Almizan :An tona asirin Isra’ila ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 699                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Duniya Labari

An tona asirin Isra’ila

Daga Hasan Muhammad

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kuduri aniyar bijirewa wani rahoto na BBC dangane da shirinta na nukiliya, wanda ya yi tsokaci a kan irin fuska biyun da kasashen duniya ke nunawa kan makaman na kasar Yahudu; jaridar Isra’ila mai suna HAARETZ DAILY ce ta ruwaito hakan.

Shirin, wanda aka tsara za a gabatar da shi a ranar Lahadi mai zuwa ya nuna cewa sojin na mamaya sun yi amfani da wani sinadari mai guba da ba a tantance shi ba a kan farar hula cikin watan Fabrairun shekarar 2001. Haka kuma wannan shiri na BBC ya bankado yadda Isra’ila ta daure wani matashin Bayahude mai suna Moedechai Vununu daurin shekara 18 a gidan kaso saboda samun sa da aka yi da laifin tona asirin kasar kan shirinta na makamashin nukiliya, sannan ga kuma shari’ar da aka yi wa Birgediya Yitzhak Yoav, wanda aka zarga da laifin bayyana wani littafi da ba a kai ga buga shi ba kan shirin na Isra’ila na makamashin nukiliya.

Ita dai Isra’ila ta dage a kan cewa ba ta da wannan makamashin, tana mai cewa wannan shirin nata na zaman lafiya ne. Amma bayanan da aka samu daga Vununu sun tabbatar da cewa tana da makamin nukiliya.

Masu shirin na BBC sun so su gana da wasu daga cikin jami’an da suka taba aiki a wajen wadanda suke korafin cewa sun gamu da cututtuka sakamakon mu’amala da wadannan makaman. A sakamakon haka ma wasu daga cikinsu ma har sun mutu. Amma dai su wadannan ma’aikata sun ki amincewa a yi hira da su saboda tsoron abin da zai biyo baya.

Jaridar ta HAARETZ ta ruwaito wani Kakakin BBC na cewa shirin ya saba wa abin da ya faru dangane da Vununu, yana mai yin watsi da batun cewa wai ana nuna son kai wajen mallakar makamashin na nukiliya, musamman ma dai Amurka da kawayenta.

Lokacin da aka yi hira da shi a cikin shirin, tsohon Firaministan Isra’ila, Shimon Peres, ya kauce wa tambayar da aka yi masa kan batun makamashin nukiliya, yana mai kauce wa yin kwatanci tsakanin shirin na Isra’ila da kuma na Iraki kafin Amurka ta mamaye ta.

Sai dai Kakakin na BBC ya ki amincewa da cewa an saka siyasa a cikin rahoton, yana mai cewa Ma’aikatar tsaron Birtaniya ma ta ki ta ce uffan dangane da wannan rahoto nasu. A bangare guda kuma ofishin jakadancin Isra’ila da ke London ya ce masu shirin ba su tuntubi Ma’aikatar harkokin wajen kasar ba, ko Kakakin ofishin.

Kakin na BBC ya ki amince cewa akwai siyasa cikin shirya shirin. Hatta Ma’aikatar tsaron Birtaniya ta ki ta ce uffan kan lamarin. A bangare guda kuma, ofishin harkokin wajen Isra’ila ya ce zai mayar da martani da zarar an gama shirin.

Shi dai wannan shirin ya zo ne bayan da aka gano wasu takardu a ofishin adana kayan tarihi na Birtaniya da suka yi nuni da cewa Birtaniya ta taba sayarwa da Isra’ila da wani makamashi mai suna ‘Deutrium,’ wanda yana daga cikin sinadaran hada bam na nukiliya a shekarar 1958. Sai dai a lokacin Ma’aikatar harkokin wajen Birtaniya ba ta nemi jin ko me Isra’ila za ta yi da shi ba.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, wani babban jami’in Birtaniya ya yi nazarin shirin Isra’ila na kera makamin nukiliya, inda ya gano cewa; haramtacciyar kasar Yahudun za ta iya mallakar wadannan makaman.

Haka kuma a wancan lokacin Shugaban Amurka John Kennedy, ya yi wa Isra’ila gargadi a kan cewa kada ta kera makamin na nukiliya, har ma ya tura masu bincike, amma sai Isra’ila ta katange wurin da makashin nata yake.

Ba tun yau ba Misra take zargin Isra’ila da laifin mallakar makamashin nukiliya, yayin da ita kuma take cewa atafau ba ta amince ba. Haramtacciyar kasar Yahudawan ta yi barazanar kai shirin nukiliya na Iran ga Majalisar Dinkin Duniya, yayin da ita kuma Iran ta ce nata shirin na zaman lafiya ne.

Sai dai abin da ya kamata a fahimta shi ne cewa ko Isra’ila ta amince, ko ba ta amince da wannan rahoton BBC ba, za ta ci gaba da shiru ne tana nuna ba ta da shi, alhali tana ma da shi din.

Wasu kiristoci ’yan kasar Pakistan sun musulunta

Sakamakon ganin mu’ujizar Imam Ridha (AS)

Wasu mabiya addinin kirista su biyu da suka zo daga Pakistan ziyarar hubbaren Imam Ridha (AS) a birnin Mashhad da ke Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun musulunta bayan wata mu’ujiza da suka gani ta bayyana masu daga Imam Ridha (AS).

Mista Robin James da ’yarsa Jasmine sun tafi ofishin kula da harkokin ’yan kasashen waje na hubbaren Imam Ridha (AS) da ke Mashhad a lardin Khurrasan, inda suka bayyana cewa shirye suke da su musulunta bayan sun bayyana babban dalilin da ya sa suka dauki wannan matakin.

Bayan sun musulunta ne sai uban ya zabi a sanya masa suna Ridha, wato ya dauki sunan Imam Ridha (AS), sannan kuma ita ’yar ta zabi suna Fatimah.

Su dai wadannan bayin Allah da suka yi gam-da-katar suka rungumi addinin Musulunci, abin da ya faru da su shi ne, ita Fatimah ta kasance ne tana fama da ciwon koda (kidney), kuma Likitan da ya duba ta a birnin Karaci ya tabbatar mata da cewa sai an yi aiki, kuma su ba su da kudin da za su iya biya a yi wannan aikin.

Saboda haka sai wani Malami a can Karaci da suke tare da shi ya ba su shawarar da su ziyarci Imam Ridha (AS) da budaddiyar zuciya da yardar Allah za su ga biyan bukata. Nan da nan kuwa suka yi niyya suka zo Iran, kuma cikin ikon Allah sai ga shi sun sami biyan bukata.

Jasmine, wadda ta koma Fatimah ta bayyanawa manema labarai cewa; bayan sun kwana bakwai suna zaune cikin hubbaren na Imam Ridha (AS), sai suka je don sake wani gwajin, inda aka tabbatar masu da cewa a wannan lokacin ba ta da sauran wata alama ta ciwon na koda.

Kare hakkin dan Adam a duniya:

Ahmadinajad ya yi wa Turai kule

Shugaban kasar Iran, Dakta Mahmood Ahmadinajad ya yi kule ga Tarayyar Turai da su zo a yi gasar baje kolin yadda kowanne yake kare hakkin dan Adam a tsakanin Malaman Musulunci da kuma fitattun masu tunani na nahiyar Turai.

A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai, Shugaban kasar ta Iran, Dakta Ahmadinajad ya tabbatar da cewa Iran a shirye take da ta shirya wani zama tsakanin su da Turai, inda za a tattauna batun kare hakkin dan Adam a mahangar Musulunci da kuma su tasu mahangar, sannan a bayyana wa duniya baki daya ta gani kuma ta zaba.

Dakta Ahmadinajad har ila yau, ya bayyana cewa; dole ne kuma a tabbatar da cewa an bayyana wa duniya hakikanin abin da aka tattauna ba tare da an yi ragi, ko kari ba.

Dakta Najad, ya kara da cewa; hakkin dan Adam wani abu ne mai tsarki, kuma mai kima, sannan bai kamata a yi amfani da shi wajen cimma wani buri na siyasa ba.

Kamar dai yadda aka sani ne tun bayan cin nasarar juyin Musulunci da aka yi a Iran daga shekara ta 1979 ne Yammacin duniya suke ta tuhumar kasar da take hakkin dan Adam, ba tare da wata hujja mai karfi ba.

Har yanzu dai babu wani mai da martani ko kuwa amsa wannan kira da Dakta Ahmadinajad ya yi wa Turai din da wani ko wasu masanansu ko gwamnatocinsu suka yi.

Kwamitin bincike kashe Hariri

Zai yi wa Bashar Asad tambayoyi?

Kwamitin nan da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, wanda aka dora wa nauyin gudanar da bincike kan kashe tsohon Firaministan kasar Lebanon, Rafik Hariri, ya nemi da a kira Shugaban kasar Syria, Bashar Asad domin ya amsa tambayoyi.

Kwamitin har ila yau, ya nemi da a kira Ministan harkokin wajen kasar Syria, shi ma don ya amsa wasu tambayoyi kan kisan gillar da aka yi wa Rafik Hariri, kamar yadda mai magana da yawun Kwamitin ya bayyana wa manema labarai a wannan makon.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai, tsohon Mataimakin Shugaban kasar Syria, Abdul-halim Khaddam, ya fito fili ya bayyana wa manema labarai cewa Shugaban kasar Syria, Bashar Asad ya yi wa tsohon Firaministan na kasar Lebanon barazana ’yan kwanaki kafin a kashe shi, abin da ake ganin ya ta da kaimin masu binciken kan yi masa tambayoyi.

Sai dai Ministan harkokin wajen kasar ta Syria, Farouk Al-Shara, ya musanta wannan magana ta Khaddam, inda ya nuna cewa ba ta da asali balle tushe.

Kasar Syria dai ta shiga kasar Lebanon ne tun shekara ta 1976, amma daga baya a shekara ta 2005 ta kwashe dukkanin sojojinta da ke kasar bayan matsin lambar da ta fuskanta daga Amurka da kuma wasu kasashen Larabawa.

Masana na ganin cewa amfani da kashe Hariri kawai ake yi da niyyar ganin an raunana karfin Syria, wadda take taimaka wa Kungiyar Jihadi ta Hizbullah a Lebanon da kuma gaba dayan yankin Gabas ta Tsakiya.

An yi tir da satar jin wayoyin mutane da Amurka ke yi

Har yanzu fadar Shugaban Amurka ta ‘White House’ ba ta ce uffan ba game da wani rahoton da aka buga cewar Hukumar Tsaro ta kasa ta saci ganin wasikun da aka aika ta sakar sama, wato i-mel, tare da satar jin wayoyin tarho na jama’a a asirce duk ba tare da izinin kotu ba, fiye da yadda ita gwamnatin ta fito ta amince cewa ta yi.

Jaridar NEW YORK TIMES ta ambaci jami’an gwamnatin Amurka na yanzu da kuma tsofaffi suna fadin cewa Hukumar tsaron ta FBI ta sa idanu da kunne a kan sakonni na cikin gida da na waje, tare da taimakon kamfanonin sadarwa.

Sai dai ba a bayyana sunayen kamfanonin da suka taimaka din ba, amma kuma an ce tun bayan hare-haren 11 ga watan Satumbar 2001, sun yi ta tattara bayanai game da irin kiraye-kirayen waya na mutane.

Jami’an Hukumar tsaron sukan duba bayanan mutanen da aka kira da irin abubuwan da aka fadi bisa fatan zakulo ’yan ta’adda.

Gwamnatin Bush tana fuskantar karin suka a saboda yadda take gudanar da ayyukan leken asiri ba tare da izinin kotu ba a cikin Amurka a kan abin da ta ce wayoyin tarho ne ko sakonnin i-mel daga Amurka zuwa kasashen waje ko daga waje zuwa cikin Amurka.

Wannan aikin leken asiri dai da ake yi a cikin gida ya jawo ta da kayar baya daga ’yan Majalisar dokokin Tarayyar Amurka.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International