Almizan :Izala za ta hade kuwa? ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426                 Bugu na 690                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Izala za ta hade kuwa?

Dakta Gumi ya yi tsinuwa

Daga Aliyu Saleh


o.
kazimiya

   

A tafsin da ya gabatar na ranar Litinin din nan da ta gabata, Dakta Ahamd Abubakar Gumi ya bayyana irin kai kawon da yake yi don gani kungiyar Izala da ta dade a rabe ta hade sun daina kafirta juna, sun ci gaba da bin jiya salla da kuma yi wa juna sallama, cin yankan juna da kuma aura daga juna kamar yadda addinin Musulunci ya tanatar.

Sai dai kamar yadda ya bayyana, fatan da ke tattare da hadewa tsakanin bangarorin na Izala da suka kwashe shekara da shekaru suna gaba da juna ya karanta. Kamar yadda ya ce, duk wani kokari da ya kamata ya yi don gani ya sasanta su ya yi, amma abin yana neman ya faskara.

Dakta Ahmad Gumi, ya nuna damuwa matuka a kan yadda 'yan Izalar suke jan kafa wajen kin yarda a hade a manta da bambance-bambancen da ke tsakaninsu duk muhimmancin da yin haka yake da shi.

Ya ce tun zuwan da ya yi na bara ya yi ta kai gwauro yana kai mari don ya sasanta su, amma hakan ya ci tuta. A aikin hajjin da ya gabata ma sai da ya yi kokarin hada kan 'yan Izalar don su hade su ci gaba da tafiya tare don fuskantar matsalar da ke gabansu, amma duk da haka hakarsa ta gaza cimma ruwa.

Dakta Ahmad Gumi ya nanata cewa duk da sasantawar ta gaza yiwuwa a kasa mai tsarki, takanas ta Kano ya je har Jos domin shawo kan mutanen Jos din su manta da duk wani al'amari su yarda su hade da 'yan uwansu 'yan Kaduna juna, amma suka ki yarda.

Ya nuna damuwarsa matuka a kan yadda 'yan Izalar Jos din suka yawo da hankalisa da kuma gindaya sharadin sai 'yan tawaye ('yan Kaduna) sun tuba sun dawo sun yi biyayya kafin su yarda a hade. ya ce idan ma haka ne ai Sama'ila Idirs suka yi wa tawaye ba jagororin yanzu ba.

Ya ce, amma yayin da ya sami 'yan Kaduna a lokacin da suke gudanar da wani taron kara wa juna sani a Sakkwato a kan batun hadewar, nan take suka yarda suka ba da kai.

Dakta Ahmad Gumi ya zargi 'yan Jos da son shugabanci da neman girma da kuma kin yarda a hade. Ya ce yanzu lallashi ya kare, za su hada kan Izala su ci gaba da tafiya tafe, ko da kuwa wasu sun ki yarda.

Ya ce abin da ya tayar masa da hankali shi ne yadda wasu kauyawa suka ziyarce shi suka ce sun ji labarin an hade tsakanin Izala, suna neman izinin bin juna salla da kuma yi wa juna sallama kamar yadda suke yi a da. Ya ce duk da ya sanar da ''yan Jos wannan al'amarin suka yi biris suka kememe suka yarda su ba su wani batu da zai karfafa masa guwiwa.

Dakta Ahmad Gumi, wanda ya zargi 'yan siyasa da ruwa da tsaki a cikin rabuwar kungiyar Izalar. Ya ce, abubuwan da ya shiga tsakanin 'yan kungiyar ba wasu muhimman abubuwa bane. Ya ce, duk matsalolin da suke rigima da ta jijiyar wuya a kansu wasu matsalalin ne da ba su kai sun kawo ba, "ba wanda ya hana bin mai yin sallama biyu salla."

Ya ambata cewa nan gaba kadan zai kira wani gagarimin taro don dai a dinke barakar da ke tsakanin 'yan Izalar, tare da sake rubata sabon tsarin mulki kungiyar da kuma yin sabon tsarin da zai yi waje da duk wanda bai yarda da matsayar da aka cimmawa ba.

Ya mai da martani mai kaushi a kan wadanda suke zarginsa da wuce makadi da rawa wajen la'antar duk wanda bai yarda da batun hadin kan da za a yi ba. Ya ce ba shi ya fara la'antar irin wadannan mutanen ba, Allah da Manzanninsa da kuma jama'a muminai ne suka fara la'anatar mutanen da suke raba kan al'ummar Manzon Allah. Ya sake nanata cewa; "Allah ya la'anci wanda duk ya ki yarda da wannan hadin kan har zuwa ranar ta'ashin alkiyama." Ya nanata haka har sau uku.

Dakta Gumi ya ce, ba zai sausatawa 'yan Izalar ba, tunda Mahaifinsa (Shaikh Abubakar Gumi) da ya sausauta masu ba su yarda sun hada kai waje daya. Ya ce da yawansu ma suna sukar sa, ba su ma amfani da littafin tafsirin da ya rubuta wajen karatuttukansu.

Ya hori Izalawan Jos da su guji neman zama jakunan da makiya Musulunci za su su hau su yi amfani da su wajen raba kan al'ummar Annabi Muhammad (S). Ya ce, yin hakan ba kawai zai kawo koma baya ne ga addinin Musulunci ba, hatta su ma ba za su girbi alheri ga barin hakan na ci gaba da faruwa ba.

Sai dai wasu da Wakilinmu ya zanta da su a wajen tafsirin, sun tabbatar da cewa duk da wannan tsinuwar da kuma kurarin hana ko korar duk wanda ya ki yarda da wannan shirin sulhun daga Izala da Dakta Ahmad Gumi ya yi, ba zai iya hadan Izalawan. Ya ce da yawansu sun huda gardin rarrabuwa. Wasu kuma da ita suke cin abinci, "don haka ba yadda za a yi su yarda a hada kai waje daya," in ji shi.

Wani da ya je wajen daga Zariya kuwa cikin fushi cewa ya yi, ya lura Dakta Ahmad yana neman ya jagaranci almajiran babansa ne da wayo. Ya ce tunda shi Shaikh Abubakar gumi ya gaza hada kan Izalawan, shi ma Dakta Ahmad zai yi ya gaji ya bar su.

Amma duk da haka wasu suna ganin matsayawar Dakta Ahmad din ya matsa kaimi ya kuma ci gaba da jawo su a jika ba tare da mai da kowanne bangare 'yan bora ko mowa ba, kila ya iya hade kansu waje daya.

Komawa babban shafinmu        Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International