Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426
Bugu na 693
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
|
Alamieyeseigha, wanda ke kan beli, an ce ya isa kauyensu, Amasoma da misalin karfe 2:00 na dare ranar Lahadi, sannan ya shiga cikin babban birnin jihar, Yenagoa cikin jerin gwanon motoci masu yi masa rakiya da misalin karfe 9:25ns. Cikakken bayanin yadda aka yi ya tsero, kamar na Gwamnan jihar Filato, Cif Dariye suna nan cikin sirri, amma sannu a hankali bayanan sai fitowa suke daga bincikenmu kan yadda ya iya ba da jami’an tsaron Birtaniya da na kasar nan har ya dawo jiharsa. A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai shi Gwamnan Bayelsan ya ki kai kansa ofishin ’yan sanda da ke London kamar yadda sharuddan belinsa ya nuna cewa zai rika yin haka a kullum wayewar garin Allah. Kashegari ’yan sandan cikin London da aka sa su su sa ido a kansa sun iya gano shi a wani gida da ke bayan otal din Hilton a London Park lane. Amma an ce ya bar gidan a wannan rana tare da wata mata matashiya, inda ya shige wani gidan da ke Peckham Street ya kwana. Kashegari kuma Lahadi, jami’an tsaro cikin farin kaya sun ga wasu mata biyu sun bar wannan gidan da ke Peckham, amma sai daga baya bayan ta tabbata Gwamnan ba shi gidan suka kai ganon cewa ashe ‘daya matar’ da suka gani Alamieyeseigha ne. Yayin da yake ba da haske kan yadda Gwamnan Bayelsa ya tsero daga London, Shugaban Hukumar yaki da aikata laifukan da suka shafi zambar kudade, EFCC, Malam Nuhu Ribadu, ya tabbatar da cewa Gwamnan shigar mata ya yi, ya kuma yi amfani da takardun tafiye-tafiye na jabu ya dawo kasar nan. Kodayake Ribadu ya ki yin karin bayani don kar ya kawo cikas a binciken da ake yi kan al’amarin, amma an ce wani mutumin kabilar Ijaw ne ya sa ma wa Gwamnan fasfo din jabu, wanda da shi ya yi amfani ya fice daga Birtaniya. Amma akwai bayanai masu karo da juna da ke nuna yadda ya shigo Nijeriya. Majiyoyin gwamnati sun ce ya shigo jirgin British Airways ne, amma wani rahoton na cewa ya shigo irin jirgin musamman din nan ne da akan yi hayarsa. Wani dan kabilar Ijaw da ake jin ya taka muhimmiyar rawa wajen ficewar Gwamnan, tuni ’yan sandan birnin London suka cafke shi. Akwai wani rahoto da ke cewa wasu na kusa-kusa da Gwamnan su hudu suka kitsa dabarar ficewar Gwamnan tare da hayar wani kamfanin tsaro na Birtaniya. A fadar gwamnatin jihar da ke Yenagoa kuwa, Gwamna Alamieyeseigha, wanda ya yi magana da harshen Ijaw ga dimbin jama’ar da suka zo yi masa maraba da dawowa, ya nuna matukar godiyarsa ga jama’ar jihar, musamman ma mataimakinsa, Dk. Goodluck Jonathan, wanda ya ce ya rike jihar yadda ya kamata. “Na yi kwanaki 65 ko kamar haka cikin duhun takura da azabtarwar wata kasar waje. Amma na gode Allah Madaukaki da ya sa wannan matsala da na shiga ta tausasa ni, kuma ina rokon Allah ya sa ’yan Nijeriya su amshi kaddarar Ubangiji a rayuwata. Yau ina kara tabbatar da kasantuwata dan Nijeriya,” cewar Gwamnan. Ya kara da cewa, “A yau na dawo kan kujerata, har abada ina mai nuna shirina na bauta wa mutanen Bayelsa da Nijeriya. Na gode wa Allah saboda kariyarsa. Ina godiya ga Bayelsawa, Ijawa da dukkan ’yan Nijeriyan da suka tsaya a bayana.” Manyan mutanen jihar na cikin wadanda suka yi wa Gwamnan maraba, ciki har da Cif Melford Okilo, Gwamnan farar hula na farko na tsohuwar jihar Ribas, ’yan majalisar masarautar jihar karkashin Basarake Joshua Igbagara da kuma Gwamnan mulkin soja na farko na tsohuwar jihar Ribas, King Alfred Diete-Spiff da wasu da dama. A titunan garin Yenagoa kuwa, matasa ne ke ta murna a kan mashina da motoci dauke da korayen ganyayen itatuwa. Wasu matasan kuma sun toshe gidan gwamnatin jihar da ke Creek House suna jiran ’yan sanda da kuma jami’an EFCC da aka ce suna kan hanyar zuwa jihar daga Abuja don kama Gwamnan. Matasan sun yi rantsuwar za su bijirewa duk wani kokari na kama Gwamnan. Dawowar Gwamnan ta shammaci jama’a da dama, ciki har da Mataimakin nasa da ya zama Gwamnan rikon kwarya, Dk. Jonathan Goodluck, wanda aka ce a sa’ilin dawowar Gwamnan ma yana cikin taro da wasu manyan mutane don samun goyon bayansu. Lokacin da Gwamna Alamieyeseigha ke wa jama’a jawabi ne ma, Gwamna mai rikon kwarya ya same shi suka gaisa, daga nan suka tattauna. Amma cikin wadanda suka tarbi Gwamnan tunda fari akwai Kwamishiniyar ayyukan mata, Remi Kuku, kawun Gwamnan, Abel Ebifeomwi da aka fi sani da ‘TO’. Sauran sun hada da mataimakin Kakakin majalisar dokokin jihar da aka tsige, Jephatath Foihgha. Amma a wani labari da ya iske mu yayin rubuta labarin nan, tuni Majalisar dokokin jihar ta mika wa Gwamnan da ya tsero takardar sanarwar tsigewa. Alamun cewa kamar Gwamnan ya fado ne daga tandun tuya zuwa cikin wuta. Komawa babban shafinmu Komawa saman wannan shafin
| |
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International
|