Almizan :Takaitaccen bayani kan aikin Hajji ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rubutun musamman

Takaitaccen bayani kan aikin Hajji

Daga Harkarmusulunci.8m.net

Shi dai aikin Hajji ya kasu kashi uku ne: Hajjin Tamattu’i. Hajjin Kirani. Hajjin Ifradi.

Hajjin tamattu'i shi ne wajibin wanda yake zaune a nesa da garin Makkah, nisan da ya kai mil 48, yayin da Hajjin Kirani da Ifradi sune wajibin wanda yake zaune a garin Makkah da kewayenta, wato nesansu da garin Makkah bai kai mil 48 ba. To amma a aikin Hajjin bakance, ko na mustahabbi, ya halatta ga mazaunin Makkah da wanda ke nesa da Makka ya zabi duk aikin Hajjin da ya ga dama tsakanin raben-raben da aka ambata a sama.

To bisa la’akari da cewa aikin Hajjin Tamattu’i shi ne wajibin mafiya yawa mutane, musamman mutanenmu, don haka za mu yi bayani ne kan wannan nau’i na aikin hajjin. Ga yadda ake yin aikin Hajjin Tamattu'in:

Da farko akan fara ne da Umrar Tamattu'i, sannan a kare da Hajjin Tamattu’i, wato Umrar ita ce juzu’in farko na Hajjin Tamattu’in. Umrar Tamattu’in na da wajibai guda biyar ne:

Ihrami. Dawafi. Sallar Dawafi. Sa’ayi (tafiya tsakanin Safa da Marwa). Aski, ko kuma saisaye.

Yadda ake yin Umurar Tamattu’in kuwa shi ne:

Da farko mutumin da ya yi niyyar yin aikin Hajjin Tamattu’i zai fara ne da daura harami a daya daga cikin wararen da ake daura haramin guda biyar, ko kuma abin da ake ce wa ‘mikati,’ wato (1) Zul Hulaifa (2) Akik (3) Juhfa (4) Yalamlam (5) Karnil Manazil. 1. Harami: Shi ne sanya kyallen tufafin nan guda biyu da Alhaji zai sa yayin aikin Hajjin.

Yadda ake daura harami shi ne: Mutum zai yi niyyar yin harami da Umurar Tamattu’i na Hajjin wajibi, sannan ya sanya tufafin haraminsa guda biyu, zai daura guda, ya kuma yafa guda, wato ya yi mayafi da shi. Daga nan sai ya fara ‘talbiyya’ wato fadin: Labbaikallahumma labbaik, labbaika la sharika laka labbaik, innal hamda, wan ni’amata laka wal mulk, la sharika laka.

To idan mutum ya yi haka ya zamanto muhrimi (wanda ya daura harami) kenan da aikata wasu abubuwa suka haramta masa kamar su kusantar mace, shafa turare, sanya kewayayyen tufafi ga namiji, farauta da makamantansu.

Akwai kuma wasu ayyuka na mustahabi da ake so mutum ya aikata, misalin yin wanka kafin daura harami da makamantan hakan.

2. Dawafi: Abu na biyu cikin aikin Umrar Tamattu’i shi ne Dawafi, wato kewaya Dakin Ka’aba. Yadda kuma ake yin sa shi ne: Mutum zai fara da yin niyyar Dawafin Umurar Tamattu’i ne, sai ya fara zagaya Dakin Ka’aba har sau bakwai, zai fara ne daga inda Hajrul Aswad yake, wato Dakin Ka’aba na hannunsa na hagun. Idan ya fara daga wajen Hajrul Aswad ya zagayo ya zo wajen da ya fara, to ya yi guda kenan, haka-haka har sau bakwai.

3. Sallar Dawafi: Idan mutum ya gama dawafi wato ya kewaye Dakin sau bakwai, sai ya yi sallar Dawafin raka’a biyu a Makama Ibrahim. Wannan shi ne wajibin Umura ta Tamattu’i.

4. Sa’ayi: Wajibi na hudu shi ne Sa'ayi, wato tafiya tsakanin Safa da Marwa, yadda ake yin ta kuwa shi ne: Mutum ya yi niyyar yin Sa'ayi na Umrar Tamattu’i na Hajjin wajibi, sai ya fara tafiya daga Safa ya zo Marwa, daya kenan, sannan daga Marwa ya zo Safa, biyu kenan har sau bakwai. Wato tafiya daga Safa zuwa Marwa sau hudu, daga Marwa kuma zuwa Safa sau uku, wanda karshen tafiyar za ta kare ne a Marwa.

5. Aski: Wajibi na biyar kuma na karshe a Umurar Tamattu’i shi ne: Aski, ko kuma saisaye, mutum ya aske wani abu daga cikin gashin kansa ko gemunsa, ko gashin bakinsa, ko kuma ya yanke farcensa.

Da hakan ne ake kare aikin Umurar Hajjin Tamattu’i, wanda hakan na nufin kenan dukkan abubuwan da aka haramta masa saboda harami a halin yanzu ya halatta a gare shi, misali kusantar mace, sanya turare da sauransu. Daga nan sai mutum ya jira lokacin daura haramin Hajjin Tamattu’i.

HAJJIN TAMATTU'I:

Hajjin Tamattu’i ya kunshi wajibai guda 13 ne, sune:

(1) Ihrami (2) Tsayuwar Arafa (3) Tsayuwar Muzdalifa (4) Jifan Shaidan (5) Hadaya, wato yanka, ko kuma suka (6) Rage gashi ko askewa (7) Dawafi (8) Sallar Dawafi (9) Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa (10) Dawafin bankwana, wato Dawafin Nisa (11) Sallar Dawafin bankwana (12) Kwana a Muna (13) Jifan Shaidan a wurare uku, wato Ulah, Wusta da Akbah. Wadannan sune ayyukan aikin Hajjin Tamattu’i.

YADDA AKE YIN AIKIN HAJJIN TAMATTU’I A AIKACE:

Da farko mutum zai daura harami ne da niyyar yin aikin Hajjin Tamattu’i daga Makkah a lokacin da ya san zai riski tsayuwar Arfa, kafin gotawar rana (zawal) a ranar tara ga watan Zulhajj, amma abin da ya fi shi ne daura haramin tun bayan sallar Azahar din ranar ‘Tarwiyya’ wato takwas ga watan Zulhajji, sannan ya tafi hawan Arfa, wato tsayuwar Arfa tun daga gotawar ranar har zuwa faduwarta, sannan ya bar wajen tsayuwar Arfa ya tafi Muzdalifa ya kwana a Mash’arul Haram, idan ya wayi gari wato rana ta 10 kenan ga watan Zulhajjin, sai ya tsaya a wurin har zuwa fitowar rana, idan rana ta fito sai ya tafi Muna domin yin ayyukan ranar salla, wanda abubuwa ne guda uku kamar haka: Jifan Shaidan, sannan sai hadaya wato suka ko yankan dabba, sannan rage gashi ko aski, amma mace ragewa za ta yi kawai banda yin aski. Idan farkon aikin Hajjin mutum ne, to ya yi aski, idan kuma ba na farko bane yana da zabi ko dai ya yi aski ko saisaye.

Yadda ake yin jifan kuwa shi ne, jefa tsakuwa dai-dai har sau bakwai.

Hadaya kuwa ita ce yanka dabba ko sokewa wanda yake wajibi ne a kan Alhajin da yake yin aikin Hajjin Tamattu’i, bayan ya yi jifa.

Idan mutum ya aikata wadannan abubuwa, to abubuwan da suka haramta masa yanzu sun halatta masa, in banda sanya turare, kusantar mace da farauta.

Daga nan idan ya ga dama a wannan ranar sai ya tafi Makkah, idan ya tafi sai ya yi Dawafin Hajjin Tamattu’i sau bakwai (kamar yadda ya gabata a Umurar Tamattu’i. Sannan ya yi sallar Dawafin raka'a biyu a Makama Ibrahim. Sai kuma ya yi sa’ayi tsakanin Safa da Marwa sau bakwai, da zai fara daga Safa ya kare da Marwa.

Sai ya yi Dawafin Nisa, wato zagaya dakin Ka’aba shi ma sau bakwai kamar Dawafin farko yake, wanda wasu suke kiransa da Dawafin bankwana.

Bayan kammala Dawafin, sai mutum ya yi sallarsa (sallar Dawafin) raka’a biyu shi ma a Makama Ibrahim. Da zarar mutum ya yi Dawafin Hajji da sallarsa, da kuma sa’ayi tsakanin Safa da Marwa, to sanya tufafi ya halatta a gare shi, kuma da zarar ya yi Dawafin Nisa, to matar mutum ta halatta a gare shi, idan kuma mace ce, to mijinta ya halatta a gare ta, don haka ne ake kiran Dawafin da sunan Dawafin Nisa.

Daga nan sai mutum ya dawo Muna ya kwana a nan, washegari wato ranar 11 ga watan Zulhajji ya je yin jifan Shaidan a wurare ukun da muka ambata a baya, kuma kamar yadda ya yi ranar Idin. Sannan ya sake kwana a Muna a rana ta 12, a nan ma zai je ya yi jifan a wurare ukun. Idan ya aikata hakan, to ya gama aikin Hajjin Tamattu’i.

Amma kamar yadda muka bayyana a baya, bayan ya kammala ayyukan ranar Idi yana da zabi, ko dai ya tafi Makkah domin gudanar da sauran ayyukan hajjinsa kamar yadda muka bayyana, ko kuma bayan ayyukan ranar sallar Idin ya ci gaba da zama a Muna har zuwa bayan zawalin rana ta 12, sannan ya tafi Makka domin gudanar da sauran ayyukan hajjinsa, amma a ranakun 11 da 21 da yake Muna, zai je ya yi jifan Shaidan a wurare ukun nan da muka bayyana.

Idan kuma ya ga dama zai zauna a Munan har zuwa rana ta 13 ga watan Zulhajjin, bayan ya yi jifan Shaidan a wurare ukun, sai ya tafi Makkah ko da kafin zawalin ne, domin gudanar da sauran ayyukan Hajjin Tamattu’insa kamar yadda bayani ya gabata.

Wannan dai shi ne takaitaccen bayani kan Hajjin Tamattu’i da yake shi ne wajibin wanda yake nesa da Makkah, wato wanda inda yake zaune yana nisan mil 48 daga Makkah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International