Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426
Bugu na 693
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
>Bukin nuna tsiraici a Abuja zai lashe Naira milyan 600
|
|
Ya bayyana haka ne sa’ilin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan shirye-shiryen da ke kasa kan wannan gagarumin taro a ranar Alhamis 17 ga Nuwamba, 2005 a wani taron manema labarai.
Kodayake Ministan ya bayyana cewa wannan buki, ba buki ne na nuna tsiraici kamar yadda wasu masu sukar sa suka nuna ba, amma ana ganin da wuya ya samu karbuwa wajen masu adawa da gudanar da bukin a Abuja.
Wasu masu sukar bukin suka ce ai ko daga sunan bukin na ‘carnival’ za a iya fahimtar inda aka dosa, don kalmar tana da nasaba da maguzancin Bature tun kafin zuwan kiristanci, musamman kuma da a yanzu al’adun mutanen kasar Birazil ya shigo ciki.
Kungiyar kiristoci ta Nijeriya, CAN, ita ce kungiyar da ta soma yin kiran a dakatar da bukin, saboda a cewarta, ya saba wa dokokin addinin kirista.
Daga baya kuma kungiyar Jama’atu Nasril Islam, JNI, ta bi sahu ta yi tir da bukin, ta kuma nemi da a dakatar da shi.
Haka kuma mashahurin marubucin nan a jardar Daily Trust, Adamu Adamu, ya shafe makwanni biyu yana ta bayyana adawarsa ga wannan buki tare da hujjoji kwarara.
Duk da haka dai, kamar yadda aka san gwamnatin Obasanjo da kunnen kashi, ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, shirye-shiryen bukin ya yi nisa, cikin masu halarta kuma har da mutanen Birazil.
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |