Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426
Bugu na 690
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Shekarau ba zai sake zama gwamna a Kano ba
In ji Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda
Shugaban matasa na jam'iyyar PDP a jihar Kano, Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda, ya tabbatar da cewa Gwamnan jihar Kano na yanzu, Malam Ibrahim Shekarau ba zai sake zama Gwamna a jihar Kano ba a 2007, saboda yadda ya yaudari jama'ar jihar Kano.
"Ina tabbatar maka cewa insha Allah irin yunkurin da aka yi da kuma irin yadda jam'iyyar ANPP ta shigo da yaudara da kuma cin mutuncin mutane da karya ta addini, a wajen mutanen Kano wannan ya kare, ya kuma kawo karshe. Insha Allah wannan ba za ta sake sabuwa a jihar Kano ba," ya jaddada. Ya ce, "mun ga yadda aka yaudare mu da sunan addini. Mu da muke PDP akwai wuraren da idan muka shiga a Kano ake ce mana ga 'yan jam'iyyar kafirai nan sun shigo. Ba wanda zai sake shigowa ya yaudari mutanen Kano da sunan addini a halin yanzu. A 2007 za mu karbe kujerar Gwamnan jihar Kano." Dakta Ali Haruna Makoda, wanda ya zargi gwamnatin Malam Shearau da rashin manufa, ya ce, matsawar manyan PDP a Kano suka hade kansu waje daya kujerar Gwamna za ta dawo hannusu. Ya ce yanzu haka suna nan suna kai gwauro suna kai mari don ganin an sasanta, "kuma da yardar Ubangiji zaben da za a yi a 2007, PDP za ta karbi jihar Kano," a ta bakinsa. Ya yi watsi da duk wasu ayyuka da wannan gwamnatin take cewa ta yi a tsawon zamanta na shekarau uku, "da za ka kwatanta da zunzurutun kudaden da gwamnatin Shekarau ta karba daga gwamnatin Tarayya a shekara biyu ba wata biyu da irin ayyukan da suka yi, za su ji kunya. Kudaden da Shekarau ya karba a shekara biyu ba wata biyu, sune Kwakwanso ya karba shekaru hudu. Tare da wadannan kudaden kuma har yanzu Shekarau bai yi rabin aikin da Kwankwanso ya yi ba." Dakta Makoda ya ce, kuskure ne babba da Malam Shekarau ya ce, bai sa samar da ruwan sha, hanya, gine-gine da sauransu a cikin irin abubuwan da zai yi wa mutane Kano ba. Ya ce, ba yadda za a yi mutum ya ce shi manufar gwamnatinsa shi ne kawai gyaran zuciya da kuma gina dan Adam. Dakta Ali Haruna Makoda, ya bayyana halin da jam'iyyar PDP take ciki a Kano a matsayin wani yanayi na rashin dadi. "Sai dai dama duk wata jam'iyya da ta karbu ga jama'a dole ne irin wadannan rigingimun su rinka tasowa. Domin wasu za su ga cewa su suka isa ba wane ba. Amma dai yanzu muna nan muna kokarin mu ga an dinke wannan barakar." Sai dai Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda, ya zargi masu rigima a jam'iyyar PDP a jihar Kano da neman yi wa su matasa mugunta da neman dakile su, "su kansu manyan ni abin da nake tunani ma akwai mugunta a zukatansu, domin ba su so a daidaita jam'iyyar nan ne don kada mu taso mu tafiyar da jam'iyyar a nan gaba. Duk wani matashi da yake Kano yake jam'iyyar PDP ya san mu ake yi wa mugunta." Dakta Makoda, ya fito karara ya zargi duk gidajen nan na PDP da ke rigima a jihar Kano -na Rimi, Musa Gwadabe, Kwankwaso da Ghali Na'abba- da laifi a rigimar da PDP take ciki, "amma babban mai laifi a wannan rigimar shi ne Alhaji Abubakar Rimi. Ba wani mutum da zai tashi ya yi mika a Kano a siyasance, sai Rimi ya ce wannan mutumin ya raina shi. Duk wani da zai tashi ya zama zakara a jihar Kano, sai Rimi ya ce bai isa ba. Haka kuma bai kamata ba." Ya nuna takaicinsa a kan yadda har yanzu ba a samun jituwa tsakanin Kwankwaso da Ghali duk da kuwa dukkansu ba su kai labari ba a zaben da aka gudanar a 2003. "Kuma tunda abin da ya faru kenan kamata ya yi su zauna su sasanta tsakaninsu dumin a samu ci gaba mai amfani a jam'iyyar PDP da kuma jihar Kano," in ji shi. Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda, ya yi watsi da ikirarin da wasu mutane ke yi na cewa sun kafa wata jam'iyyar PDP mai jama'a. Ya ce, taron da suka yi a Kano ranar Alhamsi din da ta gabata ya nuna ba su da jama'ar. Jama'a suna tare da jam'iyyar PDP ta gaskiya. Ya ce, su matasa sun shirya tsaf, matsawar su manyan da ke rigima a kan PDP ba su shirya daidaita tsakaninsu ba, suna shiri su kawar da su su ci gaba da rike PDP don ci gabanta yadda ya kamata. |
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |