Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426
Bugu na 690
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Bush da Blair ne manyan 'yan ta'addaIn ji Shugaban Zimbabwe, Robert MugabeGShugaban kasar Zimbabwe, Mista Robert Mugabe, ya bayyana Shugaban kasar Amurka George W. Bush da Firaministan kasar Birtaniya, Mista Tony Blair a matsayin manyan 'yan ta'addan duniya wadanda ke son mallakar duniya kamar yadda Hitler ya yi. |
Mugabe ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a babban taron Hukumar bunkasa aikin gona da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) da aka yi a Rome ta kasar Italy.
Mugabe ya kauce daga asalin jawabin nasa na kare matsayinsa na canje-canje cikin tsarin mallakar kasa wanda ya jawo cece-kuce, musamman a kasar Birtaniya, inda ya shiga magana kan Bush da Blair.
Mugabe ya ce, bai kamata duniya ta zura ido ta bar wadannan mutanen marasa tsarkin tunani su yi irin yadda Hitler da Mussolini suka yi a baya ba.
Haka nan kuma, Mugabe a wani bangare na jawabin nasa ya nuna cewa Bush da Blair ba sune za su ayyana Shugaba a kasar Zimbabwe, ko Venezuela, ko Iran, ko Iraki ba.
Tunda farko dai Amurka da kasashen Turai sun nuna rashin amincewa kan yadda aka gayyaci Mugabe zuwa wajen taron na Majalisar Dinkin Duniya.
Daruruwan mabiya addinai marasa rinjaye a Iran sun gabatar da wani gangami a gaban ofishin jakadancin Birtaniya da ke Tehran babban birnin kasar don nuna rashin amincewarsu kan irin yadda Birtaniyan ke kalubalantar lamarin nukiliya na Iran.
Mabiya addinan na Iran da suka yi wannan jerin gwano, sun hada da mabiya addinin Zorosta, kiristocin Armenia, kiristan Ashuri da dai sauransu.
A lokacin jerin gwanon nasu, sun rika daga tutoci dauke da rubutun nuna goyon baya a kan lamarin makamashin nukiliya na kasar Iran da kuma yin tir da matakan Ingila da Turai.
Haka nan kuma masu jerin gwanon sun fitar da wata takardar bayan taro, inda suke kara jaddada manufofinsu. Suna masu cewa mabiya addinai marasa rinjaye a Iran, suna tare da gwamnatinsu, kuma a shirye suke su kare martabar kasar ta fuskar siyasa da tsaro.
Iran dai ta sha bayyana matsayinta na mallakar makamashin nukiliya don amfani da shi ta hanyar ci gaban kasar, kuma ta dauki wannan a matsayin wani hakki nata. An gabatar da 'yan sanda uku a gaban kotu a Amurka
Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta fara wani bincike don kare hakkin wani bakar fata dan shekaru 64 da haihuwa da 'yan sanda suka yi masa duka a birnin New Orleans, inda guguwar Katrina ta daidaita.
Wannan bincike da aka ba da sanawarsa a ranar Litinin din nan da ta gabata, ya biyo bayan wani hoton bidiyo ne da aka nuna a gidajen talabijin, da ya nuna wasu 'yan sanda biyu cikin kaki a birnin New Orleans suna dukan wani mutun mai suna Robert Davis a fuska, da kuma sauran jikinsa lokacin da suka kama shi bisa zargin ya sha barasa ya fito bainar jama'a yana watangaririya.
Hoton bidiyon ya nuna wani dan sanda kuma ya kama wuyan wani ma'aikacin talabijin, wanda ya dauki hoton lokacin da suke dukan Robert Davis.
Shi dai Mista Davis ya ce bai sha giya ba a lokacin da suka tare shi. Ya ce ya fito ne neman taba sigari ne kawai suka kama shi.
Ya fada wa gidan talabijin na CNN cewa; wannan al'amari ya faru ne lokacin da yake magana da wani dan sanda da ke kan doki, sai wani dan sanda ya sa musu baki. Sai ya ce wa dan sandan wannan ba daidai bane. Shi kenan sai dan sandan ya harzuka.
Lauyan Mistan Davis, Joseph Bruno ya ce, Mista Davis ba ya jin cewa 'yan sandan sun masa wannan dukan ne don shi bakar fata ne.
'Yan sandan uku farar fata ne, an gan su a bidiyo a gaban kotu, suna cewa ba su aikata laifi ba. Tuni dai aka dakatar da su daga aiki, sai yadda hali ya yi.
Mista Robert Davis yana bayani game da dukan da suka yi masa
Majalisar dokokin Iran ta fitar da wata doka da ta tanadi dakatar da wasu kudurori da Hukumar kare makaman nukiliya ta duniya (NPT) ta gindaya mata, saboda mai da martani kan matakan kokarin kai ta gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Wannan doka da Majalisar ta fitar za a mika ta zuwa ga Majalisar kare tsarin mulki ta kasa, sannan bayan nan su kuma za su kai dokar zuwa ga Majalisar gwamnatin kasa don zartarwa.
Wakilai 162 cikin gaba dayan wakilai 231 na Majalisa ne suka kada kuri'ar yarda da dokar, yayin da wakilai 42 suka kada kuri'ar kin amincewa da ita, sannan kuma wasu 15 suka rike kuri'unsu.
A wani gefen kuma, Hnas Blix, tsohon Shugaban Hukumar makamashi ta duniya (IAEA), ya bayyana cewa kokarin hana Iran hakkin mallakar makamashin, wani nau'in mulkin-mallaka ne.
Tsohon Shugaban Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniyan, ya kara da cewa; matakan da kasashen Turai suka dauka kan shirin kasar Iran na makamashin nukiliya domin ayyukan zaman lafiya ba shi da bambanci da na zamanin mulkin-mallaka.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na AL'ALAM mai watsa shirye-shiryensa ta hanyar tauraron dan Adam da harshen Larabci a Tehran, Hans Blixs, tsohon Shugaban Hukumar ta IAEA, ya bayyana cewa a daidai lokacin da kasashen Turai suka fake da cewa kasar Iran tana da wadataccen mai da iskar gas domin amfanin al'ummarta da hakan ya sa suka bukace ta da ta sake nazari game da batun shirinta na sarrafa sinadarin uranium da take yi, sai ga shi ba su ce uffan ba ga sauran kasashe kamar irin su Mexico, duk kuwa da yawan arzikin mai da iskar gas da suke da shi.
A nasa bangaren, Shugaban Hukumar makamashi na kasar Iran, Gulam Ridha Oga Zad, a lokacin da yake bayani game da matakan nuna bambanci da wasu kasashe suka nuna game da shirin na kasar Iran, ya jinjina cewa da dama daga cikin kasashen da suka amince da matakin baya-bayan nan da Hukumar makamashin ta duniya ta dauka, suna da makaman kare dangi, kuma suna karya yarjejeniyar nan ta hana kerawa da yaduwar makaman kare dangi, wato NPT.
A ranar 7 ga watan Oktoba na shekara ta 2001 ne, shekaru hudu da suka gabata, Amurka karkashin shugabancin George W. Bush, tare da kawayenta suka fara kai hare-haren ta'addanci kan al'ummar kasar Afghanistan.
Rahoton tashar talabijin na BBC, ya nuna cewa Ministan watsa labarai na Palasdinu, kuma mai shiga tsakanin wajen sasantawa, Nabil Shahath, ya tabbatar da cewa Bush a lokacin wannan hari, ya fito fili ya nuna cewa Allah ne ya umurce shi da ya kai wadannan hare-haren, kuma ya ce yaki ne mai tsarki a kan dukkanin kirista.
Nabil Shaath, ya fadi haka ne a lokacin wata hira da aka yi da shi a wani shiri na talabijin din BBC mai suna 'Sulhu mai daure kai: Yahudawa da Larabawa.'
Nabil Shahath ya ce, wannan ne ya sa tun a farkon harin da Bush ya kai Afghanistan masana ke ta bayyana cewa wadannan hare-haren na ta'addanci da ake kai wa kasashen musulmi ya yi kama da yakin 'Salib,' wanda aka yi a tarihi.
Ya ce sai dai a halin da ake ciki yanzu, wani shiri na Yahudawa wanda Amurka ke goyon baya, na auka wa dukkanin wasu Cibiyoyi na addini da sunan cewa 'yan ta'adda ne, ya fara aiki a wasu kasashe na musulmi kamar irin su Pakistan.
Amma wasu na tambaya kamar haka cewa, menene ta'addanci? Kai hari kan al'umma, ko kuwa kare kai daga harin?
Babban Malamin addinin Musulunci na kasar Iraki, Ayatullah Ali Sistani ya yi kira ga dukkanin wakilansa da mataimakansa na kusa da kada su sanya sunayensu a matsayin 'yan takara a zabubbukan da za a gabatar a kasar nan gaba.
A ranar Lahadin nan ne ofishin Ayatullah Sistani a Iraki ya fitar da wani jawabi, inda yake nuna cewa dukkanin wakilinsa da ya saba wa wannan umurni, to zai sauka daga wakiltarsa.
Wasu daga cikin masana lamurran siyasa na Iraki sun fassara wannan mataki da Ayatullah Sistani ya dauka da cewa yana iya kawo cikas ga wasu daga cikin 'yan takarar, musamman ma wadanda suka yi amfani da matsayin Malamin a lokacin zaben da ya wuce.
A wata ganawa da jami'in ofishin na Ayatullah Sistani ya yi da manema labarai, ya tabbatar da cewa wannan mataki da Sistani ya dauka bai kore matsayinsa ba na kiran al'umma zuwa ga tarayya cikin zaben da za a gudanar.
Sai dai shi Ayatullah Sistani ba ya son tsulmawa cikin siyasar rarraba da kungiyoyi a kasar ta Iraki.
Ana sa ran fara zabubbukan kasar Iraki ne dai daga 15 ga watan Disamba na wannan shekara ta 2005.
Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |