Almizan :Rikicin siyasa a Gombe da Bauchi ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 699                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Rikicin siyasa a Gombe da Bauchi

Rikicin siyasa ya dabaibaye jihohin Gombe da Bauchi, don kuwa abin ya kai ga ba hammata iska a tsakanin magoya bayan Gwamnonin da masu neman hayewa kujerar Gwamnonin a shekara ta 2007.


.

A jihar Bauchi dai wata taho-mu-gama aka samu tsakanin magoya bayan mai neman kujerar Gwamnan Bauchi, kuma tsohon Ministan sufurin jiragen sama, Alh. Isa Yuguda da magoya bayan Gwamnan Bauchin mai ci yanzu, Alh. Adamu Mu’azu a garin Azare.

Kamar yadda muka samu labari, dukkanin manyan ’yan siyasan biyu sun tafi Azaren ne don halartar daurin auren Alhaji Baba, Talban Katagum, kuma da ga Ambasada Balarabe Tafawa Balewa sa’ilin da aka samu rikicin.

Majiyoyinmu sun shaida mana cewa an yi fashe-fashen motoci, kuma ’yan sanda sun wawwatsa barkono mai sa hawaye, amma dai ba a samu asarar rai ba.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Bauchi, Alh. Ibrahim Zailani ya shaida wa manema labarai cewa wasu da suke zargin magoya bayan Yuguda ne suka tare Gwamnan suka auka masa tare da tawagarsa, abin da ya jawo ’yan sanda suka shafe mintuna kafin su tarwatsa su.

Shi kuma wani mai fafutukar sai Yuguda ya zama Gwamnan Bauchi a 2007, Yusuf Musa Gar, ya shaida wa manema labarai cewa far musu aka yi, har kuma an lalata masu ofishinsu.

A jihar Gombe ma a dalilin daurin aure ne aka kafsa tsakanin magoya bayan Kanar Musa Muhammad (ritaya) da na Gwamna Danjuma Goje a garin Nafada.

Kamar yadda Wakilinmu ya shaida mana, Kanar Musa ya isa fadar Sarkin Nafada, inda za a daura auren jikar Alhaji Yerima Abdullahi, ba jimawa Gwamna Goje ya iso da tawagarsa. A nan aka samu hatsaniya tsakanin magoya bayan sassan biyu.

Nan ma dai kamar Azare ba a samu asarar rayuka ba.

Bayan wannan hatsaniya ne Kanar Musa ya yi zargin cewa Gwamna Goje na son halaka shi, zargin da Kwamishinan watsa labarai na jihar, Alh. Umar Abubakar ya karyata.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International