Almizan : Abubuwan da za mu koya daga rayuwar Sayyada Zahra (AS) (1) ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 15 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Dandalin Iyali

Abubuwan da za mu koya daga rayuwar Sayyada Zahra (AS) (1)


Daga Zahra’u El-Yakub


Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Tsira da aminci su kara tabbata ga Manzon rahama Muhammad dan Abdullahi da Iyalan gidansa tsarkaka, taurarin duniya da lahira da Sahabbansa managarta.

Nazari da bincike a kan rayuwar Sayyadah Zahra abu ne faffada ainun, wanda za mu iya misalta shi da iyo a teku. Amma za mu yi ne da nufin bijiro da yadda rayuwarta ta kasance don daukar darussan da ke cikinta, haka kuma don mu sanya ta a matsayin samfuri ga rayuwar Musulmi baki daya. Ta yadda za mu fahimci manufar rayuwarmu wadda domin ta ne Allah ya halicci dan Adam.

An haifi Fatimatuz Zahra ne ranar Juma’a 20 ga watan Jimada Thani a shekara ta biyar bayan wahayi. Mahaifinta shi ne Manzon Allah Muhammad dan Abdullahi, cikamakon Annabawa da Manzanni, rahama ga talikai. Mahaifiyarta kuwa ita ce; Nana Khadijatul Kubra (AS) matar Manzo (S) ta farko, wacce ta fara amsa kiran Manzo. Sannan kuma ta bai wa wannan addini muhimmiyar gudummawar da ba za a taba mantawa da ita ba har abada. Manzo (S) ya ce: “Wannan addini bai tabbata ba sai da dukiyar Khadija da takobin Ali da kariyar Abu Talib.”

Allah (T) ya yi wa Sayyidah Zahra baiwa da karamomin da ba za su kirgu ba. Tun asali ta zama fansa ga Mahaifinta daga gorin da mushirikai suke masa na ganin sa a matsayin mai yankakken baya. Shi ne Allah (T) ya ba shi Fatima (AS) kamar yadda ya zo a Suratul Kauthar. Sannan Sayyidah Zahra ta zama tsarkakakken tsatso daga tataccen rowan tuffah daga Aljanna, ta yadda har ma Manzon Allah (S) yana cewa idan ya so ya ji kamshin Aljanna yakan sumbaci Fatima ne. Kana ga shaidar sauki da rashin fargaba da zullumi da Nana Khadija ta bayar wajen daukar cikin Fatima (AS). Sannan ga magana da hira da ta gudana tsakaninta da Sayyidah Zahra tun tana cikin, kamar yadda ya zo a littafin Imamu Shafi’i da Dahlawiy. Kana ga mataye hudun da suka zo daga Aljanna don taya ta hidimar haihuwarta, inda ta zo duniya tana mai sujada ga Allah (T) tana mai daga yatsunta zuwa sama. Manzo ya yi farin ciki da wannan abar haihuwa, ya sa mata suna Fatima bisa wahayi daga Allah (T).

Cikin ikon Allah Sayyidah Zahra ta rika girma da gama-garin yara ke yi a wata ruwayar cikin sati daya. baya ga wannan suna tana da sunaye da yawa saboda girmanta da kuma daukakarta, kamar yadda ake cewa; “yawan sunaye na nuni ga girman mai su.”

Nana A’isha ta ce ba wanda ya yi kama da Manzon (S) a zamansa da tafiyarsa da zancensa kamar Fatima (AS).” Manzo (S) ya nuna matukar kauna ga wannan ’ya tasa. Yana yarda da yardarta, kuma yana fushi da fushinta, har ma ya yi nuni da cewa duk abin da ya same ta, to ya same shi ne kai tsaye da fadinsa; “Fatima tsoka ce daga gare ni, wanda ya bata mata, hakika ya bata min.” Kuma ya ce: “Fatima Allah na fushi da fushinta, yana yarda da yardarta.” To a nan za mu gane irin daukaka da matsayin da Allah (T) ya yi mata.

RAYUWAR SAYYADAH ZAHRA A MATSAYIN ’YA

Idan muka dubi rayuwar Sayyadah Zahra a matsayin ’ya, za mu same ta karkashin inuwar Mahaifinta, da tsakanin kirjin tsarkakakkiya Nana Khadija. Ta budi ido a gidan Annabta, ta taso karkashin inuwar wahayi kamar yadda Nana Khadija ta shayar da ita son imani da kyawawan halaye. Kodayake Allah (T) ya so Fatima (AS) ta fara rayuwarta ta kuruciya a cikin yanayin da ya fi kowane yanayi da da’awar Musulunci ta fuskanta na tsanani da cutarwa. Kuma ta fi yawan samun musgunawa da mugunta daga Kuraishawa wadanda a lokacin ne suka yanke hulda da Manzo (S), suka kuma sanya wa Hashimawa takunkumi.

Haka nan Fatima (AS) ta yi tarayya da Mahaifanta cikin wannan tsanani da rashi da aka kakaba musu. Da haka shekaru suka shude da Fatima (AS) cikin wannan hali mai tsanani da nauyi ba tare da gazawa ko raki ba duk da karancin shekarunta a wancan lokacin har Allah (T) ya bai wa Manzonsa nasara da galaba suka fita daga wannan hali.

Yayin da kuma Allah (T) ya kira Nana Khadija da kuma baffan Manzon Allah (S) Abu-Talib (R), a wannan lokacin Manzo (S) da karamar ’yarsa Fatima (AS) sun fuskanci wannan kadaici na rashin ginshikai guda biyu.

Haka nan Fatima (AS) ta fuskanci yanayi na maraicin uwa a daidai lokacin da ta fi bukatar ta, ta yi juriya, ta yi kuma namijin kokari wajen dauke wa Manzo (S) wannan rashin, inda ta dage wajen dafa masa, da kuma nuna masa kauna da tausayi a duk lokacin da wani abu ya faru a gare shi na cutarwa daga mushirikai. Misali Fatima (AS) ce ta je ta dauke wa Manzon Allah (S) rubabben tumbin da Abu Lahab ya dora masa a ka a yayin da yake sujada. Ta je tana kuka tana sa ruwa da hannayenta masu daraja tana wanke masa, tana tsinuwa ga masu cutar da shi (S).

Fatima (AS) ta kasance a kodayaushe mai nuna kauna da tausayi ce da soyayya ga Manzon Allah (S) kamar irin na uwa da da, shi ya sa ma yake kiran ta da uwar babanta, (Ummu Abiyha). Haka nan Fatima (AS) da Mahaifinta da sauran muminai suka ci gaba da fuskantar cutarwar mushirikai, inda a karshe har ta kai ga barazanar kashe Manzon Allah (S), wanda ya tilasta musu yin hijira daga Makkah zuwa Madina. Sayyidah Zahra (AS) ta shaidi yanayin da’awar Musulunci a Makkah, tare da jimiri, dagewa da jajircewa da Mahaifanta da sauran mumunai suka nuna, haka kuma ta shaidi hijira da yanayin zaman Madina a farkon lokaci.

Za mu ci gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International