Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426
Bugu na 690
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
|
|
Ranar Asabar din da ta gabata ne aka yi wani mummunan hadarin jirgin sama a kauyen Lisa da ke Karamar hukumar Ifo cikin jihar Ogun, inda duk fasinjoji 117 da ke cikin jirgin suka rasa rayukansu.
Wani mazaunin kauyen, mai suna Mista Akinlabi Ojo ya shaida wa manema labarai cewa lokacin da abin ya faru sun sun dauka wani tashin duniya ne ko kuma hari a aka kawo wa Nijeriya, saboda wata irin kara da suka ji, wadda ba su taba jin irin ta ba.
Ya ce; "jiya Asabar da misalin karfe 8.30 na dare muka ji wani sauti mai karar gaske. Mun dauka ma bom ne."
Mista Ojo ya kara da cewa, "da muka wayi gari da safen nan, sai muka ga wani bakin hayaki daga nesa da mu. Nan da nan sai muka shaida wa Sarkin kauyenmu. Shi kuma nan take ya aika da jama'a zuwa ga ofishin 'yan sanda na Sango."
Shi dai wannan mummunan hadari, bayan da aka gano wurin da abin ya faru, jama'a sun yi ta tururuwa zuwa wajen domin ko za su iya gano wadanda suka sani.
Amma sai dai abin bai kasance haka ba, domin babu wanda za a iya ganewa a cikin wadannan mutane, saboda ba abin da ya rage na jikkunansu, komai ya yi watsa-watsa.
Kauyen da jirgin ya fado ba shi da hanya mai kyau, ita kanta mataimakiyar Gwamnan Ogun, Alhaja Salimot Badru da ta isa kusa da kauyen sai da ta hau acaba ta iya karasawa inda jirgin ya fado.
Masharhanta kan al'amuran yau da kullum sun rika tambayar ina amfanin tauraron dan Adam (satalayit) da Nijeriya ta yi ta kurin ta harba a bara, in har za a shafe awowi 16 bayan faduwar jirgin kafin a gano inda yake?
Wani al'amari da wannan hatsari ya bayyanar shi ne yadda a Nijeriya mutum na iya shiga jirgin sama ba da sunansa na gaskiya ba. Wato abin da kan faru akwai fasinjojin da sukan sayi tikiti wajen 'yan cuwa-cuwa (taut), wadanda aikinsu sayar da tikitin wani wanda ko dai ya fasa yin tafiyar, ko kuma dai kawai yana son a kara masa riba.
A irin haka ne wani Bala Halilu, wanda ya tabbatar wa matarsa cewa yana cikin jirgin, sai ga shi ba shi a cikin jerin sunayen da ke hannun kamfanin jirgin na Bellview.
Tun kafin jirgin ya tashi ya yi wa matarsa irin wasikar wayar GSM (text) ya ce: "ke na samu shiga da sunan wani. Jirgin ya cika ta yadda ba yadda na iya in ba in saya wajen 'yan cuwa-cuwa ba. Amma wa ma ya damu? Burin dai ba shi ne mutum ya kai inda za shi ba? Ba komai, in na isa zan kira ki. Kaftin dinmu ya ce yanayin sararin samaniyar ba kyau, don haka tafiyar za ta wahalar, amma in dai zai iya tafiyar, ai ni ma zan iya."
To matsalar da irin wannan cuwa-cuwar tikiti za ta haifar ita ce idan za a ba da diyya ga iyalan mamatan, ta yaya iyalan mutane irin su Bala Halilu za su samu hakkinsu?
Jama'ar Nijeriya da dama sun nuna damawarsu a kan yadda gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta fifita mutuwar matar Shugaban gwamnatin farar hular kasar nan, Stella Obasanjo, fiye da mutanen da suka rasu a hadarin da jirgin saman kamfanin 'Bellview' ya yi, wanda ya kashe mutane 117 da ke cikinsa.
Masu lura da yadda al'amura suke gudana a Nijeriya, sun bayyana cewa yawancin kafafen yada labarai da kuma manyan jami'an gwamnati, ko don neman gindin zama ko kuma don dai wata manufa ta daban, sun fi nuna damuwa da alhini game da mutuwar Stella duk da kuwa ba wanda ya san dalili mutuwarta.
Duk da cewa hatsarin jirgin saman da aka yi ya faru ne ranar Asabar, amma jami'an gwamnati ba su nuna wata alamar wani abu na faruwa ba, hasalima sai ake ta yawo da hankalin 'yan Nijeriya game da yanayin hatsarin da adadin yawan mutane da suka rasu da kuma inda aka yi hatsarin. Da yawa daga cikin kafafen yada labarai mallakar gwamnati sun ci gaba da watsa shirye-shiryensu kamar yadda suka saba.
Sai dai yayin da labarin mutuwar Stella ya iso ranar Lahadi, sai kafafen yada labaran, mallakar gwamnati suka dakatar da watsa shirye-shiryensu da suka saba, suka ci gaba da watsa wasu ayyuka da Stellan ta gabatar a lokacin da take raye, musamman shirin nan nata na tallafawa yara nakasassu. Ayyukan gwamnati da kuma hada-hada ta siyasa suka tsaya cik, abin da dama daga cikin mutane suka nuna damuwarsu a kai.
Sai dai yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Abuja game da zargin da ake yi na cewa an fi nuna damuwa game da rasuwar Stella Obasanjo fiye da yadda aka damu da rayukan mutane 117 da suka rasu a hatsarin jirgin saman 'Bellview,' Ministan yada labarai, Mista Franka, ya karyata wannan zargin. Ya ce a wajensu duk 'yan Nijeriya daya ne ba wani da aka fi nuna damawa a kansa fiye da wani.
A wata hira da ya yi da sashin Hausa na muryar Amurka (VOA) a farkon mako, fitaccen marubucin nan da ke Kaduna, Malam Muhammad Haruna ya ce, matsawar haka ta tabbata mutane ba za su tausaya wa Obasanjo ba a kan wannan al'amarin da ya same shi na rashin matarsa.
Ita dai Stella Obasanjo, 59, ta rasu ne a wani asibitin Mada ke Sifaniya lokacin da ta je can domin a yi mata kwaskwarima a jikinta, a rage mata kiba da kuma kitse a wani mataki na shiryawa gagarumin bikin cikar ta shekaru 60 da aka shirya da za a yi ranar Litinin 14 ga Nuwamba mai kamawa.
Sai dai kasancewar Stella ta je Sifaniya cikin koshin lafiya, amma aka ba da labarin mutuwarta, hakan ya jawo zarge-zarge da kuma tuhume-tuhume, inda yanzu haka kotun majistire da ke garin Marbella ta bukaci a ba ta takardar sakamakon binciken Likita na Stellar domin ta gudanar da bincike a kai.
Jakadan Nijeriya a Sifaniya, Dakta Kingsles Ebenyi, ya nuna kaduwarsa game mutuwar ta Stella da ya ce ta zo a bazata, musamman ganin yadda ta isa kasar Sifaniya cikin koshin lafiya, amma ta bukaci a duba lafiyarta a dakin shan magani na Molding Clinic da ke daura da Banus Port a kasar. Shi dai wannan dakin shan magani sun kware sosai wajen yi wa mutane kwaskwarima a jikinsu.
Sai dai kuma bayan da abubuwan suka gagara ne aka kwashi Stella zuwa asibitin USP Hospital da ke Marbella, idan kwararrun likitoci suka yi ta kai-kawo domin ceto ran "First Lady," amma abin ya gagara.
Sai dai yayin da aka tuntubi mataimaki na musamman ga Obasanjo, Mista Femi Fani-Kayode a kan wannan lamari na binciken da kotu a Sifaniya za ta yi game da mutuwar Stella, ya ki ya ce uffan.
Kodayake dai Obasanjo yana da wasu matan, kafin ya dare karagar mulkin Nijeriya a 1999, amma dai a hukumance Stella ce aka sani a matsayin "First Lady," wacce ke gudanar da abubuwa a matsayin matar Shugaban kasa. Ana jin cewa bayan an yin bikin binne ta yau Juma'a za ayyana wacce za ta gaje ta daga ciki matan nasa.
Ita dai Stella a 'yan kwanakin nan ta shiga rigingimu da dama tsakaninta da dan kishiyarta, Gbenga, dangane da wasu makudan kudade da kuma gidan da ake jin ya saya a London, abin da ya sa har ta sa aka kama kuma aka tsaye mawallafin wata jarida mai suna 'Midwest Herald,' Orobosa Omo-Ojo, sakamakon wallafa wata kasida da ya yi mai taken "Greedy Stella," wacce ke bayani game da wannan batu.
Mai magana da yawun Obasanjo, Misis Remi Oyo, ta ce an bude littafin ta'aziyya ga masu kai wa Obasanjo gaisuwar ta'aziyyar rasuwar matar tasa a Banquet Hall da ke gidan gwamnati Abuja, da kuma wanda ke Marina Lagos gami da wanda ke Otta mahaifar Obasanjo. A yau Juma'a ne dai za a rufe gawar tata a garin Abeokuta.
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |