Jarida don Karuwar Musulmi
Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki ISSN 1595-4471
Juma'a 25 Ramadan, 1426
Bugu na 690
Tunatarwa | | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari Tattaunawa | Labarai |
Ka kara sanin Iran (4)Ci gaba daga makon jiya
A yankin Susa (wato Sush) an samu wata wayewar kuma da ta yi tashin gwauron zabo kafin shekara ta 3,000 kafin haihuwar Annabi Isa (AS); wannan wayewar dai ta samu asasin kafuwarta ne daga Elamiyawa. A arewacin Susa da ma yankin Elamiyawa kuma, an yi wata jama'ar da ta zauna a jigawar da ke gangaren yankin tsaunukan tsakiyar Iran. Wadannan mutane kuwa sune; Kasiyawa, Lulbiyawa da kuma Gutiyawa. Za ma a iya ganin fadar Basaraken Gutiyawa, wato Annubaini a gindin tsaunin Sare-pol a daura da babbar hanyar da ta doshi kan tsaunuka a matsayin misali. A wajajen shekara ta 1250 kafin haihuwar Annabi Isa (AS) ne Elamayawa suka kafu daram a garin Sousa, wanda hakan ya sa aka samu zaunanniyar al'ada dorarriya kuma wadda ta ci gaba ce. Alal misali hamshakin mashahurin ginin nan na Ziggurat din Choga Zanbil an gina shi a cikin wannan zamani a yankin jigawar Khuzestan, kuma wannan gini wanda da asalinsa hawa biyar ne, an gina shi ne domin gudanar da sha'anin addini, a yanzu hawa biyu ne rak suka saura. An kuma gina shi ne da bulo din gasasshen yumbu, kana kuma fadin murabba'in kafa 346 da kuma kafa 174, tsawonsa. Wani Farfesan ilimin kufai ne, wato Roman Ghirshman ya hako ginin daga karkashin kasa, cikin shekarar 1950 zuwa 1960. Wuraren tarihi da kuma abubuwan da ke nunar da wayewar kan Iran tun zamanin dauri dai, wasu abubuwa ne na ban sha'awar gaske da ke matukar daukar hankulan masu yawon bude ido da shakatawa. Muhimmi, kana kuma fitaccen matsayin da Iran din ke da shi a taswirar duniya na kasancewarta wata mahada tsakanin bangarorin gabashi da kuma na yammaci ya sa 'yan kasuwa da masu yawon bude ido daga ko'ina sun samu dimbin faragogi a fagagen tattalin arziki da kuma musayar al'adu. Kyakkyawar misali kuwa a nan ita ce babbar hanyar kasuwancin siliki tsakanin yammacin duniya da gabashinta ta ratsa ne ta cikin yankunan Iran din, tun ma farkon kafuwar wannan harka a tsakiyar karni na 2 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Saboda ci gaba da mu'amala tsakanin 'yan kasuwa, masu yawon bude ido, masu yawon bincike da kuma jama'ar yankunan, an samu giggina hasumiyoyin tarihi a yankunan da ke gindin tsaunuka da kuma na hamada. Kyawawan misalai kuma a nan sun hada da masaukan fatake, gadoji, kasuwanni da kuma masallatai. Jinsin mutanen Aryan dai, wadanda kuma a ilimin sanin jinsunan mutane da kuma yarukan duniya ake kira da Indo-European a Turance, sune jama'ar farko da suka fara zama a yankin arewa maso gabashin kasar Farisa, daga nan kuma sai yankin Siberiya, ma'ana yankunan kudancin kasar Rasha kenan. Shi kuma wannan suna na Iran, ya samo asali ne daga kalmar Aryana, wacce ma'anarta a gun masu yaren, ke nufin mazaunin 'yan kabilar Aryan. Shi kuma Fars, (wanda yanzu lardi daga cikin lardunan kasar Iran din yau) nan ne inda babbar fadar daular 'yan jinsin Aryan. A farkon karni na 20 kafin haihuwar Annabi Isa (AS), an samu wata tawaga ta jinsin mutanen Indo-European wato Aryaniyawa kenan, da suke yankin tsaunukan da ke arewacin Iran a daura da gabar kogunan Saihun da kuma Jihun A wani dadadden zamani, Mediyawa ne suka zauni yankin yammacin Iran da farko, sannan kuma tare da Farisawan da ke yankin kudanci, suka hada kai suka mamayi tsohuwar daular Assyria. Sarkin Mediyawa Phraotes ne farkon wanda ya sa Iran ta zama wata fitacciyar kasa a taswirar duniyar wancan zamani, bayan ya cinye daular Assyria da yaki. Garin Echbatana ne babbar fadar Meidiyawa; sannan kuma nan ne mazaunin garin Hamedan din yau yake da zama. Bayan Mediyawan sun cinye daular Assyria da yaki, ba da wata jimawa ba kuma sai daularsu ta yi karfi, inda ta ayyana 'yancin cin gashin kanta, kai, daga bisani ma ta tunkude daular Assyria gaba daya. Bayan Sarkin Mediyawa Phraotes, wanda ya yi mulki daga shekara ta 525 zuwa 585 kafin haihuwar Annabi Isa (AS) ya bar duniya ne kuma, sai dansa Siyakzares ya gaji karagar mulkinsa. Shi ne kuma wanda ya gama da dan abin da ya saura na daular Assyria kwata-kwata, har ma ya yi nasarar kame babban birnin daular, wato Nineveh a wajajen shekarar 612 kafin haihuwar Annabi Isa (AS), sannan kuma ya fadada daularsa har zuwa yankunan Asiya karama. Sai dai kuma kash, karfin daular Mediyawan bai yi tsawon zamani ba. Domin an samu wata kabila kuma daga jinsin Aryan din, wato Farisawa, da ita ma ta zama wata ta-gakin-gakuma. Zuriyar Arkemeniyawa ne dai ke sarauta a wannan daular. Wannan suna, "Arkemeniyawa" ya samo asali ne daga sunan daya daga ciki Sarakunan da suka taba mulkar daular. Wato Sarki Harkemanesh, ko kuma Arkemanesh, a wata lahajar. Wannan Sarkin ne kuma ya karfafa rundunonin yakin da daular ke da su har zuwa cikin tsakiyar karni na 6, kafin haihuwar Annabi Isa (AS). A shekara ta 553 kafin haihuwar Annabi Isa (AS) ne kuma, Sarki Sirus, wanda kafin hawansa karagar sarautar tsohuwar daular Farisa, Hakimi ne a gundumar Parsa, ko kuma Parsis (yanzu dai wannan gunduma daya ce daga cikin lardunan kasar Iran a yau), wanda kuma shi ne aka fi sani da Sirus hamshakin Sarki (Cyrus the great) a dukkanin tarihi; shi ne wanda ya fara yin tutsu da kuma tawaye ga mulkin mulukiyar Mediyawa a zamanin mulkin Sarkin Mediyawan Astiyages. Sakamakon haka ne kuma aka samu wata kyakkyawar jituwa tsakanin jama'ar Farisawa da ta Mediyawa, har ma aka hada wata kakkarfar rundunar yaki da ta rika kai wa jerin hare-haren da suka yi nasarar kafa makekiyar daular Farisa din nan da ta yi suna a duniya. Saboda haka Sarki Sirus ya yi suna a tarihi ba a matsayin mayaki ko wanda ya gina daula ba kawai, a'a, har a matsayin wani haziki mai hikima sannan kuma wayayye, kana masani kan sha'anin mulki. Sarki Sirus dai, a lokacin rasuwarsa cikin 529 kafin haihuwar Annabi Isa (AS), ya kasance shi ne mai iko da ba wai Farisa ba kawai, har ma da Babila, Lidiya, Siraiya da kuma Palasdinu. Shi kuma Sarki Dariyus, baya ga kasancewarsa na hamshakin Basarake, to ya kuma kasance hamshakin magini. Shi ne ma ya gina wasu mashahuran dandamaloli, jerin rukunin gidaje da kuma dakwalen fadoji a birnin Persepolis. Wadanda kuma har yanzu suna nan kuma suna bayar da sha'awa da kuma daukan hankulan masu yawon bude ido daga ko'ina a duniya. Wannan guri da aka gina jerin rukunin gidaje a Persepolis shi ne daya rak da ya fi kowanne irin sa kyau a duniya. Idan aka hango gurin daga kan tsauni, to za a ga wani makeken shimfidadden fili ne da ke da kasa mai dausayi, sannan kuma ga jerin rukunin gidaje a sigar murabba'i, sannan ga wata katanga mai ginshikai na duwatsun da aka sassaka na kewaye da su. Sarki Dariyus ne dai ya fara ginawa, Sarki Zarzeks da kuma Sarki Artazekszeks na 1 kuma suka kammala ginin. Gwamnatin da Arkemeniyawa suka kafa dai ta kasance ne mai sassaucin ra'ayi kana kuma marar duhun kai a iya tsawon zamanin da ta yi na sama da shekaru 2,500. Hakuri da kuma juriya ta fuskacin addinin da suka nuna ga Babilawa, Assyriyawa, Misrawa, da ma Yahudawa, na barin su su yi addinansu a sigar da suke, duk kuwa da cewa an ci su da yaki, sannan kuma ga shi gwamnatin ta masu bin addini Zorostiriyananci ne, ba shakka wani abu ne na gani, kuma na fada. Tsarin tafiyar da gwamnatinsu na inganci kwarai da gaske, hakan ne ma ya sa daular ta ci gaba wanzuwa kuma ta zama wata samfuri a zamunnan da suka biyo baya lokacin. Siga, salo da kuma tsarin zane-zanen fasahar Arkemeniyawa sun bayyana a irin sassake-sassaken da suke yi a jikin duwatsu na hotunan dabbobi da kuma dan Adam Bafarise ya yi shigar sutura irin ta gargajiya; kuma sukan yi irin wadannan zane-zanen a jikin bangwaye, ko kuma tasoshin zinare da azurfa. Abin na da gagarumar daraja mai burgewa. Idan kuma aka ga zanen hoton dabbobi ne a wata irin siga da a wasu lokuta dabbobin ke samun kansu a ciki, to, irin wannan kuma yana nuna wata manufa ce, ko kuma wani tunani, ko ra'ayin mazaunin game da wani wani abu. Kayayyakin adon mata na zamanin, wadanda aka yi da lu'u-lu'u kuma, kamar su awarwaro, munduwar kafa, abin wuya, dan kunne, da dangoginsu, da damansu sun iso har zuwa wannan zamanin namu. In aka ziyarci gidan adana kayan tarihi na Okzus, inda aka ajiye dukkanin wadansu abubuwa dangogin zinare, azurfa da sauran duwatsu masu daraja dangin lu'u-lu'u, murjani da makamantansu, na nan a launuka dabam-daban. Za mu ci gaba insha Allah. |
Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani | Hadisai | Crescent International |