Almizan :Zarcewar Obasanjo ba za ta zo masa da sauki ba ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426                 Bugu na 690                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Zarcewar Obasanjo ba za ta zo masa da sauki ba

In ji Malam Albishak
Daga Aliyu Saleh

MATAKAN DA MUKA DAUKA

a

Shi wannan abin da ya faru ya rage wa 'yan Arewa ne. Wannan fa jaridar tasu ce, ni kuma dan Arewa ne, shi Shugaban kamfanin da ya sa aka yi wannan dan Arewa ne, yanzu ya rage wa jama'a ne su ga fa abin da ke faruwa a kamfanin da Sardauna ya kafa, wanda yake manufarsa dama shi ne ya taimaka wa Arewa. Kuma Sardauna sai da ya jaddada mana cewa ya kafa kamfanin nan ne ba don komai ba sai don mu fadi gaskiya. Ya ce kuma idan kai ba ka busa naka kakakin ba, ba wanda zai busa maka. Don su 'yan Kudu suna nan suna ta busa nasu. Saboda haka Sardauna ya kafa kamfanin New Nigerian ne ba don komai ba sai don ya yada ra'ayin jama'ar Arewa, ya fito da su a fili, don a ga cewa ana girmama 'yan Arewa ana karrama su, ana ganin su da mutunci. Wanda kuma duk wasu abubuwan da muke yi muna yi ne don haka.

Misali kamar a rubuce-rubucena na filin Baitul Hikma da su Al'aleem za ka lura cewa duk wani abu da ake sukar Arewa a kansa, muke ganin cewa ba daidai bane, za ka ga muna kare Arewa. Kuma muna bincike mu shiga tarihi, mu ga cewa kafin Turawa su zo ma ina Arewa take? Don idan ka yi bincike kafin mulkin-mallaka Arewa ita ke kan gaba a komai, a tattalin arziki, a ilimi da ko ma menene. Shi ya sa lokacin da Turawa suka yi mulkin-mallaka Arewa aka ce suna da iliminsu, tsarin shugabancinsu, suna da kotuna, suna da makarantu, da ma'aikatu, komai nasu a tsare yake. Shi ya sa da Turawa suka zo sai suka ce irin mulkin da za su yi shi ne mulki-mai-shamaki, (Indirect Rule) ta yadda za su mallaki 'yan Arewa, amma ta hannun 'yan Arewan, sai su ci gaba da mulkinsu yadda suka ga dama. Sai dai duk abin da shugabannin Arewa za su yi za su karbi umurnin ne daga su Turawa.

Amma a Kudu sai suka yi mulki-na-kai-tsaye (Direct Rule), da yake da suka je babu duk irin wadannan abubuwan da muke da su a Arewa. A can ne aka kafa masu gwamnati, aka gina masu makarantu, aka gyara masu tattalin arizikin kasarsu da duk wani abu da ake da shi a Arewa tuntuni. A takaice ma a kan wannan abin ne ma ya sa daga baya aka zo aka sa 'yan Kudun suka yi galaba a kan 'yan Arewan, aka kuma fifita su a kanmu da yake su sun ba su ilimin boko, mu kuma dama can muna da iliminmu ne na Muhammadiyya. Sai aka dankwafar da wannan aka daga wancan. Shi ya sa ma da aka zo daukar ma'aikata da yake suna da ilimin boko har a nan Arewa su Turawan suka dauko (mutanen Kudu) suka zo suka mamaye Arewa, sai ya zama mu da muke a sama muka koma a kasa.

Lokacin da na fara rubutu a filina na Baitul Hikma, akwai wani tsohon Ministan shari'a a zamanin Shagari, Rechad Akinjide ya fito fili yana cewa kuskure ne ma da Turawa suka hada Arewa da Kudu a 1914. Ya ce an yi haka ne don a cuci mutanen Kudu, don mutanen Kudu suna da kudi da dukiya, amma mutanen Arewa ba su da komai, amma kawai sai aka hada mu da su don dai kawai mu je mu yi ta tatsar su. Yana ta wannan babatun ba wanda ya amsa masa. Da na ga abin da mutumin nan yake yi shirme ne, sai na je na yi bincike na tona asiri, na ce mutumin nan karya yake yi. Na ce idan kuma yana ganin yana da gaskiya ne ya fito da takardun da yake cewa Turawa sun bari a dakin karatu ko a gidajen tarihi.

Na je na yi bincike na dauko tarihin yadda Arewa ta yi kudi ta yi komai da komai na zo na fallasa na sossoke shi. Na nuna masa cewa Arewan nan fa da yake gani mu mun fi 'yan Kudu. Baicin da sa'ar da suka yi kawai da Turawa suka fara zuwa ta gefensu, kuma aka fara ba su ilimin boko, kawai ta nan aka zo aka mamaye Arewa. Na ce, amma in ba haka ba Arewa ita ke kan gaba. Na ce in ma dukiya ne Arewa tana da dukiyarta, saboda kudin da take da shi na auduga da gyada da kuza da sauransu.

BA WANDA YA YABA MIN

Tunda na fara aiki a wajen babu wanda ya taba zuwa ya taba ba ni takardar yabo banda abubuwan da mutane suke yi daga waje da kuma martanin da suke ta aikowa. Wani ma ziyara zai kawo ya ce, "Malam kuna burge mu, kuna fid da mu kunya." Amma ni tunda na fara aiki a New Nigerian babu wanda ya taba zuwa a cikin kamfanin ya ce, mutumin nan yana abin kirki bari mu aika masa da takardar yabo. Sai dai zargi da kuma bakin ciki, wanda wani yake ganin ka fi shi rawar gani.

ABIN DA YA KAMATA 'YAN AREWA SU YI

Su 'yan Arewan ba sai an gaya masu ba, tunda wannan jaridar fa ta Arewa ce, kuma kada amanta mu da muke yaki domin Arewa ba muna yaki bane domin a goyi bayan Arewa kawai ba, don dai tana Arewa, a'a, muna yi ne muna duba matsayin Arewa a cikin kasar baki daya ba, so muke kasar nan ta hadu ta zama daya. Amma kamar yadda Marigayi Sabo Bakin Zuwo, tsohon Gwamnan Kano yake cewa, Nijeriya daya ce, amma kowa ya san gidan ubansa. Mu kanmu mun yarda da cewa Nijeriya daya ce, kuma muna son zaman lafiya, kasar nan ta hadu, kuma kabilu da mutane masu bambancin addini duk muna so kowa ya hada kansa waje daya don kasar nan ta samu ci gaba.

Amma kuma yin haka din, musamman ma dai a aikin jarida, za ka ga cewa 'yan Kudu kullum suna kare bukatun mutanensu ne, mu ma Arewa ya kamata mu tashi tsaye mu kare namu mutanen. Idan fa aka samu aka wayi gari cewa 'yan Arewan su ke cin naman 'yan uwansu, wannan kuma talakawa da sauran jama'a su ya kamata su yi maganin wannan. Tunda dai shugabanninsu ai suna nan suna ganin abin da ke faruwa, tunda dai sun san tarihin jaridarsu, ya kamata su hana abin da shugabannin kamfanin suke yi idan ba daidai bane.

Yanzu misali, a matsayina ka ga sharhin da nake rubuta wa jaridar ya kawo mata kwarjini, kuma ina samo masu talla, kamfanin yana samun kudi. Yanzu duk wannan ba abin alfahari bane? Idan a kamfanin aka samu mutane da yawa wadanda za su rika rubuta sharhi ana sai da jaridar, kuma suna kawo talla, ai ka za a samu ci gaba. Amma me ke faruwa ka ga shi Manajan-Daraktan, gwamnatin Tarayya ta ba shi kyautar miliyan 200 don ya gyara kamfanin, amma har yanzu da kyar ake biyan albashi. Alhali wanda yake a wajen kafin shi, Dakta Umar Faruk Ibrahim shi gwamnatin Tarayya ta ba shi Naira miliyan 100 ne kawai. Kuma da miliyan 100 nan shi ne ya samo karin ma'aikata da kuma masu ba da shawara (irinmu), muka zauna aka gyara kamfanin, aka yi ayyukan da za su kawo kudi, kamfanin ya samu ci gaba. A lokacinsa, kuma ana biyan albashi, sai da aka kau da shi, shi wannan da ya gaje shi, Ndanusa Alao aka yi baya, duk da ya samu Naira miliyan 200. Sai kuma mu da muke ta kokarin muna ganin muna samo masu kudi aka ce mu ba a son mu. Haka nan dai kawai aka zo aka sa mana karan tsana. Yanzu ka ga watanni shida da suka wuce, duk wata sai dai ya je ya samu wani Gwamna ya roke shi a taimaka a ba shi kudi don ya biya albashi. Abin da ya kamata ya zama ana yi kenan?

Yanzu New Nigerian irin kadarorin da take da shi da kuma irin abubuwan da take da shi, kamata ya yi a ce za ta iya yin komai da kanta, ba wai duk da yake mutum ya karbi Naira miliyan 200, amma kuma yana nan yana ta bara yana neman a ba shi kudi. Ina kudin da ake samu na jaridun da ake saidawa? Ina kudin tallace-tallacen da ake samu? Ina kudin hayar gidajen da kamfanin ya mallaka? Ina kudin ayyukan da ake yi na waje da suke shigowa? Duk ina wadannan kudaden da ake samu suke tafiya? Shi kenan duk da wadannan kudaden da ake samu kullum sai dai a ce mutum yana yawo yana zuwa wajen wannan Gwamnan ya ba shi kudi, ya je wajen wancan Gwamnan ya ba shi kudi? Hakan Arewan za ta ci gaba? Don haka ya rage ga shugabanninmu da sauran 'yan uwa su ya kamata su tashi tsaye su ga an yi abin da ya kamata.

MANUFAR KAFA JARIDA

Menene manufar kafa jarida? Manufar kafa jarida shi ne ta yada labarai, ta fadi abubuwan da suke faruwa a kasa. Sannan kuma tana yin sharhi, wanda idan ta ga ana yin wasu abubuwa ba daidai ba ta yi kiran a gyara. Misali, kamar a ce yin sharhin da muka rubuta, ba an ce dauke ABUTH aibi bane, amma cewa aka yi kada a yi shi cikin garaje. Ka ga wannan ai shawara ce ba suka bane. Ita jam'iyyar PDP da take son ta saba wa tsarin mulkin jam'iyyarta da ba ta son ta yi zabe, ka ga wannan ai bai dace ba, kuma mu mun gaya mata ne ta yi abin da ya dace. Kuma ko ranar Litinin da ta gabata akwai kotun da ta yanke hukuncin cewa abin da jam'iyyar PDP take so ta yi ba daidai bane. Shi kenan sai a cire alkalin da ya zartar da wannan hukuncin? Saboda haka ka ga a kyale mutane haka nan, Shugaban kamfani ya rika yin abin da ya ga dama, yana neman ya sai da kamfanin ga shugabannin da ke mulki, ka ga bai kamata ba. Ya kamata mu san akwai Allah fa. Shi ya sa ni wannan abin da ya faru ne nake tawakkali.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International