Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426
Bugu na 690
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
|
|
Alhaji Rufa'i ya kuma shaida wa Wakilin namu cewa a halin da ake ciki dai yana da kungiyoyi a karkashinsa masu neman Gwamna Ahmad Sani ya fito takara a 2007 har kimanin kungiyoyi sama da 40. Ga dai yadda hirar tasu ta kasance:
ALMIZAN: Idan aka yi nazarin yadda al'amuran siyasa ke tafiya a Nijeriya, shin wane hanzari ne kuke da shi har ya sa kuke kiran Yarima da ya fito ya nemi Shugaban kasa a 2007?
ALH. RUFA'I HASAN: A'uzu billahi minas shaidanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. Idan ka lura da yadda kasar nan take ciki akwai matsalar wahalhalu na tafiyar da rayuwa ga al'ummar kasar nan. Jin dadin rayuwa sun yi karanci kwarai da gake. Misali abinci da kuma bangaren ilimi da kuma wasu bangarorin da suka shafi kiwon lafiya, ba da ruwa ga karkara da giggina tituna. Sannan akwai wadansu abubuwa wadanda ke da sha'awar rungumar al'umma domin ci gaba, dalilin haka ne ya sa muka ga ba wanda ya cancanta ya yi wannan jagoranci sai Yariman Bakura, Alhaji Ahmad Sani, domin ya yi a jihar Zamfara mun gani.
Sannan kuma irin wadannan ayyuka kamar jini ne a gare shi tunda na san shi tun da dadewa yana da sha'awar kyautatawa da rungumar al'umma domin bai nuna bambanci a tsakanin 'yan uwansa na kusa da wadanda ba ma na kusa ba. Duk yana da sha'awar ya ga ya taimaka ma jama'a su kasance cikin walwala da jin dadi a tafiyar da rayuwarsu.
ALMIZAN: A lokacin Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kawo ziyara a jihar Kaduna, duk kan hanyar da ya bi, an bi duk an ciccire takardun da ke dauke da hotunan Yarima da kuma manyan alluna wadanda aka kakkafa su a muhimman wurare, da zane-zanen hutunan Yarima a jikin gidajen mutane wadanda kuma suna tallata shi ne a matsayin dan takara. To sai muka sami labarin an ce gwamnatin jihar Kduna ce ta sa duk a ciccire wadannan hotuna. Da yake kana jagorantar wannan gwagwamaya don ganin cewa Alhaji Ahmad Sani Yarima Bakura ya fito ya yi takara na Shugaban kasa a 2007, shin yaya kuka ga wannan al'amari, wanda duk an bi an maye su da na PDP. Shin me za ka ce a kai?
ALH. RUFA'I HASAN: To, alhamdulillahi, in ka duba wani abu ne wanda mutane ba su san manufar a yi abu yadda ya dace ba, musamman yadda Nijeriya tana da'war mulkin dimokradiyya. A ce wai don wani dan takara da mutane ke yin kira da ya fito ya yi takaran Shugaban kasa, ba a sha'awar a ga wata alama tasa. Idan ka duba wadanda suka aikata wannan, mutane ne wadanda ba sa sha'awar dimokradiyya, sun fi son mulkin kama-karya, ko kuma sun fi son wani yanayi wanda sai sune za a ce sun yi fice. Wannan in ka duba rayuwar duniya gaba daya, musamman dai nan Nijeriya da yake babu wani tsari na cewa gwamnatin tarayya ko kuma gwamnatocin sun fitar da wani tsari na cewa daga lokaci kaza zuwa lokaci kaza bai dace wani dan takara a ga hotonsa a kan hanya ba, babu wannan tsarin.
Saboda haka a ce wai za a hana wani dan takara ya sa hotonsa, kuskure ne. Inda a ce akwai doka ne, kamar yadda wasu kasashe suke yi a duniya, lokaci kaza ne ake nuna ba a son a ga hoto, to ka ga babu wata hujja da Malam zai je ya sa hotonsa a kan tituna. Amma a Nijeriya a halin da ake yanzu duk wanda ya ce zai hana hakan, to ya yi kuskure.
ALMIZAN: A lokacin da wannan abu ya faru, wata daga cikin kungiyoyinku, wato "Yarima Solidarity Association" ta yi barazanar za ta kai gwamnatin jihar Kaduna kara a kan wannan abu da gwamnatin ta sa aka yi wa hotunan na Yarima. Ba mu sani ba ko kuna da masaniya a kan hakan. In kun sani, shin an kai kotun ko kuwa me ake ciki?
ALH. RUFA'I HASSAN: A'a, wato abin da ya faru shi ne in har sun yi yunkurin zuwa kotu suna da hujja, domin babu wata doka kamar yadda na ce tun farko, wadda ta hana wani dan takara kada ya manna hotunansa ko ya bayyana ra'ayinsa a kowane lokaci a wannan kasar.
ALMIZAN: A kwanakin baya akwai lokacin da wasu kungiyar limamai suka kai wa Gwamna Yarima ziyara. Cikin jawabin nasu sun bukace shi da ya fito ya yi takara a 2007, to a lokaci kamar shi Gwamna ya amsa musu cewa zai fito takarar. To bayan wannan kuma sai ga shi muna ganin labarai cewa ana rokon sa ya fito ya yi takaran. Shin menene ake ciki, ya amsan ko kuwa zai dai amsan ne?
ALH. RUFA'I HASAN: To Alhamduhillahi. Ita dai rayuwa mataki-mataki ce, ka fara daga nan kuma za ka bar nan don ka kara gaba. To ga dukkan alamu kuma a namu tunani da namu hasashe, in Allah ya so zai tsaya takaran Shugaban kasa.
ALMIZAN: Yawancin mutanen da ke kudancin kasar nan wadanda ba musulmi ba a halin yanzu suna sukar Yarima saboda shari'ar Musulunci da ya kawo, shin yaya kuke ganin wannan tafiya ta Yarima, musamman a kudancin kasar nan?
ALH. RUFA'I HASAN: Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura mutum ne mai kishin addininsa, kuma ba zai yiwu ba ya ce zai iya hana wani wanda ba musulmi ba ya yi kishin nasa addinin, amma ana son mutum mai kishin addini a tsari irin na Nijeriya ya kasance shi ne jagora, koyaushe Kiristoci suna da 'yanci. Allah ne ya hada mu da su kiristoci a Nijeriya, babu wata hujja da za a ce a hana Kirista ko musulmi yin addininsa yadda ya dace. In ma ka duba a Nijeriya musulmi shi ne aka tauye ma 'yancin addininsa.
ALMIZAN: Akwai masu yin zarge-zarge da dama wanda aka sani su 'yan asalin jihar Zamfara ne, sun sha kalubalantar shi Gwamna Ahmad Sani cewa yadda ya fito din nan yana neman takaran Shugaban kasa, to kamata ya yi idan an zo jihar Zamfara ya nuna kyawawan ayyuka wadanda ya yi don inganta rayuwar al'ummar jihar, musamman ta bangaren samar da ruwan sha, kiwon lafiya, wutar lantarki a karkara da kuma uwa-uba giggina hanyoyi domin hade kauyuka da manyan tituna. Komai za ka iya cewa a kan wadannan zarge-zargen?
ALH. RUFA'I HASAN: To, alhamdulillahi. Duk wanda ke yin wannan korafin, ko dai yana yin da'awar cewa shi dan jihar Zamfara ne ko kuma su ba 'yan jihar Zamfara bane. Domin duk dan jihar Zamfara, shekaru shidan da suka wuce ya san a jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura a shekara ashirin da za a yi nan gaba ba za a yi irin ayyukan da ya yi ba a cikin shekaru shidan nan.
ALMIZAN: Mun ga kungiyoyi da dama suna ta bullowa domin tallata Yarima ya fito takara a 2007. Shin ya zuwa yanzu kana da kungiyoyi nawa ne a karkashinka?
ALH. RUFA'I HASSAN: To ya zuwa yanzu dai akwai Kungiyoyi daban-daban a karkashin kungiyata, wadda ita ce uwar Kungiyoyin gaba daya, muna da Kungiyoyi sama da arba'in, wadanda suka hada da Kudu maso Gabas da kuma Kudu maso Kudu da dai sauransu. Haka kuma akwai su a yammacin Nijeriya da kuma nan Arewa maso Gabas da Arewa maso yamma da Arewa ta Tsakiya. Dukkansu muna zama muna tattauna yadda za mu yada manufofinmu da kuma tattauna matsalolinmu da muke samu.
ALMIZAN: To wadannan Kungiyoyi mun ga suna da dama da sunaye daban-daban, ba ka jin cewa ya dace a mai da su Kungiya daya mai suna daya ta yadda zai fi dacewa su kasance suna magana da murya daya a cikin kasa, maimakon karkasuwa?
ALH. RUFA'I HASAN: To, idan ka lura da wannan, ai kusan da a ce duk yanayi ne irin na Nijeriya wanda yake kowane bangare yana bukatar a gano shi yana yin wani abu. Wannan shi ne dalilan da suka sa muka zura masu ido. Haka nan za a yi tafiya har a kai lokacin da jam'iyya za ta tsayar da Alhaji Sani Yarima Bakura ya tsaya takara, to a lokacin duk wadannan Kungiyoyin duk kuma sai a koma karkashin jam'iyya. In Allah ya so.
ALMIZAN: Akwai masu ganin cewa da Yarima da shi Janar Buhari suna jam'iyya daya ne wato ANPP, kuma kowa na kallon cewa shi Janar Buhari shi ne jigo na adawa da kuma takaran Shugaban kasa a jam'iyyar ANPP, kusan haka 'yan ANPP suke cewa, kuma don haka wasu ke zargin cewa Gwamna Alhaji Ahmed Sani ana ganin kamar ya zo ne ya bata ruwa ba don ya sha ba. Kome za ka ce ga masu irin wannan ra'ayi?
ALH. RUFA'I HASAN: To, alhamdulillahi kodayaushe idan ana irin wannan maganar nakan so in tattauna ta a bangare daban-daban. Janar Muhammad Buhari a 2003 shi aka tsayar a dan takaran Shugaban kasa, kuma alhamdulillahi ni na sani shi Yarima yana daya daga cikin wadanda suka yi ruwa suka yi tsaki wajen ganin an tsayar da Janar Buhari a lokacin. Sannan kuma a ce Yariman Bakura ya fito ne don ya bata ruwa ba don a sha ba, wannan magana ba ta da tasiri.
Yariman Bakura mutum ne wanda yake a kodayaushe yana kokarin ya ga ya fito da abin da yake al'ummar Nijeriya za su yi na'am da shi kuma talaka zai dara.
ALMIZAN: To ya dangantakarku take da shi Janar Buhari?
ALH. RUFA'I HASAN: Dangantakarmu da shi lafiya lau take. In ka duba sati biyu da suka wuce (a lokacin da aka yi hirar) ya je Gusau, inda ya sadu da Yarima kuma har aka sanya wa wani masallaci sunan Muhammadu Buhari Mosque a lokacin da ya ziyarci bikin bude shi.
ALMIZAN: Ko yaya karfin ita wannan tafiya take a kudancin kasar nan a yanzu?
ALH. RUFA'I HASAN: To alhamdulillahi, ga kiddigar da muka yi, ya zuwa yanzun, muna da wajen kashi arba'in ne na magoya baya a yanzu.
ALMIZAN: Ko kana da wani abin da za ka ce domin ka jawo hankalin 'yan Nijeriya a kan su goyi bayan wannan yunkuri da kuke yi na ganin ya fito don ya yi takaran Shugaban kasa a 2007?
ALH. RUFA'I HASAN: To abin da zan ce ko kuwa zan yi kira ga 'yan Nijeriya shi ne mu duba mu ga yadda Nijeriya take a yanzu, matsalolin more rayuwa kamar yadda na fara da farko musamman a kan abin da ya shafi tattalin arziki, idan ka dubi matsalar karin kudin mai da Nijeriya ta yi da kiraye-kiraye da kuma kuma tsare-tsaren gwamnatin tarayya, ya kamata a ce gwamnatin tarayyar ta fito da wani tsari wanda ko da ta yi karin kudin mai din 'yan Nijeriya zai rage masu fitinar rayuwa.
Haka kuma idan aka zabi Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura za a ga tsari wanda zai shafi talaka tun daga kasa har ya zuwa sama. Kamar idan ka dubi tsarin shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ta bullo da shi, koyaushe ana daukar samfur ne, wato ana koyi ne da jihar zamfara domin lokacin da aka fito da yaki da rage talauci a jiha, lokacin gwamnatin tarayya ba ta yi nata ba, Alhaji Ahmed Sani Yariman Bakura shi ne ya fara wannan tsare-tsaren rage matsalolin sufuri. Yariman ne ya fara kafin wasu jihohi da gwamnatin tarayya ma su yi. Sannan karin albashi, ita kanta gwamnatin jihar Zamfara, musamman shi Alhaji Ahmad Sani, shi ne ya fara shi kafin wasu Gwamnonin su yi.
Kuma akwai fannoni da dama dai idan ana maganar su a yanzu Nijeriya aka dubi babu wani mutum daga cikin masu jagoranci a Nijeriya, musamman Gwamnoni wanda yake yana da wata hangen nesa na hangen talaka kamar wanda ya kai na Alhaji Ahmad Sani Yarima Bakura.
Saboda haka ne ya sa muke yin kira ga Alhaji Ahmad Sani da ya fito ya ceci al'ummar Nijeriya, domin shi mutum ne wanda yake tun kafin ya soma tunanin zai zama Gwamna yake tunanin matsalolin da talaka yake ciki. Shi ya sa yana daga cikin abin da ya kara masa kwarin gwiwar ya rungumi aikin gona domin talauci da yunwa sun yi kamari, musamman a wannan bangare namu na Nijeriya. Abin da ya shafi karancin abinci da sutura da kuma wasu abubuwa na more rayuwa da rashin aikin yi, cikin ikon Allah, Alhaji Ahmad Sani idan ya zama Shugaban kasa zai cika burin 'yan Nijeriya.
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |