Almizan : Wakilanmu ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 8 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Wakilanmu

‘Imam Ja’afar (AS) ya sha wahala wajen tabbatar da adalci’




Na’ibin Limamin Juma’a a birnin Tehran, kuma Shugaban Hukumar kare tsarin mulki a Iran, Ayatullah Ahmad Jannati ne ya jagoranci al’ummar Musulmi sallar Juma’a da aka gabatar a babban masallacin Juma’a da ke Jami’ar Tehran a makon jiya.

A lokacin da yake gabatar da hudubobin sallar Juma’a, Ayatullah Jannati, ya fara ne da kiran al’umma zuwa ga lizimtar tsoron Allah kamar yadda aka saba a kowanne mako.

A lokacin da yake kawo munasabobin da suka wuce a makon da ake ciki, ya fara ne da kawo Shahadar Imam Ja’afar Assadik (AS), inda ya bayyana cewa ya yi zamani da Sarakunan Banu Umayya da wasu daga cikin Abbasiyawa, sannan ya tabbatar da cewa lalle Imam Assadik (AS) ya sha wahala sosai wajen ganin ya tabbatar da adalci a tsakanin al’umma ta fuskar koyarwa da kuma nuna dabi’u na kwarai.

Shi ma Na’ibin Limamin Juma’a a birnin Tehran, kuma Shugaban Hukumar fayyace maslahar tsarin Musulunci a Iran, Ayatullah Hashemi Rafsanjani ya bayyana irin muhimmiyar rawar da Imam Assadik (AS) ya taka wajen karfafa ilimi da fikirar al’umma wadda aka nemi tarwatsawa a lokacin Sarakunan Banu Umayya, wanda ya ci gaba har lokacin farkon mulkin Abbasiyawa.

Ayatullahi Rafsanajni, ya nuna cewa a wancan lokacin Assadik (AS) ya yi cikakkiyar amfani da damar da yake da ita ya cika abin da Mahaifinsa, Imam Al-Bakir (AS) ya soma na yada ilimi da kawar da munanan akidu da aka fara dasawa.

Shi dai Imam Assadik (AS) ya yi shahada ne sakamakon shayar da shi guba da aka yi a ranar 25 ga watan Shawwal a shekara ta 148 bayan hijirar Manzon Allah (S) a lokacin mulkin Dawaniki, daya daga cikin sarakunan.

Imam Ja’afar Assadik (AS) dai shi ne na shida a cikin jerin Limaman gidan Manzon Allah (S) wadanda duk ruwayoyi suka zo kan zuwan su daya bayan daya bayan Manzon Allah (S). Na karshensu shi ne Imam Mahdi (AF).

Imam Assadik (AS) ya fara samun tarbiyya ne daga Mahaifinsa Imam Al-Bakir (AS) a lokacin yana raye, sannan kuma shi kansa ya zama Limamin al’umma na kimanin kamar shekaru 34, inda ya sami damar yada ilimi da tarbiyya a duniya.

Sama da almajirai manya 4,000 ne suka yi karatu a hannun Imam Ja’afar Assadik (AS) cikin su kuwa har da Imam Malik da Imam Abu Hanifa Limaman mazhabar Musulunci da ake da su yanzun haka a duniya.

Dukkaninsu sun tabbatar da cewa lalle a lokacin Assadik (AS) babu wani mai falala ko daraja kamar sa. Imam Malik yana cewa bai taba ganin wani mutum mai ilimi da tsoron Allah ba a lokacin kamar Imam Ja’afar Ibn Muhammad Assadik (AS).

Hatta makiyin Imam Ja’afar (AS) kamar Addawaniki, wanda shi ne ma ya yi sanadiyyar ajalinsa, suna nuna cewa lalle Imam Assadik (AS) yana cikin wadanda Allah Ta'ala ya zaba.

Haka nan kuma, Ayatullah Jannati, ya yi magana a kan makon ’yan ‘Basij’ wato rundunar da Marigayi Imam Khumaini (RA) ya yi umurni da a hada ta bayan cin nasarar juyin Musulunci da aka yi a kasar, inda ya bayyana cewa; ‘Basij’ samari ne da ake so su rayu kan koyarwa ta addini, sannan su koma ga Allah kan wannan hanya.

Su ’yan uwa Musulmi ’yan ‘Basiji’ a Iran, sune wadanda suke kare juyin Musulunci da aka yi ta kowane bangare, kuma babban manufar Marigayi Imam Khumaini (RA) na assasa wannan runduna shi ne don haka nan.

A karshe Ayatullah Jannati, ya yi magana kan makamashin nukiliya na kasar Iran, inda ya kara tabbatar da cewa wannan abu hakkin Iran ne, kuma babu yadda za a yi a ja da baya a kai.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International