Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426
Bugu na 693
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
|
|
Babban mai taimakon Gwamnan jihar Zamfara kan al’amuran da suka shafi kafafen watsa labarai, Dakta Halliru Andi ya bayyana cewa duk masu kushe gwamnatin Ahmad Sani Yariman Bakura da cewa ba ta yi aikin komai ba, ba su yi wa kansu da gwamnatin jihar adalci ba.
Ya kuwa bayyana haka ne a gaban editocin wasu jaridun Hausa guda takwas a ofishinsa da ke gidan gwamnati a Gusau a makon jiya sa’ilin da ya gayyace su ziyarar gani da ido da kuma tattaunawa da Gwamnan jihar.
Dakta Halliru Andi ya ce, “ko su ’yan PDP din da suke cewa Gwamna Yarima bai yi aiki ba, to ina tabbatar muku, kuma zan kai ku ku gani, har titunan mota Mai girma ya yi a kofar gidajensu da na iyayensu a nan birnin Gusau.”
Ya ce amma babbar nasarar da suka samu ita ce ta kafa shari’a wacce ya bayyana ta da “dutsen da masana falsafa suka rasa, amma Gwamna Ahmad Yarima ya samo musu ita.”
Sannan kuma ya ce, jihar Zamfara ce ta fara yaki da cin hanci da rashawa a duk fadin tarayyar kasar nan, domin kuwa shi ya fara bayyana kaddarorinsa yana hawa mulki, ya kuma bayyana su a lokacin da wa’adin mulkinsa na farko ya kare. “Kuma wadannan bayanai a bayyane suke ga duk mai son bincikawa,” ya ce.
Dakta Halliru ya ce duk wani yunkuri na kawar da cin hanci da rashawa dole ya fara fada da karuwanci, shan giya, rashin aikin yi da caca. “To sanin kowa ne cewa fara hawa mulkin Yarima, abin da ya fara fada da su kenan,” in ji shi.
Daga nan ya shiga bayanin irin ayyukan ci gaba da Gwamnan ya yi a cikin tsukin shekaru shidan da ya yi yana mulkin jihar. Ya ce ta bangaren ruwan sha, wanda yana daga cikin manya-manyan matsalolin da suka addabi jihar, musamman garin Gusau, Gwamna Ahmad Sani ya gina dam, wanda yanzu haka akasarin garin yana samun ruwan sha, wasu kuma ana kan aikin shimfida musu bututun ruwan.
Daga nan ya yi wata tambaya ya ce, “A duk fadin biranen kasar nan, musamman manyan birane irin su Kano, da Kaduna ina ne ba a karancin ruwa? Amma me ya sa mutane sai su danne nasu su hango na jihar Zamfara?”
Har ila yau babban mataimakin Gwamnan kan harkokin da suka shafi watsa labarai ya bayyana wa editocin jaridun na Hausa cewa idan aka duba ta bangaren kyautata jin dadin jama’a da kuma samar da ayyukan yi, to suna iya bugun kirji su ce duk fadin tarayyar Nijeriya babu kamar Gwamna Ahmad Sani.
Ya ce kowa shaida ne cewa Gwamna ya raba wa jama’a da kungiyoyi motoci da babura don su samu abin yi. “Kuma ku kanku da kuka shigo yanzu, ai kun gan su birjik a gidan Gwamnati. To duk na jama’a ne.”
Sannan ya bayyana cewa ta bangaren harkar ilimi kuwa, Gwamna Ahmad Sani, baya ga gyara makarantu da giggina sabbi, ya kyautata harkar koyarwa ta yadda yanzu ana samun kaso mai yawa na daliban jihar da ke cin jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare.
Ya kuma ce Gwamnatin Yarima ta bullo da shirin horar da matasa sana’o’i, wanda ake dibar matasa daga kowace Karamar Hukuma ana horar da su kan kananan sana’o’i kamar yin takalma, daukar hoto da na bidiyo, gyaran wuta, aikin kafinta da ma uwa-uba harkar sarrafa kwamfuta.
Sannan ya ce, “idan muka je ga harkar noma, to duk wani manomi da ka tambaya zai shaida maka irin kokarin da maigirma ya yi kan samar da takin zamani a jihar nan.” Ya ce a dalilin haka ne yake ganin a kakar bana Zamfarawa za su dara sosai saboda sun yi noma kuma damina ta yi albarka.
Sannan ya yi bayanin cewa gwamnatin jihar ta hada kai da kungiyar nan ta a-kori-yunwa da ake kira Sasakawa Global. Ya ce kuma a duk fadin tarayyar kasar nan ba inda aka rungumi wannan kungiya da hannu bibbiyu kamar jiharsu ta Zamfara, kuma suna ganin alfanunta.
Dakta Halliru Andi bai tsaya nan ba sai da ya yi bayanin irin namijin kokarin da Gwamnan jihar ta Zamfara ya yi wajen inganta harkar kula da lafiyar jama’a, inda aka samar da magunguna a asibitoci, aka kuma kyautata yanayin aikin ma’aikatan lafiya din kanta.
Bayan ya gama jawabin nasa ne ya dauki tawagar editocin suka zagaya don ganin kadan daga cikin ayyukan da Gwamna Ahmad Sani ya yi wa jama’ar jihar. Inda suka fara yada zango shi ne gidan talabijin da rediyo mallakar jihar. A nan ne suka ga cewa kusan dukkan ayyukan kafa gidan ya mallaka har sun fara watsa shirye-shiryen gwaji. A ta bakin Manajan gidan suna jiran dan kwangilar da aka ba aikin ya kawo wata na’ura ce kwara daya kafin gidan ya shiga watsa shirye-shiryensa ba kama hannun yaro.
Daga nan suka dunguma sai babbar kasuwar zamani ta garin Gusau da ake aikin ginawa. A nan editocin sun shaidi cewa aiki ya yi nisa, “da Zamfarawa Kanawa ne da tuni sun tare a kasuwar sun ci gaba da hada-hadar kasuwancinsu,” a ta bakin daya daga cikin editocin.
Bayan sun gama kewaya kasuwar ne suka nufi Makarantar koyar da sana’o’i, inda suka tarar ana koya wa matasa sarrafa kwamfuta, yin takalma, yin ayyukan kafinta, zane-zanen gine-gine, daukar hoto na bidiyo da sauran da sana’o’i.
Dakta Halliru Andi ya zagaya da editocin cikin garin na Gusau don su ga irin titunan da Gwamna Ahmad Sani ya yi, wadanda ya bayyana da cewa har ta gidajen ’yan adawa, ’yan PDP, titunan sun bibbi.
Kodayake kafin nan sun je madatsar ruwa da gwamnatin jihar ta gina, inda suka tarar aikin samar da ruwa a birnin Gusau ya kankama.
Abin da ya rage wa tawagar editocin ita ce ganawa da Gwaman Ahmad Sani Yariman Bakura. Har sun zauna a dakin zaman baki suna jiran a yi musu iso, sai ga Dakta Halliru ya fito ya ce su biyo shi.
Ai fa a tsattsaye editocin suka gaggaisa da Gwamnan, yana mai ba su hakurin cewa yanzu aka aiko ana neman sa a Abuja, “amma ku yi hakuri za mu shirya a yi hirar a Abuja ko Kaduna.” Gwamnan ya kuwa kama hanya sai Abuja.
| Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |