Almizan :Burin Obasanjo da kwankwaso kashe PDP ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426                 Bugu na 690                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Burin Obasanjo da kwankwaso kashe PDP

Inji Alh. Gambo Dan-pass

Daga Ali Kakaki kakakis@fastermail.com

yaron

An bayyana karfa-karfa da take tsarin mulkin jam'iyar PDP da Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da 'yan korensa irin su Ministan tsaro, Rabi'u Musa Kwankwaso suke yi da cewa burinsu su kashe jam'iyyar PDP a zaben 2007. Alhaji Muhammadu Abdullahi Gambo Dan-pass mai neman shugabancin jam'iyyar PDP na jihar Kano ne ya bayyana haka a yayin zantawarsa da ALMIZAN a ranar Asabar din makon da ya gabata a Kano.

Alhaji Gambo ya ce a matsayinsa na mai neman shugabancin jam'iyya da kuma kokarin ganin an magance barakar da ke damun jam'iyyar a jihar Kano saboda kawai yana adawa da kokarin tazarce da Obasanjo yake son yi a 2007, an hana shi sabon katin shaidar dan jam'iyar PDP a mazabarsa ta Karamar Hukumar Gwale. "Dama magoya bayan Obasanjo tazarce ne kawai ake yi wa wannan kati, shi ya sa ma Alhaji Abubakar Rimi ya ki yarda a yi masa katin, don haka ni ma ba na bukatar sa," a ta bakin Dan-pass.

Haka kuma ya ci gaba da cewa, Kano kamata ya yi a ce an kawo mata sabon katin nan kamar miliyan uku ko hudu, sai aka kawo wadannan adadin, shi ne zai wadaci 'yan jam'iyya. A kawo ya samu, amma sai dubu biyar kacal suka kawo, ka ga su burinsu jam'iyyar PDP ta karye, ta wargaje saboda ba son jam'iyyar suke yi ba.

Alhaji Dan-pass ya kara da cewa, "tunda Obasanjo da 'yan korensa irin su Kwankwaso marasa kishin halin da talakawan kasar nan ke ciki a halin yanzu illa kawai kare mukaminsu babu ruwansu da halin da talakawa da arewa ta shiga a wannan mulki na Obasanjo, tunda yake sun dauki wannan mataki, to mun san Allah ba ya zalunci. Saboda haka ga mu ga su ga Allah nan; suna da Shugaban kasa, muna da Allah."

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International