Almizan : Abubuwan da za mu koya daga rayuwar Sayyada Zahra (AS) (2) ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 22 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Dandalin Iyali

Abubuwan da za mu koya daga rayuwar Sayyada Zahra (AS) (2)


Daga Zahra’u El-Yakub


Ci gaba daga makon jiya

AURENTA

Auren Sayyidah Zahra (AS) ya kasance tare da wanda ya dace da ita wajen daukaka da kuma kusanci ga Mahaifanta, wato Imam Ali dan Abu Talib (AS). Bayan da ya sanar da Manzo (S) bukatarsa zuwa ga Fatima (AS), da Manzo ya shaidi mata ta kuma amince sai ya daura musu aure a bisa wahayi daga Allah (T) da kuma sanarwar daura auren a sama da shaidarwar Mala’iku tun kafin a yi shi a nan duniya. Fatima (AS) ta bar gidan Mahaifanta zuwa gidan mijinta Ali dan Abu Talib (AS) da ake yi wa lakabi da Zakin Allah, Kofar Birnin Ilimi, Mabudin Haibara.

A nan ne Sayyadah Zahra (AS) ta baje irin tarbiyyar da ta samu daga gidan Annabta, wanda ta ba da kyakkyawan misali ga dukkan ma’aurata. Misali Fatima ta dage wajen jibintar lamarin mai gidanta da tausaya masa, nuna masa kulawa da soyayya da karfafawa kamar yadda ta sha daga Nana Khadija Mahaifiyarta. Sannan da kanta take hidimomi da aikace-aikacen gida, tare da taimakon mijinta, wani lokacin har da Mahaifinta wajen kula da yaranta da kuma renonsu.

An jiyo wata daga makwabtanta na cewa ta haddace Alkur’ani mai tsarki a wajen Sayyidah Zahra (AS) ba tare da ta je wajenta karatu ba. Wato ta hanyar sauraron Sayyidah Zahra (AS) daga gidanta yayin da take ayyukan gida tana yi, tana karanta Alkur’ani tana nika, ko girki. Wato a takaice ita wannan makwabciya ta Sayyadah Zahra (AS) ta haddace Alkur’ani mai tsarki ne ta hanyar sauraro ta kai-tsaye daga gidanta a tsakanin aikace-aikacen Sayyadah Zahra (AS) na wuni da kuma sallar dare. Tirkashi! Wani aikin sai masu shi.

Wato a nan za mu fahimci cewa Sayyadah Zahra (AS) da ta je gidan mijinta ba mike kafa ta yi ba, a’a, ta yi amfani da wannan dammar ne wajen kara neman kusanci ga Allah (T) da bai wa dukkannin ma’aurata samfur na taimakekekeniya wajen gudanar da harkar gida da iyali.

Sayyadah Zahra (AS) ta dage sosai wajen tarbiyyar iyalanta da ba su kulawa, ta so su, ta nuna musu kauna da tausayi irin na uwa da ’ya’ya, ta karfafe su, ta kasance takan sa su bacci da rana da ba su abinci marar nauyi da dadare don magance nauyin jiki a yayin sallar dare. Wannan ma wani samfari ne ga duk mai son nishadi. Fatima ta dage sosai wajen tarbiyyantar da yaranta, ta nuna musu kauna.

An rawaito cewar karshen aikin da Sayyadah Zahra ta yi a duniyar nan lokacin da shahadarta ta zo bayan ta yi wanka ta yi ado ta sa turare, sai ta kirawo ’ya’yanta Imam Hasan da Husain (AS) ta sa ruwa ta wanke musu kawunansu ta goge musu.

Haka kuma an ruwaito cewa daidai lokacin da ta cika a yayin da ’ya’yanta suka kwanta a kan kirjinta suna kuka an ga ta sa hannayenta masu daraja ta rungume su. Allah mai girma!

Sayyidah Zahra (AS) a rayuwarta bata manta da mabukata marassa shi ba a duk lokacin da suke da bukata sun san gidan da za su je su samu. Ta kasance tana fifita mabukata a kan kanta. Wanda a kan wannan sura guda ma aka saukar a kaknta da iyalanta aka yi musu shaida a kan wannan hali na girma.

Sayyidah Zahra (AS) ta kasance mai ba da kulawa ce sosai ga makwaftanta da kyautata musu. Imam Hasan (AS) ya ce; “Fatima ta kasance tana ibada da daddare a mihirabinta sai da alfijir ya fito. ,Daga karshe sai na ji tana yi wa mutane addu’a a wurin Allah (T), amma bata sa kanta ba. Sai na tambaye ta yaya ba ki sa kanki ba? Sai ta ce, ‘makwafta sannan gida ya dana.” Ta nan za mu gane irin yadda Fatima (AS) ta damu da makwabta da jama’ar Musulmi baki daya.

Idan mu ka lura da baki dayan rayuwar Sayyidah Zahra (AS) za mu gan ta a matsayin wani samfuri ga al’ummar Musulmi baki daya. Wato ta nuna kyakkyawan misali ga ’ya’ya yadda ya kamata su kasance wajen mu’amala da iyayensu. Haka nan ma ta koya wa matan muminai yadda ya kamata su yi musharaka wajen gudanar da gidansu da kuma cewa ciki ko goyo ko hidimar gida ba sa hana ibada. Su yi kokari su tsara rayuwarsu, sannan su jajirece wajen taimakon gaskiya da dafa mata kamar yadda ta nuna hakan wajen dafa wa Imam Ali (AS) wajen fafatawa da makiya gaskiya masu take wasiyyar Manzon Allah (S) wanda ta dage ta yi kokari ta ba da duk wata gudummawar da ta iya wajen ganin wasiyyar Manzon Allah (S) ta tabbata kamar yadda ta gogu da rayuwar jihadi tun a Makka har aMadina, wanda hakn ne ma ya yi sanadiyar shahadarta. Haka kuma ya kamata mu tuna da kasancewar Sayyidah Zahra (AS) a matsayin Shugabar Matan Duniya da kuma Matan Aljanna.

Wato duk wani yanayi da mace za ta shiga a duniya Sayyadah Zahra (AS) ta shige shi. Sai a sa rayuwarta a matsayin samfur, haka kuma duk wata mai neman kusanci ga Allah (T), kuma take son zama a karkashin shugabancin Sayyidah Zahra (AS) a Aljanna, to sai ta saka rayuwarta a gaba a matsayin samfur. To a nan ba mata kawai ba har ma da maza muminai. Abin da ya sa aka ce mata saboda su mata sune iyayen al’umma, kuma su ne masu tarbiyyantar da ita al’ummar, kuma iyaye musamman mata suna da tasiri a cikin rayuwar ’ya’yansu. Don haka sai mu dage mu yi kokarin koyi da Sayyidah Zahra (AS).

Allah (T) ya ba mu albarkacinsu, ya sanya mu a cikin cetonsu, ya saka wa Malaminmu, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da dukkan alherinsa, ya bar mu a karkashinsa, ya tabbatar da mu a tare da shi, amin.

MANAZARTA

·Alkur’ani mai tsarki

·Fatima Minal mahdi ilal lahad.

·Mu’ujaz Rasul (S) wa Ahli Batihi (AS).

Hadisan da aka danganta su ga Manzon Allah (S)

Haka nan kuma a zamanin Umar, ya kasance babu ruwansa da Ali Bin Abu Talib, ballantana ko ya tura masa wasu mutane, ko kuma wani abin da ya yi kama da haka. Kai, hasali ma, sun hana shi gadon Fatima, kuma sun hana al’umma su yi wata mu’amala da shi. Haka kuma, marubuta tarihi sun rubuto yadda suka tilasta wa Ali yin mubaya’a bayan rasuwar matarsa Fatima (AS), musamman a lokacin da suka yi ta ingiza mutane har suka soma juya masa baya.

Allah yana tare da kai ya Baban Hasan! Ai dole wadannan mutanen su yi gaba da kai, domin kai ne ka karkashe gwarzayensu, ka wargaza rundunoninsu, kuma ka hana mafarkinsu ya zama gaskiya. Kai ne wanda ba ka bar su da wani matsayi na-gani-na-fada ba ko daya. Dadin-dadawa, kai ne dan uwa ga wanda Allah ya zaba daga cikin mutane, Manzon Allah (SAWA). Kai ne mijin Fatima, Shugabar dukkanin matayen duniya. Haka nan kuma kai ne mahaifin shugabannin samarin Aljanna (Hasan da Husaini). Kai ne ka soma yin imani da Musulunci, kuma kai ne wanda ka fi dukkaninsu ilimi.

Kawunka Hamza, shi ne Shugaban Shahidai, sannan kuma Ja’afar Al-Tayyar, da ne ga mahaifi da mahaifiyarka. Haka nan kuma, Abu Talib, ‘Hadimi’ ga wurare mafifita, kuma wanda ke ba da kariya ga Manzon Allah (SAWA) shi ne mahaifinka. Haka nan kuma, Khalifofi (Khulafa’ur Rashidin), wadanda Manzon Allah ya yi bayanin sunayensu gaba daya, dukkaninsu daga tsatsonka suke. Kai ne ka yi wa wadancan na zamaninka fintinkau! Haka nan kuma wadanda suka zo bayansu, suma ka yi musu nisa. Kai ne Zakin Allah da Manzonsa, kuma kai ne takobin Allah da Manzonsa. Kai ne amintacce a wurin Allah da Manzonsa, kuma kai ne ‘Faruk’, kai ne aka tura ga makiya Allah, a yayin da babu wanda Allah da Manzonsa suka aminta da shi, suka tura shi sai kai. Kai ne mafi kololuwar masu gaskiya (baya ga Manzon Allah), kuma bayan kai da zuri’arka tsarkakaka (ma’asumai) kowannensu zai iya yin karya. Kai ne ‘Faruk’ na gaskiya, mai bambance karya da gaskiya, sannan kuma kai ne kake yi wa gaskiya rakiya domin ta murkushe karya. A gare ka ilimi yake, kuma kai ne mafi kololuwar haske (baya ga Manzon Allah). Kai ne wanda imanin mutum ba zai cika ba, sai ya nuna kauna a gare ka, haka nan a kan gane cikakken munafuki, shi ne wanda yake kiyayya a gare ka. Kai ne kofar birnin ilimin Manzon Allah (SAWA), duk wanda ke son shiga wannan birni, sai ya bi ta gare ka. Duk wanda ya shiga wannan birnin ta bayan gida, sunansa makaryaci.

A saboda haka nan sai mu duba mu gani cewa babu wanda ya zarce Ali a duk cikin Sahabbai. Shi ne mafifice a duk cikinsu. Wannan ne ya sa wasu suke yi masa kishi da hassada da baiwar da Allah ya yi masa, har kuma suke nisanta kawunanu daga gare shi, bayan kuma Allah ya zabe shi ya kasance a kusa da shi.

Hakika alkaluma sun yi rubutun bayanan Imam Ali Bin Abu Talib da yawan gaske, dangane da yadda wadannan mutanen suka zalunce shi a lokacin yana raye, da kuma yadda suka cuce shi bayan ya koma ga Mahaliccinsa. Haka nan kuma alkaluma sun yi bayanai kan yadda wadannan mutanen suka cuci Manzon Allah (SAWA) a lokacin yana raye da kuma bayan ya koma ga Mahaliccinsa.

Manzon Allah (SAWA) shi ne ya kasance a duk tsawon rayuwarsa ya rika fadi-tashi, da nuna musu shiriya, da kuma kauna, tare da ba da kariya ga wadanda suka yi imani. Amma kuma a daidai lokacin da zai koma ga Mahaliccinsa, sakamakon da suka yi masa shi ne, suka rika gaya masa maganganu marasa dadin ji, har suna cewa ba ya cikin hayyacinsa. Sune kuma suka ki bin umarninsa a lokacin da ya shugabantar da Usama a gaba gare su.

Haka nan kuma, sune jim kadan bayan wafatin Manzon Allah (SAWA) ba su tsaya an yi jana’izarsa a tare da su ba, sai suka garzaya zauren taro na Sakifa domin su yi zaben Khalifa. Babu wani daga cikinsu da ya nuna damuwarsa cewa ya kamata a tsaya a yi wa Manzon Allah (SAWA) sutura. (sai wadansu ’yan kalilan daga cikin Sahabbai suka tsaya). Haka nan kuma bayan wafatin Manzon Allah (SAWA), suke kan gaba wajen kushe shi da kokarin rage masa daraja, har suke nuna cewa shi ba Ma’asumi bane, bayan kuma Alkur’ani da hankali sun tabbatar da haka. Duk wadannan abubuwan da irin wadannan Sahabban suka yi, sun yi ne domin neman samun shugabanci a wannan duniyar mai karewa.

Sarakunan Banu Umayya, wadanda Mu’ayiwa Bin Abu Sufyanu ke yi wa shugabanci, duk sun haye kan khalifanci ne ta hanyar gado. Sun rika shugabantar al’umma daya-bayan-daya, ba tare da tunanin cewa wata rana shugabancin zai rabu da su ba. Amma abin tambaya a nan shi ne; me ya sa Banu Umayya suka ci gaba da rage darajar Manzon Allah (SAWA) har suka yi ta kirkiran hadisai wadanda suke rage darajarsa (S)?’

Da akwai dalilai guda biyu wadanda suka sa suka yi haka: Na farko, rage darajar da Banu Umayya suka rika yi wa Manzon Allah (SAWA), yana da nasaba da hassadar da suke yi wa Banu-Hashim, saboda yadda suka ga dukkanin kabilun Larabawa suna girmama su, saboda kasancewar Manzon Allah (SAWA) daga cikinsu ya fito. Wannan ya kara tabbata ne saboda yadda Umayya ke nuna kishinsa ga Hashim.

Haka nan kuma, Ali Bin Abu Talib ya kasance Shugaba ga Banu Hashim bayan wafatin Manzon Allah (SAWA), sannan kuma ga irin tsananin kiyayyar da Mu’awiya ya nuna masa, wanda a saboda haka ya daura yaki da shi saboda ya nisanta khalifanci daga gare shi. Bayan kuma sun shirya makarkashiyar kashe shi ya koma ga Mahaliccinsa, Mu’awiya ya sunnata la’antarsa a kan mumbarorin salla. Manufar Mu’awiya na sunnata la’anatar Imam Ali shi ne, domin ya san cewa duk wanda ya la’anci Ali, to kai tsaye ya la’anci Manzon Allah ne (SAWA).

Abu na biyu kuma na dalilan rage darajar Manzon Allah (SAWA) da Banu Umayya suka yi ta kokarin yi, shi ne ya tabbatar da irin ta’addancinsu da muguwar aniyar su wadanda suka fito fili.

Ku duba ku gani, Banu Umayya ne fa suka nuna cewa Manzon Allah (SAWA) yana bin son zuciyarsa saboda wai tsananin damfaruwa da ya yi da matansa har wai ya kan manta da wajiban da suka hau kansa (wa’iyazu Billahi!). Haka nan kuma suka nuna cewa wai Manzon Allah (SAWA) yana nuna tsananin kauna ga daya daga cikin matayensa, har a saboda haka ya daina yin adalci a tsakaninsu, wai har sai da (matan) suka yi aike gare shi suna rokonsa da ya yi adalci a tsakaninsu.

Wata makarkashiya da Umayyawan suka shirya dangane da haka shi ne, ta yadda suka kirkiri hadisai wadanda suka yada su, kuma suka gadar da su tun daga wancan lokacin, har zuwa wannan zamanin da muke ciki, inda a cikin irin wadannan hadisan suka yi bayanan da suka ga dama a kan Manzon Allah (SAWA), suka kirkiro ruwayoyi suka ce shi ne ya fada, ko kuma ya aikata, har kuma a yanzu irin wadannan hadisan suka zama sunna ga mafi yawan Musulmi.

A nan, bari na ba da misalin kadan daga cikin irin wadannan hadisan wadanda Banu Umayya suka kirkira suka danganta su da Manzon Allah (SAWA) domin su rage masa matsayi da darajar da Allah (T) ya ba shi. Ba zan kawo misali daga kowane littafi ba, zan tsaya ne kawai ga kawo misalai ne daga cikin littafan Bukhari da Muslim, wadanda suka ruwaito a cikin littafansu na cin zarafin Manzon Allah (SAWA).

Al-Bukhari ya ruwaito a cikin littafinsa, a wurin da yake bayani a kan wankan tsarki, a cikin babin da yake magana a kan wanda ya yi jima’i, ya sake yin jima’i.” “Wai an karbo daga Anas cewa wai Manzon Allah yana zagaye matayensa su 11, yana yin jima’i da su cikin awa guda a dare da rana.” Wai sai aka tambayi Anas aka ce, “Yanzu Manzon Allah (SAWA) yana da karfin da zai yi jima’i da matayensa haka?” Wai sai Anas ya ce, “ai Manzon Allah (SAWA) yana da karfin mutum 30 ne...”

Don Allah ku yi dubi ku gani ’yan uwana Musulmi, irin wannan hadisin maras dadin ji, wanda ya nuna Manzon Allah (SAWA) a matsayin wani mutum mai tsananin son jima’i, har a saboda hakan nan yakan yi jima’i da mata 11 a cikin awa guda, kuma wai yakan yi haka ne ko da rana ko kuma a cikin dare, ba tare da ya yi wankan janaba ba a tsakanin jima’in da ya yi da waccan, kafin ya yi da ta gaba.

Ku yi dubi ku gani ’yan uwa Musulmi, don Allah ya za a yi mutum ya rika tunkarar iyalinsa domin jima’i kamar yadda dabbobi suke yi, ba tare da gabatarwa (’yan wasanni) ba? Hatta su ma dabbobi idan muka yi dubi, ai sukan jima suna gabatar da wasanni kafin su yi jima’i. Idan haka ne ya za a yi a ce Manzon Allah (SAWA) wanda Allah ya fifita birbishin kowa, kuma ya yi masa shaida a cikin Alkur’aninsa na kyawawan dabi’u, kuma za a ce shi ne yake aikata wadannan abubuwan da suka yi bayani.

Su Larabawa, tun a wancan lokacin, har zuwa wannan lokacin da muke ciki, sukan yi alfahari da irin kwazonsu a fagen yin jima’i, wanda a cewarsu, ta haka ne ake gane namiji na gaskiya. A saboda haka ne suka danganta wannan halayya tasu ga Manzon Allah (SAWA). Hakika Manzon Allah (SAWA) ya fi gaban haka! Manzon Allah da kansa yana cewa “Kada ku je ga matayenku kamar dabbobi, ku yi wani abu wanda zai ta da muku sha’awarku da tasu.”

Za mu ci gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International