Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426
Bugu na 693
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
|
|
Wadansu mutane ne wadanda ba a san ko su wanene ba suka zo gidan wannan bawan Allah da misalin karfe 8:00 na dare, inda suka tarar da ’yarsa a kofar gida tare da saurayinta suna hira, suka tambaye ta shin ko Malam yana cikin gida? Sai ta ce masu yana ciki. Sai suka ce mata ta yi masu sallama da shi. Sai ta shiga ta yi sallama da Malamin.
Bayan Malam ya fito ne sai suka koma gefe, kai ka ce wata maganar arziki za su yi. Kafin ka ce me, sai kawai suka harbe shi a kafa. Ji kake tas! Sai Malam Abdullahi ya yi wani kara, sai suka kara harbin sa a ciki.
Ganin Malam Abdullahi ya fadi, sai su kuma suka ranta a na kare. Daga nan aka dauke shi sai asibiti. To a nan ne Allah ya yi masa cikawa.
Wata majiya ta shaida wa ALMIZAN cewa wadannan mutane sun dade suna zuwa gurin wannan bawan Allah, tun kimanin shekaru biyu da suka wuce.
Majiyar ta shaida mana cewa Malamin ya taba gaya masu cewa shi fa wadannan mutanen bai yarda da su ba, saboda haka zai tashi daga nan zai koma garin Minna ta jihar Neja, amma jama’ar unguwa suka ce masa bai kamata ya tashi ba. Shi kuma sai ya hakura bai tashin ba.
Haka ma a ranar da abin ya faru, wata majiyar ta shaida mana cewa sai da suka bugo wa Malamin waya cewa suna nan zuwa.
To, da yake Malam Abdullahi mutum ne mai hulda da jama’a dare da rana yana ba da taimako irin na Malamai, idan an bugo masa waya cewa Allah ya gafarta Malam zan zo lokaci kaza, ko kuma za mu zo lokaci kaza, ba zai damu ba.
Amma hasashen da ya fi karfi kan ko su waye makisan shi ne cewa wasu masu kisa da sunan addini ne suka bulla.
Don kuwa akwai wani aminin marigayin da ake kira Malam Arab, wanda shi ma mai ba da taimako ne na Malamai a Abuja road da ke Rigasa, amma aka samu wasu suka rubuta masa wasikar gargadi da barazana kamar haka: “Muna neman tsarin Allah daga sharrin Shaidan tsinanne. Da sunan Allah Mai rahama, Mai jin kai. Wannan wasika ce daga Sarkin muminai zuwa ga boka Arab. Aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya. Muna kira gare ka da kira na tauhidi, ka musulunta, ka musulunta. Allah (T) Yana cewa: “Kuma suka bi abin da Shaidanu ke karantawa a kan mulkin Sulaimanu…” har zuwa inda Allah ya ce “Kuma lalle ne hakika sun sani tabbas, wanda ya saye shi ba ya da wani rabo a cikin lahira. Kuma tir da abin da suka sayar da rayukansu da shi, da sun kasance suna sani.”
Kuma Manzon Allah ya ce “Duk wanda ya je gun boka, ko ya gaskata shi kan abin da ya fada, to ya kafirce wa abin da aka saukar wa Muhammad (S) .” Ka sani cewa bokaye kafirai ne bisa ijma’in musulmi.
Don haka idan wannan takarda ta same ka, ka tuba zuwa ga Allah Madaukaki, idan kuwa ba ka tuba ba, ka sani cewa Allah Mai iko ne a kan ya yi maka ukuba.”
Ba jimawa da ba shi wannan takarda, kuma suka nufo shi da harbi cikin dare, shi ma ya mai da martani, suka gudu, kamar yadda muka samu labari.
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |