho. Amma kuma sai ya zama daidai wannan aka dasa bom, ya tashi, ya kone.

Wannan lamari na kwace birnin Kudus da kuma abin da ke kewaye da wannan wurin kasa ta Palasdinu, shekara da shekaru an mai da abin tamkar kawai siyasa ta jinsi da kuma lunin fata kawai da ''yan kasancei. Kulum in ana maganar, sai a dinga batun Larabawa da yahudawa, kouma Palasdinawa da Isra'ilawa, wato an mai da abin al'amari ne na kasa da kasa, ko kuma na jinsi da jinsi. In aka ce al'amarin na kasa da kasa ne kenen kai mutumin Nijeriya kai da ba Bapalasdine ba, ba Bajodane bane ba Bamisre ba, ba Balarabe ba, kila sai ka ce, to ai kai me ya hada ka da rigimar kasa da kasa, abin da bai shafe ka ba? Kasar wasu aka kwace kai kuma ba kasarka bace.

In kuma aka ce jinsin Larabawa da Yahudawa ake fada, kai ba jinsin Larabawa bane, ba kuma Bayahude bane. To, amma al'amarin shi ne ba wadannan mahangu biyu bane ke da muhimmanci ba. Wannan al'amari mahangarsa shi ne na addini. Wannan shi ne sahihin magana. A wannan kuwa, duk musulmin da ke gabas da wanda yake arewacin duniya ko yake kudancinta, to ya shafe shi. Ko ko, ko da rigimar masallacin Babri a Ayodiya za ka ce kai bai shafe ka ba, ai tsakanin Hindu da musulmi ne na Indiya? Hindu suna neman su kawar da wannan masallacin su gina dakin tsafi, saboda haka sai ka ce kai ba Hindu ba, kai ba musulmin Ayodiya bane? Ai ka ga ba za ce haka nan ba. Tunda dai aka ce masallaci ne ake so a rushe a gina matsafa, to ko ina kake, musulmi kake, ya shafe ka. Da kai a ciki. Wanda kuma ya rusa masallaci a Ayodiya, in ya ga na A.B.U ba zai kyale ba. To ballantana wannan Masjidil Aksa ne wanda Allah Ta'ala ya ambace shi a Alkur'ani. Wanda ma saboda girman wannan masallaci, ba wani Annabi cikin Annabawa, tun daga Adamu har ya zuwa Manzo na karshe, mai tsira da aminci wanda bai da dangantaka da wannan masallaci.

Don haka ne ma Allah Ta'ala ya dauki Manzon nan mai tsira da aminci ya kai shi wannan wuri, ya nuna masa ayoyinsa. Daga nan ya yi mi'iraji da shi. Ya zo a ruwaya cewa yayin da ya isa mallacin, sai ya samu dukkanin Annabawa sun yi sahu, da ma suna jiran Liman ne kawai ya zo. Da zuwansa, ya wuce gaba ya yi musu salla. Wannan shi ne ya tabbatar da cewa shi ne Limamin Annabawa. To a wannan wuri ne wannan abu ya auku. To ka ga wannan wuri mai tsarki a wajen musulmi, sai ya zama shi ne wai aka kwace, kuma wadanda suka yi hakan sune makiya addinin nan, wanda Allah Ta'ala ya gaya mana cewa su za mu samu sun fi nuna tsananin gaba da kiyayya gare mu. Allah yake cewa: "Za ka samu wadanda suka fi nuna tsanananin gaba ga wadanda suka yi imani, to sune Yahudu da mushrikai." To, amma Yahudawa aka fara gabatarwa. Don haka muna iya cewa babu wanda ya fi nuna wa musulmi gaba fiye da Yahudu. Haka nan ne. Alkur'ani ya riga ya zo da wannan.

To sai ya zama wannan masallaci mai daraja kuma yanzu yana hannun shi Bayahuden ne. Ba ma kawai yana hannunsa bane, a'a har ma yana keta alfarmar wannan masallacin, ta yadda zai shiga da kazantar da ke jikinsa na kafirci da butulcii, baya ga ma janaba da ke tare da shi, sannan ya kutsa masallacin da bindiga; wanda yake masallaci ko ba Masjidil Aksa ba, ko wannan masallacin ne, ko da wane irin masallaci ne, an hana a shiga da makami, ko da wuka ce. Sai ya zama za a shiga da bindiga mai sarrafa kanta a dinga bindige musulmi. Kuma ba ma kawai a bindige musulmin ba, a'a musulmin nan salla yake, sallar ma yana sujada. Haba!! Ta yaya wannan al'amari zai zama tsakanin Larabawa da Yahudawa, ko ko Palasdinawa da Isra'ilawa? Al'amari ne da ya shafi kowannenmu, al'amarin da ya shafi imani da kafirci.

Baya ga wannan kuma, har wala yau mutanen nan wani ayyanannen manufa ce tasu, wadda suka bayyana cewa nufinsu shi ne su gusar da wannan masallaci su gina dakin bauta irin nasu. To mun sani Allah Ta'ala ya aiko da Annabi Musa da addini na gaskiya (ya saukar masa da Attaura), amma bayan zuwan wannan Manzo, Ataaura ta gushe. Ko da Annabi Musa ne, yanzu abin ya dawo, ba abin da zai yi aiki da shi face abin da Manzon nan ya zo da shi. Wannan ma Manzo ya tabbatar da shi, inda ya ga wani rike da wasu warkoki na Attaura, ya bata rai ya ce ko da Musa (AS) yana tsakaninku a yanzu, ba zai bi wani abu ba face abin da na zo da shi. To ko da Musa ne ya zo, Alkur'ani zai bi, kuma alkiblarmu zai bi, kuma shari'armu zai yi aiki da ita. Saboda haka butun addinin Annabi Musa (AS), zamaninsa ya riga ya wuce. Ko masu dikiri ma sukan kawo wani dikiri kuma ya goge wancan.

Yanzu kana iya dauko tsarin mulkin da aka yi aka samu 'yanci a Nijeriya na 1960 ka ce shi ne za ka yi aiki da shi? In ka duba sai ka ga a cikin wannan tsarin mulkin akwai jihohi guda uku a Nijeriya, yanzu ko guda nawa ne? Ka ga ai wannan tsarin mulkin ya riga ya wuce. Saboda haka kenan ko da saukakken addini ne daga Allah, in Allah Ta'ala ya kawo wanda ya goge shi, wanda ya goge shi din da shi za a yi aiki ba wancan ba.

Ballantana ma su Yahudu ba addinin Annabi Musa suke bi ba, su tun tuni suka bar addinin. Kuma tuni suka sha tsinuwa daga bakunan Annabawan da suka biyo baya. "An tsine wa wanda suka kafirta daga bani Isra'ila a bakin Dawud da Isa dan Maryam." Ka ga wadannan Annabawa duk sun riga sun tabbatar da tsinuwa a kansu. Mutane ne da tun tuni suka fandare daga addinin nan da Annabi Musa (AS) ya zo da shi, saboda haka ko dama addini sahihi suke so su kafa, ba zai yiwu a gusar da masallaci wanda ya doru a kan ibada da shari'ar Manzon Allah, mai tsira da aminci a kafa na Musa ba; ba zai yiwu ba. To, ballantana ma a ce za a gusar da shi a kafa wani irin daki na surkulle.

Da ma can sun ce wannan masallaci kowa yana da hakki a ciki, tsakanin mu musulmi da Yahudawa da kirista. Saboda haka, musulmi su je ranar Juma'a su yi Juma'a, Yahudawa su je ranar Asabar su yi surutu, kuma shi ma kirista ya je ranar Lahadi ya yi nasa. Kuma in har ya kasance ana yin haka nan, ba mamaki mutum yana salla sai ya ga Arna sun shigo da takalmi a kafafuwansu sun zo za su yi waka. Sai su ma su ce ranar ibadarsu ce.

Wannan al'amari na Kudus, wanda kullum ake neman sawwala shi zuwa cewa wani al'amari ne wanda ya shafi wadansu jinsin mutane ko wadansu kasashe, to yanzu su da kansu ma sun yi watsi da wannan din. Sun fara ba shi ma'ana daban. Sun fara ba shi mahangar addini. Alal misali yanzu zancen nan da muke yi akwai mutane fiye da 400 wadanda aka kore su daga kasar haihuwarsu aka bar su a wani irin dajin Allah. Ba don komai ba, sai don su musulmi ne. Su wadanda suka kore su, da can suna cewa suna korar Palasdinawa 'yan ta'adda ne, amma wannan karon ba su ce sun kori 'yan ta'adda ba, sai suka ce sun kori masu kishin addinin Musulunci. Ka ga ashe su ma da kansu sun yi ma abin fassara ta addini, wanda yake ko wanda yake da ma yana ganin abin ba na addin ba, to yanzu an ba shi wannan. Su ma da kansu sun ayyana cewa ba abin da ya fi ba da barazana gare su illa addinin Musulunci. To da ma mana, ko ma ba su fada ba, mun san wanda ke kokarin ya rushe masallaci, ai ya ayyana da me yake fada.

Wannan lokaci namu mun dauke shi ne ya zama lokacin juyayi. Ba mu samu yin juyayinsa a Ramadana ba saboda akasari a lokacin muna i'itikafi, amma muna kara'insa a yau. Wato yau za mu biya wannan rana ta Kudus domin juyayin nan ya zama ya tabbata a zukatanmu. Wato yana da kyau yazama musulmi kowane lokacin ya kwana ya tashi yana da tunannin wannan. Ko da takaici kake yi ya zama dai akalla dai bai fice daga zuciyarka ba. Ballantana ma dai wani abu ne da ya zama tabbas cewa ba wani irin nau'in zalunci da ya taba dawwama. Ko ba dade, ko ba jima, wata rana kasar nan da ake ce wa Isra'ila sai ya zama ba ta kawai. Yau ta shekara 45, to ba yana nufin ta dinga zama abadan sarmadan ba, wata rana za a neme ta a rasa.

Har wala yau kuma ko ba dade, ko ba jima, masllacin nan na Al'aksa zai dawo hannun musulmi kamar yadda ya kasance a hannunsu. To amma wannan ba yana nufin zai zo bisa hadari bane. Kawai sai a wayi gari a ce, "ka ga da ko da Yahudawa a nan, amma ka ga ba su." Ko a ce, "ya zo nan ya yi harbi, amma ka ga yau da safe na ga ba shi."

Ba bisa hadari zai kasance ba, dole ne sai an yi kazar-kazar a namu bangaren. Dole ne wato ya zama muna da kumajin kwatar wannan masallacin. Mu ba da iya gudummawarmu, kuma Allah Ta'ala ya ba mu nasara. Amma ba za mu zauna kawai mu ce wata rana dai masallacin zai zo hannunmu kawai, sai wata rana kawai ya zama namu ba, ina!!

Dole ne ya zama wato ta namu bangaren ma sai mun yi wani irin fafatawa. Dole ne ya zama mun zauna da burin cewa, sai mun kwace wannan masallaci. Kuma bayan burin, wanda yake a zuci ne, dole mu yi wani abu, ko yaya na yunkurin ganin mun kwato shi. Da ma namu shi ne wannan fafatawar daidai gwargwadon iko. Kuma nasara daga Allah take.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International