
Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426
Bugu na 699
| Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Ra'ayin Almizan
|
|
|
Tun bayan harin da wasu zauna-gari-banza suka kai kan ’yan uwa musulmi a lokacin muzaharar Ashurar da ta gabata a watan Almuharram a Sakkwato, birnin Shehu ya dauki sunan garin da ake tashe-tashen hankula na addini a kafafen watsa labaru na cikin gida da kasashen duniya. Ba kuma wani abu ya jawo haka ba sai yadda gwamnatin da alhakin tsaron jihar ya rataya a wuyanta ta sa ido ana ta bugu, kisa, kamu da kona gidaje da dukiyoyin ’yan uwa musulmi ba ji ba gani.
Ganin irin kaurin sunan da garin ya soma yi a idon duniya, gwamnatin jihar ta kama masu ingizo zauna-gari-banza, wanda a sanadiyyar haka kurar ta dan lafa. Sakkwato ta dan bace daga kanun labaran kafafen watsa labarai na cikin gida da duniya baki daya. A nan mutum na iya zaton cewa da gaske gwamnatin Bafarawa take yi na samar da wanzajjen zaman lafiya a Sakkwato da kewaye. To, amma ganin yadda jifa-jifa akan kame ’yan uwa musulmi a tsare, musamman wasu ’yan uwa musulmi su 18 da ke tsare tun watan Ramadanan da ya gabata, ya sa shakku kan wannan kuduri na samar da zaman lafiya a birnin Shehu.
Su dai wadannan’yan uwa ba su ci ba su sha ba, aka auka musu a Markazin ’yan uwa musulmi a nan Sakkwato din aka kame su, sai gidan kurkuku, can suka yi karamar salla, kuma ga dukkan alamu can za su yi babbar salla, yau watanni uku cur! Akwai zaluncin da ya wuce a tsare bayin Allah ba cas ba as har na tsawon wadannan watanni ba tare da an hukunta su ba kan laifin da ake zargin sun aikata, kodayake ba wani laifi da suka aikata tunda ba su zagi ko doki dan kowa ba?
Wai shin menene laifin wadannan bayin Allah wadanda cikinsu akwai masu iyalai da dama? A takardar tuhumar su an ce ana tuhumar su da niyyar shiga muzaharar Kudus. ALMIZAN na da tambaya ga Hukumomin da abin ya shafa. Tana ina kulla niyyar abu ba tare da kama hanyar aikata abin ba ya zama laifi a ma dokokin da ba na Allah ba, balle kuma na Allah? Haba jama’a! In dai ba gwamnatin jihar Sakkwato tana son sunan da birnin Shehu ya yi na birnin bin ka’idojin addinin Musulunci ya baci ba, menene na yin irin wannan zargi mara tushe balle makama?
Sanin kowa ne a kasar nan da ma duniya baki daya cewa a biranen musulmi da dama na kasar nan da sauran kasashen duniya an yi muzaharar Kudus an tashi lafiya, ciki kuwa har da Sakkwato, sai dai inda Yahudawa da ’yan barandansu suka yi kaka-gida. To, don menene za a tsare wasu da sunan suna da niyyar shiga wannan muzaharar wacce kowa shaida ne cewa ta zaman lafiya ce?
Sannan kuma ina batun ’yancin yin addini da tsarin mulkin da jami’an gwamnati da na tsaro a jihar Sakkwato suka sabi layar karewa aka yi da shi? Ko ko abin zabe ne, wasu na da ’yancin bauta wa kyankyaso in sun so, wasu kuma ba su da ’yancin yin tofin Allah tsine ga Yahudawan Sahayoniya masu kashe al’ummar musulmi a kullum a Palasdinu?
Kiran da ALMIZAN take da shi a safiyar Juma’atu babbar rana ta yau shi ne a gaggauta sakin wadannan bayin Allah ba tare da bata lokaci ba. Ci gaba da tsare su danne musu hakkinsu ne a matsayinsu na ’yan Adam musulmi kuma ’yan kasa.
Muna kira ga ’yan uwa musulmi a ko’ina suke a doron kasa da su yi amfani da wadannan kwanaki goman farko na Zulhaj din nan masu alfarma su roki Allah ya saka wa wadannan ’yan uwanmu da ke tsare a Sakkwato haka siddan. Duk wanda ke da hannu a wannan zalunci da ake musu Allah ya kassara shi, ya mai da masa da aniyarsa. Su kuma Allah ya sa su cinye wannan jarabawa da suke ciki.
| | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |