Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426
Bugu na 690
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
|
|
Wani kusa a cikin jam'iyyar PDP a jihar Kano, Alhaji Hamisu Danwawu, ya bayyana Alhaji Buba Marwa a matsayin dan kore, kana kuma karen farautar Shugaban Nijeriya Obasanjo.
Alhaji Hamisu Danwawu ya bayyana haka ne ga manema labarai a Kano, a cikin makon jiya, a lokacin da yake sharhi dangane da halin tsaka-mai-wuya da jam'iyyar ta shiga ciki a duk fadin kasar nan.
Alhaji Hamisu Danwawu, ya ci gaba da cewa, fitowar takarar shugabancin Najeriya da wadansu mashahuran 'yan arewa suka yi, irin su Buhari, Atiku da Babangida, ba wani abu bane da zai kawo matsala ba, domin a cewarsa, cikin su ukun, dole ne a fitar da guda daya, ba tare da la'akari da jam'iyyar da ya fito ba. Yana mai tabbatar da cewa, arewa za ta hada kanta.
Sannan kuma ya tabbatar da cewa a 2007, dole ne mulkin Nijeriya ya dawo Arewa.
Tunda farko, sai da Alhaji Hamisu Danwawu ya fito fili ya bayyana cewa, duk da kasancewarsu 'yan PDP, amma mutane masu ra'ayi irin nasa, sam ba su da ra'ayin Obasanjo da Kwankwaso. Don haka ne ma ya tabbatar da cewa ba za su taba yarda Obasanjo ya zarce ba a 2007. "Mun yarda mu mutu, domin ganin cewa Obasanjo da 'yan kanzaginsa ba su zarce ba", ya tabbatar.
Da yake kare kansa dangane da zargin da ake masa na hada kai da Gwamnan Kano Shekarau domin yi wa PDP makarkashiya kuwa, Alhaji Hamisu Danwawu ya ce, wannan wata karya ce kawai ake shararawa a kansa.
Sannan ya tabbatar da cewa, wannan zargi da ake masa ba zai sa gwiwarsa ta yi sanyi ba, yana mai tabbatar da cewa, za su ci gaba da yakar PDP har sai sun daidaita mata sahu.
Alhaji Hamisu Danwawu ya waiwaya baya, yana mai cewa, kamar yadda Allah ya dau ran Abacha, ya kawar da shi daga yunkurin zarcewa, kuma ya fitar da Babangida daga mulki yana kuka, ba tare da yana so ba, haka nan zai kawar da Obasanjo daga mulkin Najeriya.
Daga karshe, Alhaji Hamisu Danwawu ya yi fatan cewa, za a yi zaben 2007, alhali Obasanjo da 'yan kanzaginsa suna raye, kuma suna ji suna gani dole su bar mulki.
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |