Almizan : kiwon lafiya ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 1 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
kiwon lafiya

AKWAI WANNAN MA


Daga Muhammad Kabari Al Kanawi


Godiya da yabo, sun tabbata ga Allah Ta’ala, Mahaliccinmu, abin bautar mu, wanda yake jujjuya al’amura bisa hikimarsa, Shi ne Gwani, Masani, Mai iko. Tsira da aminci mai tarin yawa su kara tabbata bisa Manzon Rahma, Shugabanmu, Annabi Muhammad (SAW) da ’ya’yan Dakinsa tsarkaka.

Allah ya kara taimako, kariya, shiriya, imani, ilmi da kusanci da Annabi ga Jagoranmu, kuma Malaminmu, wanda ya cika shekaru 54 a duniya a kwanakin baya. Allah Ta’ala ya kara lafiya da tsawon rai a cikin da’arsa da kira zuwa ga hanyarsa.

’Yan uwa assalamu alaikum. Ta yiwu wasu su ce, me ya faru ne? Kwana da yawa an jima ba a ga rubutunmu ba. Ko rashin sukuni ne? Ko ko yau da gobe ce? Sai in ce, AKWAI WANNAN MA. Ko ba a lura ba? Abin da nake so na tunatar da mu a wannan karon shi ne, muhimmancin da ke tattare da kara sallamawa mika wuya, natsuwa musamman lokacin da aka yi mana muwafaka da kasantuwa a gaban Malamai (Hafizahumullah) a majalisi ne, ko wajen wa’azi, ko wajen zanen suna, ko daurin aure, ko wajen wata muhadara, ko ma wajen tafsiri!

Idan na ce Malamai kun san abin da nake nufi. Na kawo a jam’i ne domin na tunatar da mu wani karatun da muka yi a baya. Ko ba a lura ba?! Ladabi da girmamawa sun koyar da cewa ka yi magana da sigar jam’i maimakon ka ce, kai, ka ce, ku, maimakon, ka, ko, ki, ka ce ku. Ana gaishe ku. Ko ka ce ’yan uwa sun ce na gaishe da Malam. Ko ba a lura ba?

Mu koma kan tunatarwarmu, wanda muka kira AKWAI WANNAN MA. Da sannu za ku fahimci abin da nake nufi insha Allah! Na lura, na san kuma ba ni kadai bane, da yawa wasu mu ba sa cin ribar karatu, wasu ba sa cin ribar ilimi, wasu ba sa cin ribar tafsiri. Ta yiwu ka ce ba sa cin ribar zance ake cewa, sai in ce maka akwai wannan ma.

Akwai wani dan uwa da muke ‘khidma’ tare lokacin yana hayar babur ana kiran sa Jan Wuya (wanda suka shiga kurkuku ko ta hanyar Allah ko ta wata hanya daban sun san abin da ake nufi da Jan Wuya). Ban san ko yana da kyau a ci gaba da kiran sa da wannan suna ba, sunansa Abdulhamid Isa. Abin da nake so in kafa hujja da shi a nan shi ne; akwai wani dan uwa shi kuma da ke zaune a Kano, yana ganin ‘Brother Abdulhamid da jar riga da ma jan wando! Ko ba a lura ba! Wata rana sai ya hadu da wani wanda ya san dan uwa Abdulhamid a can Kano, sai ya ga hoton Abdulhamid a can, sai ya yi mamaki. Sai dan uwan can ya ce da shi ka san shi kuwa? Sunansa Jan Wando! Sai mutumin ya ce masa Jan Wuya dai. Mun yi sana’ar kabu-kabu da shi. Sai wancan dan uwa ya ce masa akwai shi da Jan Wandon ma. Ina fata ana fahimta ta. Sai ya ce akwai wannan ma. Wato akwai wani abin da ba ka sani ba. Ka da ka ji an karanta aya ka ce ba haka bane, ko kuwa kai a tafsirin da ke gabanka ba haka aka ce ba, ko kuwa a kira’ar da ka sani ba haka abin yake ba, yanzu ka ji an ce ma akwai wannan ma. Ko ba a lura ba?

Kazalika shi wancan dan uwa mazaunin Kano, wata rana mun hadu da shi a Zariya, sai ga wani dan uwa daga Kankiya ya zo, ya same mu. Bayan mun gaisa sai ya tambayi dan uwa yaya su Malam Yusuf? Sai na ce Malam Bashir dai! Sai dan uwan ya ce mani, akwai wannan ma. Wato ni Malam Bashir Yusuf na sani. Akwai kuma Malam Yusuf Kankiya. Ma’ana na yi ‘fawul,’ shi kuma ya gyara min karatun. Ko ba a lura ba?

Da mutane za su kara sallamawa su natsu da sun cin ribar tafsiri, da sauran abubuwa. Allah Ta’ala ya tabbatar da mu! Kada ana cikin magana, ka yi tsalle (kai ko kana zaune ba ka yi tsalle ba), kada ka ce ai kaza ne, ko kuwa ka ce ga yadda yake, to lalle za ka sha mamaki, kila ma har da kunya sai ka sha, ko sai ya sha. Yawwa akwai wannan ma!

Wannan yakan faru. Ko ba a lura ba. Shi ya sa muka ga ya dace mu tunatar da juna a kai, ko ba komai ana yi mana tarbiyya ne, ya kamata kuma in an girma a san an girma! (Kul Rabbiy), sai wani ya yi zumbur ya ce (Kala Rabbiy), sai ka ji Malamai, da tausayawa sun ce. Akwai wannan ma. Wato kira’ar da ka sani kenan, akwai kuma wata kira’ar. Kira’ar nawa ta? Daya ta? Ko biyu? Ko ko sun wuce haka? Nemi sani ka ga ka tabbata. Bida ake cewa ko kuwa nema? Wane yana nema, ko kuwa wane yana bidar aure? Alahwadu alhtaniya (saboda su ikhwanuna in an ka ce wane na neman wance, to al’amari ya lalace). (Nushran baina yadai rahmatihi). Sai wani ya ce (bushran ne) sai a ce masa akwai wancan ma.

Rajab watan Allah ne, Sha’aban watan Manzon Allah (SAW), Ramadan watan al’ummar Annabi. A wata ruwayar da aka samu daga Ameerul Mumineen, Imam Aliyu (AS) ya ce; Rajab watansa ne (Imam Ali), Sha’aban watan Manzon Allah, Ramadan kuma watan Allah! Ko ba a lura ba? Ka ga akwai wannan ma! Wato akwai wanda ka sani, akwai wanda ba ka sani ba. Saboda haka kada ana cikin jawabi ka ji an fadi wani abu da kai ba haka ka san shi ba, aya ce ko Hadisi ka je ka kwafsa. Ko ba a lura ba? Akwai (Fihi muhana), Akwai kuma (fihiy muhana). Akwai wannan ma. Akwai kira’ar fihi (babu ja), akwai kuma (fihee), (da ja). Akwai inda Fir’auna yake cewa a kyale shi ya kashe Musa (AS) in ya so ya kira Ubangijin nasa ya zo ya kwace shi, domin shi Fir’una yana jin tsoron kada Musa (AS) ya canza wa mutane addini (watakila yana tsoron Annabi Musa ya kawo wa jama’a Shi’a daga Madyana ne), ko kuma ya bayyanar da fasadi da barna a doron kasa! Ka ji manya suna wa’azin a zauna lafiya! A lura a wata kira’ar ya ce (wa an yuzhira) a wani wuri kuma an ce (au an yuzhira). Ko ba a lura ba? Akwai (wa an) akwai kuma (au an). Saboda haka AKWAI WANNAN MA!

Wanda ya wayi gari al’amarin musulmi bai dame shi ba, to ba ya cikinsu ‘falaisa minhum.’ Akwai kuma ‘falaisa bi muslimin.’ Akwai wancan da ka saba ji. Akwai kuma wannan ma da Malaman garinku ba su saba ji ba!

Kalmar Yateem (yatimi), da yawa ana fassara ta da maraya, wanda ya shiga hali na maraici, ya rasa uba ko uwa. Wasu na cewa a mutane wanda ya rasa mahaifi, a dabbobi wanda ya rasa uwa, a tsuntsaye wanda ya rasa duka biyun! Wasu ko suka ce duk wanda ya rasa dayan biyun ne ake kira maraya! Ko ba a lura ba? Ka ga akwai wannan ma. Akwai kuma wancan ma.

Abin da nake so na tunatar da mu a nan shi ne; kalmar ‘yatama’ (jama’in ‘yateem’ce) kamar yadda ya zo a suratul Nisa’i, yana nufin mata ne zawarawa wadanda aka kashe mazajensu a fagen fama, wajen jihadi. Su aka kira su ‘yatama.’ Wato maraya, ba lale wanda ya rasa mahaifi ko mahaifiya ba, a’a, duk wanda ya shiga hali na tausayi. Domin in muka lura shi ma marayan da aka kira ‘yatimi’ saboda ya shiga wani hali ne na tausayi, ya rasa uwaye, (iyaye), akwai wannan ma. Hali na maraici, hali wanda ya cancanci a tausaya masa. Saboda haka, akwai waccan fassarar ma!

‘Wattakhazu min mukama Ibrahim Musalla.’ Akwai wannan ma. Akwai kuma ‘Wattakhizu’ da sigar umurni, wancan kuma da sigar ‘fi’ili madi.’ Wato sun riki Mukama Ibraheem wajen salla, ko kuma, ku riki Mukama Ibraheem wajen salla. Ko ba a lura ba!

Shin wanda yake shiryayye yake shiryarwa shi ya kamata a bi, ko ko wanda ba ya shiryarwa sai dai a shiryar da shi, za a bi? Akwai ‘la yahdiy,’ akwai kuma ‘la yahiddiy’ ‘da tashdeedi da kisra.’ Akwai wancan ma!

Sau da yawa za ka ji Jagora (Allah ya dada kare shi) yana fada, ko a wajen jawabi, ko a wajen tafsiri cewa; akwai wannan ma. ‘Wala yakhafu ukbaha.’ Akwai kuma ‘fala yakhafu.’ Saboda haka, akwai wannan ma. ‘Wal anhum la’anan kabeera.’ Akwai kuma ‘wal anhum , la’anan katheera!’

Wanene ‘shahida shahidun min ahliha’ da aka ambata a cikin kissar Annabiy Yusuf (AS). Wasu da yawa sun ce wai wani wai yaro ne jarri, wanda ko magana ba ya yi. Akwai kuma fassarar da ta fi ma’ana da kan gado da kwanciya a rai, wadda muka ciro ta daga Maulana, Malaminmu kuma Babanmu, Allah Ta’ala ya kare shi, ya tabbatar da mu a karkashin jagorancinsa da ya ce; ‘Shahidun min ahliha’ wani dattijo ne kamili mai hankali mai hikima ba jariri ba. Ko ba a lura ba? Ka ga akwai wannan ma.

Ka san wasu karatun (mankama) ne da su! Wasu kuma (Mannakum). Ashe ka gane! Wata kissa ce mai ban mamaki tausayi da dariya. A nan kasar ne, wannan abin ya faru. Da sannu da izinin Allah za ka fahimci dalilin da muka ce wasu karatun ‘mankama’ ne da su. Wani Malami ne da dalibansa sukan zo karatu, kowa ya biya (karanta) littafinsa, galibi babu wasali. To sai wani daga cikin daliban ya zo karatu ya kawo kan kalmar ‘minkum,’ wato daga gare ku, sai ya ce “mankama.” Sai Malaminsa ya ce, a’a, duba dai da kyau. Sai ya kara cewa “mankama.” Aka ce anya kuwa? Sai ya ce “man nakum!” Wato maimakon ya fada daidai, sai ya kuskure, da aka ce ya gyara, sai ya kara kwafsawa, ya kara manne karatun! Maimakon ‘minjayen’ farko ya ba shi kisra, sai ya aza masa fataha, ‘nunun’ kuwa ya daure ta. Ya ce “wannan.” Kaulasan kuma sai ya maka masa fataha, maimakon rufu’a. Mi’arar karshe kuma, maimakon sukun (dauri), sai ya zabga mata fataha, wasali bisa! Ina ruwan mankama! Da aka nemi ya duba da kyau, sai ya sake bata karatun, ya ce mannakum! Maimakon minkum. Mutumin sun yi karatu da Marigayi Shaikh Nasiru Kabara (Allah Ta’ala ya rahamshe shi).

Don haka daga nan sai abin ya zama sara. Wato idan ana so a nuna cewa wasu ba su fahimci karatu ba, yin sa kawai suke ba kan gado kamar kidan girbi, sai a ce masu karatun mankama. Ko ba a lura ba? Wanda ya san kissar, da ka ce mankama, shi kuma sai ya ce ko kuma mannakum ba! Wato duk ba daya, balle kanwar biyu!

Da yawa wadanda ake kira Malamai da Ustazai a nan kasar, karatun mankama ne da su! Ko kuma ‘mannakum’ ba! Yawwa ashe ka gane. Allah Ta’ala ya azurta mu da ilimi mai amfani, ya kiyashe mu bata bayan shiriya!

‘Waman indahu ilmul kitab.’ Allah Ta’ala ya isa shaida, kazalika, wanda ilmin littafi ke tare da shi! “Kafa billahi shahidun bainiy wa bainakum.” “Waman indahu ilmul kitab. ‘Su’ali’ (tambaya), wa ake nufi da ‘man indahu ilmul kitab?’ Jawabi; (amsa), wasu sun ce wani Bayahude ne. A wata fassarar da ta fi kan gado, ta fi inganta kuwa, an ce Imam Ali ne, Sarkin Muminai (Amincin Allah ya kara tabbata a gare shi). Abul Hasanaini, Angon Zahra (Salamullahi Alaiha) Babu madinatu ilmi Rasulillahi, Wasiyyin Annabi, Surukin Annabi, wanda ya fara imani da Annabi (SAW)! Saboda haka, akwai wannan ma. Ko ba lura ba?

A cikin kissar Annabi Sulaiman (AS), an ambaci wanda ya ce zai zo da gadon Bilkis a cikin kiftawar ido, shi ne Asif dan Barkhaya, Wasiyyin Annabi Sulaiman (AS). Mu lura me Allah Ta’ala ya ce dangane da wancan bawan Allah? “Wakalal laziy indahu ilmun minal kitab.” Yawwa, “indahu ilmun minal kitab, wato ilmi daga littafi. Shi kuwa Imam Ali Wasiyyin Manzon Allah, “wa man indahu ilmul kitab” (ilmin littafi), wancan kuwa ilmi daga littafi. Wannan duk ilmin littafi, wancan kuwa wani bangare, sashen ilmin littafi. Tirkashi! Wani aikin sai mai aikin. Duk masu ja da Imam Ali (AS) a da da yanzu sun gama yawo, sun lalace, kuma sai sun tozarta!

“La yuhibbuhu illa muminun, wala yubgiduhu illa munafik.” A suratul Kasas. Wasu na cewa, “laula an mannallahu alaina la khasafa bina.” Ko kuma (la khusifa). Akwai wannan ma. Akwai khasafa, akwai kuma khusifa (wato bina’i a kan majhuli).

‘Su’al’ (tambaya) me ake nufi da kalmar ‘kailu’ da ‘waznu?’ ‘Jawab’ (amsa), duk mutanenmu suna fassara shi da awo. Ko ba a lura ba? Suna ce masu ma’aunai! Alhali, ‘kailu’ shi ne wanda ake aunawa da mudu, ko a zuba a wani abu kamar awon kananzir, ko fetur. Shi kuwa ‘waznu’ shi ne abin da ake daurawa a sikeli ya ja a ga nauyinsa! Mizani ya kamata a kira shi. Lalle Hausa ta rasa gata. Da za ku natsu ita kanta Hausar ma za su kyautata maku ita.

Watakila a rubutunmu na gaba insha Allah za mu dora a kan inda muka tsaya, domin magana in ta yi tsawo sai a manta da wani bangare nata. Saboda haka akwai wannan ma. Zan dakata a nan saboda karancin ilmi da rashin sukuni. Na fara rubutun nan tun kafin Nisfu Sha’aban, ga shi yau 10 ga watan Ramadan. Wanda ya zo cewa ita ce (10/Ramadan), ranar wafatin Sayyidah Khadija (AS), matar Manzon Allah (SAW). Kamar kai ka ce, mummunar ala’adar nan, ta ‘tashe’ da cin zarafin gwagware marasa aure (bayan da sun yi) da ake yi a wannan kasa, wadda kuma ba a yin ta sai da watan Ramadan, kuma ba a fara wannan cin zarafi, da isgili sai ranar 10 ga wata, tamkar dai ana ‘shammati’ ne da isgili ga Manzon Allah da masoyansa.

Lalle tushen wannan zai iya kasancewa daga wajen makiya Manzon Allah ne da Iyalan gidansa kamar yadda suka kirkiro hadisai domin su rufe ta’asar da suka yi na danne ’ya’yan Annabi (SAW), suka yayyanka su a Karbala ranar 10 ga Muharram (Ranar Ashura)! Allah Ta’ala ya kara rahma ga uwargidan Manzon Allah, Nana Khadija (AS).

Allah Ta’ala ya la’anci makiyanta da makiyan Mijinta da makiyan ’yarta Sayyidah Zahra’u (AS) da makiyan Surukinta da makiyan Jikokinta, ya tattara su, ya wurga a wuta! Allah Ta’ala ya saka wa Malaminmu, Jagoranmu, mai kira zuwa ga Allah, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da alkhairi, ya sanya mu cikin wadanda zai tabbatar da addini da su, kada ya canza mu da wasu ba mu ba! Allah ya gagguta bayyanar mai ceton wannan al’umma, Imam Mahdi (AS), ya sanya mu cikin wadanda za a ’yanta daga wuta.

Bissalam Muhammad Kabir Alkanawiy, Mafi Kankantar Khadiman Cibiyar Malam (H) Fudiyyah Islamic Centre Zariya.

GINA SHAKSIYYAR ’YAR UWA MUSULMA (3)

Ci gaba daga ALMIZAN ta 692

MACE MUSULMA DA ’YA’YANTA

Duk macen da ta dauki ciki, to ya hau kanta ta yi addu’ar Allah Ya kare ’ya’yansu daga sharrin Shaidan, ta ‘Allahumma janibbul Shaidan wa jannibbunal Shaidan ma razaktana.’ Sannan kuma idan ta samu cikin ta rika karanta; rabbi inniy nazartu laka ma fiy badaniy muharraran fa takabbal minniy.’’

Idan mace tana da ciki kowane numfashi ana rubuta mata lada a kankare mata zunubi. Kuma idan ta haihu za a gafarta mata kurakuranta kamar ranar da aka haife ta. Idan tana shayarwa, matan (Huril’een) suna roka mata gafara, a rubuta mata lada a kuma kankare mata kurakuranta.

Yana da muhimmanci wanda za ta yi unguwarzoma ta zama saliha, dakin haihuwa ya zama mai tsafta, babu wasa a wurin. Idan an haihu a yi addu’o’i a jikin yaro a kuma tofa a kwano a ba shi, ana karanta masa Ayatul Kursiyu kullum. Kuma ana karanta masa “Rabbi u’izuhu bika wa zuriyyatuhu minas shaitanir rajiim. Rabbi haffizhu min bayna yadaihi wa min khalfihi wa an aimanihi wa min faukihi wa tahtihi wakzifit tauhidati fi kalbihi wa a inniy ala tarbiyyahtihi ya arhamar rahimeen.” Da addu’o’i masu yawa da aka kawo a littafin addu’o’i kamar su Sahifah Sajjadiya da sauran su.

A kula da abincin yaro idan ya isa cin abinci, a ba shi mai gina jiki idan da hali. Kamar irin su madara, kwai, wake, hanta, kifi, nama da makamantansu. A kula da sa masa ‘Nafkin,’ sannan kuma a rika canza masa a kai, a kai. Idan kuma za a wanke ‘Nafkin’ din a rika sa sinadarin kashe kwayoyin cuta na wanki, wato ‘parazone.’ A kula da yi wa yaro wankan safe da yamma, idan zai kwanta bayan ya yi datti a jikinsa. A tarbiyyantar da shi tsoron Allah, son Annabi, karatun Alkur’ani da son Iyalan gidan Annabi (S), domin su yara ne Allah ya ba mu, kuma zai tambaye mu a kansu. Saboda haka a sa ido sosai dangane da irin abokan da yaro ke yawo da su, kuma a nuna musu so da kauna da tausayi.

Manzon Allah ya ce, “wanda ba ya girmama manya namu, ba ya cikinmu, haka ma wanda ba ya tausaya wa kanananmu.” A kuma kula sosai da tarbiyyarsu da karatunsu. Idan sun girma a hada mata da mazaje nagari, maza kuma da mataye nagari a wajen aure.

MACE MUSULMA TARE DA MAKWABTA

Yana da kyau sosai, musamman ma don yada da’awa mace musulma ta kasance tana da kyakkyawar dangantaka da makwabtanta. Ta rika yi musu ihsani, ta rika kai musu ziyara tare da taya su murna idan abin murnar ya taso, da kuma taya su bakin ciki a lokacin bakin cikin, ta kuma rika yi musu kyakkyawan zato.

Manzon Allah (S) yana cewa: “An aiko ni don na cika kyawawan dabi’u. Kuma wanda zai fi kusa da ni a ranar tashin kiyama shi ne wanda ya fi kyawawan dabi’u, wanda yake magana ta tausayi.” Kuma ya ce: “Wanda imaninsa ya fi cika a cikinku shi ne wanda ya fi kowa kyawun dabi’a ko da yana da karancin ibada.”

Kamar yadda aka ruwaito cewa wata mata tana cutar da makwabtanta da harshenta, amma kuma tana da yawan ibada, sai Manzo ya ce tana cikin wuta. Sai kuma aka ce masa akwai wata baiwar Allah wadda take kyautata wa makwabtanta, amma kash! tana da karancin ibada, sai Manzon Allah (S) ya ce tana cikin Aljanna. Saboda haka sai mu kula da aikinmu, don ba zai yiwu mu aikata sharri kuma mu girbi alheri ba. Lalle duk wanda ya aikata sharri, to sharin zai girba. Don haka sai mu dukufa wajen aikata alheri kenan.

SALLAR DARE

Idan mutum ya je kwanciya ya kwanta da alwala, sannan ya yi addu’o’i irin su Ayatul Kursiyyu, Kulhuwallahu, Falaki da Nasi da kuma Alhakumuttakathur, sai ta karkade shimfidarsa ya kwanta. Ya zo cewa Shaidan na daure mai barci da igiyoyi guda uku. A kowane kulli ya rubuta “kana da sauran dare.” Idan ya farka ya yi Ta’awizi, sai igiya daya ta kwance. Idan ya yi alwala, sai wata igiyar ta kwance. Idan ya yi salla, sai sauran ta ukun ma ta kwance. Duk wanda ya yi alwala mai kyau ya zo ya kabbarta salla saboda Allah da ikhlasi, to Mala’iku za su yi sahu bakwai a bayansa. Ga kowane sahu za su cika su kai nisan gabas da yamma. Kuma ana ganin mai tahajjud a sama kamar tauraro mai walkiya. Duk mai barci har asuba, to Shaidan ya yi masa fitsari a kunne.

Mahaifiyar Annabi Sulaiman (AS) tun yana da shekaru sha biyar take yi masa nasiha da ya daina yawan barci da daddare, domin duk mai yawan barci zai zo ranar tashin kiyama fakiri.

Allah na cewa: “Sasanninsu na nisanta daga wuraren kwanciya, suna kiran Ubangijinsu bisa ga tsoron Allah da imani, kuma don ciyarwa daga abin da muka azurta su.” Sajdah: 16.

Sallar dare na da fa’idoji da yawa wadanda suka hada da cire tsoron duk wani mahaluki da ba Allah ba. Ga karin arziki da lafiya da sanya farin ciki. Sannan kuma kashin gadon baya na daidaituwa.

MANAZARTA

1. Tarjamar Alkur’ani mai girma ta Marigayi Shaikh Abubakar M. Gumi.

2. Shakhsiyyatul Aliyu Hashmy.

3. Mizanul Hikmah na Muhammad Rayshahry.

4. Mujallar ‘Muslim Health’ ta daliban BUK.

CUTAR KUTURTA (Leprosy (Hansen’s Disease)

Kodayake cutar kuturta bata cika yaduwa barkatai ba a tsakanin mutane, amma lalle cutar fata ce mai yaduwa daga wannan mutum zuwa ga wannan, musamman tsakanin iyali, wato ma’aurata da ’ya’ya ko iyaye da sauransu.

KWAYAR CUTAR KUTURTA

Kwayar hallita mai cutarwa dangin “bacteria’ mai suna ‘mycobacterium leprae’ ita ce ke haddasa wannan muguwar cutar fata a jikin dan Adam.

ALAMOMIN KUTURTA:

Alamomin cutar kuturta suna da yawa kasantuwar kuturta ta kasu kashi-kashi kamar yadda masana suka gano. A nan za a ga wasu alamomi na dunkule ga kowace irin kuturta kodayake za a iya samin bambanci gwargwadon irin cutar, wato a rabe-rabenta kamar yadda bayani zai zo insha Allah.

Jami’an tsaro sun ba da sanarwan cewa jama’a ya sa daular ta ci gaba wanzuwa kuma ta zama wata samfuri a zamunnan da suka biyo baya lokacin. A idan aka dubi jikinsa baki daya za a lura da wasu tabbai kala-kala masu launi a jikin fatar. Sannan labbansa da bakinsa da idanu da al’aura da hanci duk za su canza yanayi.

Fatar jiki kuwa za ta kasance ta canza yanayin amsa da fassara sakonin kwakwalwa da yanayin da jiki ya sami kansa. Abin da nike nufi shi ne kamar yadda fata za ta fahimci zafi ko sanyi ko haske ko wani radadi, ko zafi kamar tsunguli da sauransu. Wato za a iya ganin canji bisa fatar jiki a wadannan yanayi, ainihin jiki ya kasa fassara hakikanin zahirin abin da ya shafi fatarsa.

Wadannan sune manya a takaice, kodayake za a iya ganin abubuwa da yawa ga wadanda ke tare da cutar kuturta, musamman idan ana maganar rabe-rabenta.

RABE-RABEN CUTAR KUTURTA:

Ana gane rabe-raben cutar kuturta gwargwadon irin kwayoyin cutar da suke shigewa marar lafiya. A cikinsu akwai wadanda suka fi saurin yaduwa da cutarwa, akwai kuma masu saukin matsaloli da yawa ko saurin yaduwa.

Kungiyar lafiya ta Majalisar Dikin Duniya (WHO) ta fitar da wani sharhi a kan rabe-raben cutar kuturta bayan dogon nazari da masana wannan cuta suka gabatar kamar haka: ‘Tuberculoid’ (TT) ‘Baderline Tuberculoid (BT)’ ‘Borderline (BB)’

Wadannan sune nau’i masu saukin cutarwa da saukin saurin yaduwa a tsakanin mutane kasantuwar ba taron dangin kwayoyin cuta ne ke haddasa wadannan ba wato ‘Paucibacillary forms.’ ‘Borderline Lepromatous (BL)’ ‘Lepromatous (LL)’

Lalle wadannan sun fi muni da saurin yaduwa a tsakanin mutane saboda taron dangin kwayoyin cutar da kan yi sanadin wannan wato ‘Multibacillary Forms.’

ALAMOMIN RABE-RABEN KUTURTA:

Kasantuwar duk bayanan da za a gani a nan takaitattu ne, kuma hikimar wannan nazari shi ne mu san cutar da abin da ke haddasa ta da wasu alamomin da za su iya bayyana a yi hanzarin neman agajin Likita a asibiti. Sannan hatta likitoci da jami’an lafiya irin wannan bayani da nazari yana amfanarsu idan sun so, ballantana wadanda ba su da masaniya a kan wannan fanin.

Don haka sai an yi hakuri da irin yadda bayanan suke tahowa. Na yi wannan dan sharhi ne saboda bayani a kan alamomin cutar kuturta yana son dogon bayani da nazari, amma na zabi yin wannan bayani na wasu karin alamomin gwargwadon rabe-raben cutar kamar haka:

1. TUBERCULOID LEPROSY:

a) Babbar alamar irin wannan kuturta, wato ‘Tuberculoid’ ita ce taurin fatar jiki da tsoka, wato idan aka taba fatar a ji ta yi tauri sosai.

b) Rashin iya tantance zafi ko dari bisa fatar jiki.

c) Rashin iya tantance zafi ko dari a jikin mutum yana yin sanadin jin raunuka daban-daban a wurare daban-daban bisa a irin wannan nau’in kuturta.

d) Tabbai manya na kurajen kuturta wadanda ke sanya fata ta yi baki ko kaloli daban-daban.

2. LEPROMATOUS LEPROSY:

a) Abin da ya fi shahara a alamomin irin wannan kuturta shi ne cabewar kurajen jikin maras lafiya wadanda za su rika zubar da rowan kurji ko mugunya.

b) Manyan kuraje a fuska da bisa kunnuwa da bisa hannuwa da kafafu.

c) Za a iya ganin kurajen a wani lokaci sun sha bamban da juna wato kala.

d) A irin wannan sakonin kwa-kwaiwa ba su cika saurin yankewa ba, a bisa fatar jiki.

e)Hanci a wasu lokuta zai rika fitar da jini da wani irin ruwa.

f) Kafafu za su kumbura daga can kasa.

3BORDERLINE LEPROSY:

Kamar yanda za a iya ganin, alamar fassara wannan kalma wato ‘Border line’ da harshen Hausa lalle haka ne a nan ma. Wato irin wanan cutar kuturta ta tattaro wasu alamomin irin cutar ‘Tuberculoid’ da ‘Lepromatous.’ Kenan za a iya ganin wasu alamomin wannan da waccan a jikin marar lafiya. Wannan kuma dai duk a takaice ne. Da fatan Allah ya kasance tare da mu, ya yafe mana kurakuran da muka yi.

MAGANIN CUTAR KUTURTA:

Kodayake wasu sun dauka cutar kuturta bata da magani kasantuwar kwayoyin cutar kuturta miskilai ne; amma babu daya daga cikinsu wanda ba a iya ganin bayanta da magungunan kisan kwayoyin cuta (Anti Biotic Drugs) wadanda aka tanada domin wannan.

Abin da kawai ake bukata shi ne kada a bari cutar ta yi kamari a jiki, wato a hanzarta zuwa asibiti domin sha da karbar magani, musamman don a hana maras lafiya ci gaba da yada wannan muguwar cuta ga ’yan uwa da abokan arziki kamar yadda bayani ya gabata a kan haka.

A kasashen da wannan cuta ta bayyana a matsayin annoba, lalle ya kamata a sanar da hukuma don ta shirya matakan agazawa wadanda suka kamu, da kuma hana ci gaba da yaduwar wannan cuta.

Yayin kulawa da masu fama da wannan cuta, ya kamata kowanensu ya san alamomi da ire-iren raben-raben cutar kuturta don ya iya fahimtar canjin da zai iya samu a jikinsa, kasantarwar cutar na iya canza salo da kamannu.

Zan takaita a nan a kan cututtukan fatar jiki, da fatan ’yan uwa za su saka ni cikin addu’o’insu, Allah ya ba mu lafiya da iyalanmu da al’ummar musulmi baki daya. Allah ya taimaki Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da kiransa; Allah ya zabe mu, mu kasance cikin mataimakansa, amin. Wasslamu alaikum.

Naku Abdulkarim Usamah (ABU SHAHEEDAH KARIM KATSINA) 13 Satumab, 2005

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International