MAKERO (Dermatophytoses /Ring Worm)
Daga Abdulkarim Usamah Katsina
Makero cutar fata ce mai yaduwa wadda kwayoyin cuta dangin ‘Fungal’ suke haddasawa bisa fatar jiki ko akaifa da sauransu. Wata kwayar cuta ce mai suna ‘dermatophytes tinea’ ke nasarar makalewa fatar jiki ta haddasa wannan cuta, wato makero; kodayake kwayoyin cutar sun kasu kashi-kashi, kuma suna haddasa makero iri-iri. Makero ta fi cutar da yara kanana saboda rashin kulawa. Sannan tana kama kai, fatar jiki, akaifa, tafukan kafa da hannu da sauransu.
Bari mu dan yi bayanin yadda ake kulawa da makero gwargwadon rabe-rabensa ta inda ya kama a jiki.
MAKERON KA:
Makeron bisa kai yana da alamomi ga yara kanana a bisa kai wanda sune suka fi kamuwa da wannan ciwo mai yaduwa. Kamar ganin wasu zagayayyun kuraje kanana masu kaikayi sun yi da’ira ko da’irori bisa kai. Yayewar gashi ba tare da an yi aski ba, wato gashin ya zube.
Sannan gashin kai zai rika datsewa yana faduwa kasa. Haka kuma makero yana iya sanya kaluluwa a wuraren da take fitowa a cikin jiki da dukkan alamominta kamar masassara da sauransu.
KULAWA DA MAKERON KA:
Da farko dai a fara aske gashin kan, a rika wanke kan da sinadarin kashe kwayoyin cuta, kamar sinadarin ‘chlorohexidine, cetrimide, dettol, septol, purit,’ wadanda aka hada da ruwa gwargwadon yadda ka’idar hada su take a tsarin asibiti.
Akwai man shafawa na kuraje kamar ‘whitfield’s ointment, sulphur lotion’ da sauransu wadanda ake son yin amfani da su sau biyu akalla a yini na tsawon sati biyu zuwa wata guda.
Akwai kuma magungunan kisan kwayoyin cutar da za a iya samu a asibiti da sauran cututtuka da wannan makero zai iya haddasa wa jiki baki daya.
MAKERON FATA:
Irin wannan yana nacewa ne bisa fatar jiki ya rika karuwa ko yaduwa bisa fatar jiki a hankali. Yana da kaikayi da da’irorin kuraje kanana, wani lokaci za su fashe, ruwa ya rika fita.
Za a iya ganin tsakiyar makeron babu kome, kuma babu wata alamar cuta a tsakiyar inda ya gewaye.
KULAWA DA MAKERON FATA:
Kamar bayanin makeron bisa kai, na inganta tsafta da wanke wurin da wadannan sinadarai masu kisan kwayoyin cutar irin su sinadaran ‘dettol’ da sauransu duk ana bukatarsu a nan. Wato a kula da wanke wurin sosai kuma a kai a kai, ana shafa ire-iren wadannan mai masu kashe kwayoyin cutar, kamar ‘whitfields’ da sauransu.
Haka kuma idan wadannan makeron suka yawaita, to lalle suna bukatar magani ko allurai wadanda likita ne kawai zai tsara su cikin yardar Allah.
Bayan makeron bisa fata a kai tsaye, akwai wanda ke fitowa bisa tafukan hannu ko kafa ko cikin hammatar hannu da sauransu. Kusan duk matakan kulawa da wadannan makeron daya ne. Sai dai ana son yin amfani da shan-shabale (GV paint) ga makeron bisa tafukan hannu ko kafafu kafin a fara amfani da man kashe kuraje, kamar ‘whitfields’ ko ‘smulphur ointment’ da sauransu.
MU KEWAYA DUNIYA
Ka kara sanin Iran (5): Tarihin daulolin Farisa na dauri
Ci gaba daga Almizan ta 690.
Siga, salo da kuma tsarin zane-zanen fasahar Arkemeniyawa sun bayyana a irin sassake-sassaken da suke yi a jikin duwatsu na hotunan dabbobi da kuma dan Adam Bafarise ya yi shigar sutura irin ta gargajiya; kuma sukan yi irin wadannan zane-zanen a jikin bangwaye, ko kuma tasoshin zinare da azurfa. Abin na da gagarumar daraja mai burgewa. Idan kuma aka ga zanen hoton dabbobi ne a wata irin siga da a wasu lokuta dabbobin ke samun kansu a ciki, to, irin wannan kuma yana nuna wata manufa ce, ko kuma wani tunani, ko ra’ayin mazaunin game da wani wani abu. Kayayyakin adon mata na zamanin, wadanda aka yi da lu’u-lu’u kuma, kamar su awarwaro, munduwar kafa, abin wuya, dan kunne, da dangoginsu, da damansu sun iso har zuwa wannan zamanin namu. In aka ziyarci gidan adana kayan tarihi na Okzus, inda aka ajiye dukkanin wadansu abubuwa dangogin zinare, azurfa da sauran duwatsu masu daraja dangin lu’u-lu’u, murjani da makamantansu, na nan a launuka dabam-daban.
Wannan daula ta Sirus ta shafe tsawon zamani daga shekaru 350 kafin haihuwar Annabi Isa (BC) zuwa shekaru 332 bayan haihuwar Annabi Isa (AD), a lokacin da Sarki Alexander The Great ya kifar da ita. Bayan rugujewar daular da kuma mutuwar Alexander a shekara ta 332AD, sai Girkawa ko Hellemiyawa suka yi tasiri a kan Iran da ma Gabas ta tsakiya na karnoni da dama bayan Alexander. A wannan zamani Selesudawa, wadanda suka gaji Alexander sai kuma Parthinawa (da kuma aka sani da Arsidiyawa) suka mulki Iran.
A daidai kimanin shekara ta 211 AD, Ardeshir ya shirya wani bore a lardin Fars, kuma aka shekara ta 224 AD rundunarsa ta kashe Sarkin Parthinawa na karshe a wani yaki da aka gwabza. A sa’ilin ne Ardeshir ya mulki dukkanin Iran banda lardunan Armeniya da Baktariya.
Sassinawa, sunan sabuwar daular da ta kafu, tana jingina asalinta ne ga Arkeminiyawa ta hannun jerin sarakunan Fratedra wadanda suka kasance suna cin gashin kansu har zuwa faduwar lardin Fars a karkashin mulkin Parthiniyawa. Wasu kudaden kashewa da aka tsinta a Iskhr kusa da Perposlis sun nuna haka. Shi kansa Ardeshir jikan wani shugaban bauta ne na Sassan a dakin bauta na Anahita da ke Iskhr.
Shapur I, a shekarar 241-271 AD, dan Sarki na biyu daga cikin shahararrun Sarakuna uku na wannan daula, ya kama Sarkin Ruma Valerian a wani yaki kuma ya tsare shi har sai da ya mutu. A lokacin da take tsakiyar cin ganiyarta, daular Sassaniyawa a zamanin Khosrow Anushirvan da Khosrow Parviz ta dangana tun daga gabar bakin teku har zuwa Indiya.
Zamanin mulkin Sassaniyawa ya shaidi sake dawowar karfin ’yan kasancin Iraniyawa. Ta yalwatu a kashin kanta, kuma ta ki karbar tasirin haduwa da sauran daulolin waje. Wannan zaman lafiya da kwanciyar hankali da aka samu a cikin gidan wannan daula ya samu ne kusan saboda irin kyakkyawan tsarin tafi da mulki da aka mai da shi gu guda na Ministocin da jami’an gwamnatin lokacin. Rundunar sojin daular biyan su ake yi, kuma ana lura da su ne daga baitulmalin sarakuna.
Irin yanayin gine-gine da sassake-sassaken zamanin Sassaniya za a iya ganin sa kamar a yadda fadoji, dakunan bautar wuata, dam-dam, gadoji, manyan gine-gine, tsarin birni da wuraren tuna tarihi na musamman kamar sassake-sassaken duwatsu suke. Haka kuma ragowar manyan fadoji da zane-zanen duwatsu za a same su a Firuzabad, Bishpur, Nagsh-e-Rajab, Nagsh-e-Rusta da Sarvestan a Fars da kuma Tesiphon a kwarin Tigris da kuma Qasre Shireen a kan iyaka tsakanin Iran da Irak.
Daular Sassaniyawa ta yi karkon fiye da shekaru arbaminya tun daga 226 AD zuwa kusan 641 AD, a lokacin da Sarkin Sassaniyawa Yazdegerd na III ya sha kashi a hannu Halifa Umar a yakin Kadisiyeh da Nehavand.
Za mu ci gaba insha Allah.
Komawa babban shafinmu Komawa saman wannan shafin
|