Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426
Bugu na 693
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Shari'ar Wamakko da Almizan
Almizan na neman Naira miliyan 117
Ranar Talatar da ta gabata ne aka kira karar da Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aliyu Magatakardan Wamakko ya kai ALMIZAN domin a fara sauraronta karkashin alkalancin Mai Shari’a Dogara Malam a wata babbar kotu da ke Dogarawa Zariya. Sai dai ba a sami damar fara sauraron wannan kara ba saboda rashin halartar shi Magatakardan, wanda, kamar yadda Lauyansa ya yi wa kotun bayani, Magatakardan bai sami daman halartar kotun bane sakamakon ziyarar da Shugaban gwamnatin mulkin farar hular kasar nan, Cif Olusegun Obasanjo ya kai zuwa jihar. Amma sai dai Lauyan ya shaida wa kotun shawarar cewa duk ranar da aka sake sanyawa, Mataimakin Gwamnan da wasu biyu za su halarci kotun domin gabatar da jawabansu. Tuni dai Mai shari’a Dogara Malam ya sanya ranar 17 ga Fabrairun 2006 ran da za a ci gaba da sauraron karar. Tun kafin wannan rana ne dai Lauya mai kare Kamfanin ALMIZAN da sauaran wadanda ake kara, Lauya M.D Abubakar ya gabatar da jawaban kariya bisa tuhumar da aka yi wa wadanda yake karewa. Sannan ya bukaci kotun ta umurci Magatakardan ya biya diyyar N117,801,335.00 ga ’yan uwa uku da ya sa aka kashe, wadanda aka raunata da kuma wadanda aka barnata wa dukiya. Lauayan ya kasafta wadannan kudade da za a biya diyya kamar haka: Mutane uku da aka kashe, kowanne za a biya diyyar N8,013,995.00 a matsayin diyyar rai da kuma kudin jana’iza. Sannan su kuma ’yan uwan aka jikkata su 153 jimla za a biya su diyyar N1,134,630.00. ’Yan uwa 19 da aka kama aka tsare a Sakkwato ba tare da hakkinsu ba, Lauyan ya bukaci a biya su diyyar N2,981,634.00. Sannan ’yan uwan da aka barnata wa dukiya su 80, Lauya M.D Abubakar ya bukaci a biya su diyyar N89,043,088.00, wanda jimlar wadannan kudade ya zama N117,801,335. Cikin jawaban kariya da Lauyan ALMIZAN din ya hannata wa kotun, ya nuna cewa duk jawaban da aka buga a wannan jarida game da Mataimakin Gwamnan, suna bisa gaskiya domin a lokacin da abin ya faru shi ne ke rikon shugabancin jihar, zai iya hana a yi abin da aka yi, amma sai ya ki, ya kyale su suka ci karensu ba babbaka. Lauyan ya ce a lokacin da ake yin wannan abu, Mataimakin Gwamnan ya fito a fili a rediyon sashen Hausa na BBC ya bayyana cewa ’yan uwa musulmi suna tayar da fitina don haka sai an yi maganinsu ta kowane hali. Don haka wadannan kalamai sun kara wa ’yan ta’addan nan kwarin gwiwar aiwatar da abin da suka yi. Cikin karar da Wamakkon ya gabatar ya nuna cewa ba a ji ta bakinsa ba kafin a rubuta labaran da aka yi a kan shi. Lauyan ALMIZAN ya karyata wannan zargi, inda ya bayar da tabbacin cewa daya daga cikin wakilan jaridar ya nemi jin ta bakinsa a Kaduna lokacin da ya je wani taro, amma ya ce ba zai yi magana a kan wannan batu na rikicin Sakkwato ba. Lauyan ya kuma nuna cewa duk da koken da Magatakardan ya yi na cewa ba a yi masa adalci a labarin da aka buga ba, to ita jarida tana da ikon ta buga labarin da ta tabbatar da ingancinsa domin jama’a su san halin da ake ciki, wato abin da ya kira a turace ‘priviledge and quality information which it is entitled to publish.’ Jawaban kariyar da Lauayn ya gabatar suna da dama wanda ba za mu iaya kawodukkansu a nan ba. Bayan da Lauyan ya gama bayar da jawaban kariya, sai ya shiga jera bukatunsa ga kotun, wanda a ciki ya kara tabbatar da wadancan labarai da jaridar ta buga. Ya kuma nuna cewa an yi wa ’yan uwa ta’addancin da aka yi masu ne saboda kalaman da Mataimakin Gwamnan ya yi a lokacin da yake rike da kujerar Gwamnan jihar lokacin da Gwamna Alhaji Dalhatu Attahiru Bafarawa ba ya kasar, wanda shi Mataimakin Gwaman ya hada kai da ’yan iskan gari suka karkashe tare da jikkata da ’yan uwa da dama da barnata dukiyoyin da dama. Bayan da ya gama lissafa wadannan ne da ma wasu, sannan sai ya bukaci a biya wadancan diyya da ya lissafa a baya. Komawa babban shafinmu Komawa saman wannan shafin
| |
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |