Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426
Bugu na 693
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Yadda EFCC ta cafke Husaini Jalo
Hukumar da ke yaki da cin hanci da zarmiya, EFCC, ta cafke, sabon Shugaban Hukumar Asusun Bunkasa Fasahar Hako Man Fetur ta Kasa, (PTDF), Alhaji Husaini Jalo, bisa tuhumar da ake yi masa da rub-da-ciki a kan wasu makudan biliyoyin Nairori. Majiyoyi masu tushe daga hedikwatar Hukumar PTDF da ke Abuja, sun tabbatar wa da ALMIZAN cewa, da yammacin ranar Alhamis din nan da ta gabata ne, jami’an Hukumar EFCC suka yi awon gaba da Alhaji Husaini Jalo, suka nausa da shi wajen da suke ajiye wadanda suke tuhuma da ke hedikwatarsu da ke Laegas don a yi masa tambayoyi. A karshen watan Yulin da ya gabata ne dai aka nada Alhaji Husani Jalo, wanda yake tsohon Kwamishinan muhalli da filaye ne na jihar Kaduna a matsayin Babban Sakataren Hukumar PTDF, bayan an damke wanda ke kan matsayin a da, Alhaji Hamisu Abubakar Mai Rago bisa tuhumar da shi ma ake yi masa ta yin handama da babakere. Wasu ma’aikata a Hukumar PTDF sun bayyana cewa jami’an Hukumar EFCC su uku ne suka fara zuwa Hukumar PTDF suna son ganin ‘Babban Sakataren.’ Bayan sun cike wasu takardu aka yi masu zagi don isa gare shi. Wani da yake wajen, ya ce ya lura lokacin da wani jami’an Hukumar ta EFCC yake yin waya yana cewa, “mun same shi! Yana nan!” Ba a jima ba, kuma sai ga wasu motoci kirar Fijo 406 gudan uku cike da ’yan sanda dauke da makamai sun yi wa ofishin Hukumar kwanya. Majiya tamu ta ce lokacin da ’yan sandan suka shigo harabar Hukumar PTDF din, jami’an da suka fara zuwa sun shiga ofishin Alhaji Husaini Jalo, wanda a lokacin yana shan shayi, suka bayyana masa abin da ke tafe da su. Ba a jima ba suka fito da shi suka cusa shi a daya daga cikin motocin da suka zo da su, suka fice daga harabar Hukumar ta PTDF. Wasu bayanai na sirri da muka samu daga ofishin Hukumar EFCC, sun tabbatar da mana da cewa, ana tuhumar Alhaji Husaini Jalo ne, wanda ya taba rike mukamin Shugaban Karamar Hukumar Igabi har sau biyu, da laifin karkatar da wasu makudan kudade da yawansu ya zarta Naira miliyan 80 a zaman da ya yi na Babban Sakataren Hukumar PTDF. Kazalika kuma mun samu labarin cewa, Hukumar EFCC tana zargin Alhaji Husaini Jalo, wanda yake na hannun daman Gamnan jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Makarfi ne da laifin sayen wasu maka-makan motoci kirar jef guda shida, wanda kowace daya kudinta ya haura Naira miliyan 20, kuma ya sa masu jiniya suna yi masa rakiya a duk inda zai shiga. Wata majiya mai tushe a gidan gwamnatin jihar Kaduna, ta tsegunta wa ALMIZAN cewa, kafin a kai ga kama Alhaji Husaini Jalo, sai da aka sanar da Gwamna Muhammad Makarfi irin ta’asar da “yaron nasa” yake tafkawa a Hukumar PTDF, amma sai Makarfi ya ce, ana iya kama shi idan dai ana da tabbacin zargin da ake yi masa. Wasu da suke tare da Alhaji Husaini Jalo dai sun bayyana cewa a tsawon kwanaki 150 din da ya yi a kan mukamin, ya rinka yin facaka da kudi fiye da kima, tare da yin sayayya marasa kan gado, gami da bayyana cewa shi zai gaji Makari a 2007. Wasu da muka zanta da su sun bayyana cewa suna jin shigo-shigo ba zurfi Makarfi da na kusa da shi suka yi wa Alhaji Husaini Jalo. “Ka ga dai yanzu shi da Mai Rago ba su da sauran ta cewa a siyasar jihar Kaduna a 2007. Yanzu sai wanda Makarfi ya ce zai bai wa mukamin tunda dama su biyun nan sune barazana a wajensa,” in ji wani dan jihar Kaduna. Wasu ma’aikata a Hukumar PTDF da aka zanta da su sun bayyana cewa lokacin da Alhaji Husaini Jalo ya dare kan mukamin Babban Sakataren Hukumar PTDF ya kori wasu da yake jin suna da dangantaka da wanda ya gada, Alhaji Hamisu Abubukar, sai dai duk da haka akwai wasu da bai iya gano su ba, kuma sun ci gaba da sa masa ido da kuma lura da duk kai-kawo da facakar da yake yi. Ana jin irin su ne suka tsegunta wa Hukumar EFCC halin da ake ciki, tare kuma da gabatar wa Hukumar da kwararan shaidu da dalilan da zai sa Jalo ya gaza fitowa da wuri. Amma wata majiya ta shaida mana cewa shi kuwa Mairago ya samu sa’ida a yanzu, don kuwa ba a tsare a hannun EFCC din yake ba, yana dai zuwa kai rahoton kansa ne. Wata sanarwa da Sakataren gwamnatin Tarayya, Cif Ufot Eksette ya fitar, ta ce an nada tsohon dan takarar Gwamnan jihar Yobe a jam’iyyar PDP, kuma tsohon Shugaban Hukumar yaki da talauci ta Nijeriya, Alhaji Adamu Wazari a matsayin wanda zai gaji Alhaji Husaini Jalo wanda ke hannun Hukumar EFCC a Legas. |
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |