Almizan : Ba sauran zaman lafiya a Nijeriya idan Obasanjo ya zarce ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tattaunawa

Ba sauran zaman lafiya a Nijeriya idan Obasanjo ya zarce


Daga Shu’abu Lili


Alhaji Shu’aibu Lili, kwararren dan jarida ne, kuma tsohon abokin Obasanjo ne, ya san shi kamar yunwar cikinsa, amma yanzu yana cikin na gaba-gaba a cikin jerin ’yan Nijeriyan da ke adawa da shirin gyaran tsarin mulkin da zai bai wa Obasanjo damar ya zarce. “Ni a matsayina nan na zauna da Obasanjo shekara bakwai a Abeokuta. Yadda kake dan jarida, ni ma tsohon dan jarida ne. Shekarata 32 ina aikin jarida. Na zauna da Obasanjo na san halin Obasanjon. Hasali ma abin da ya sa na bar aikin gwamnati, ina mataimakin Janar-Manaja na kamfanin buga jaridun NEW NIGERIAN a 1999, sanin halin Obasanjo ya sa na bar aikin. Don haka idan wasu sun zo daga Arewa sun ce Obasanjo na kirki ne aka kawo, don ba ni da karfin da zan kare na ce a’a ne, wannan kuma wani abu ne daban. Amma ni na san Obasanjo, duk yawanmu a nan da Obasanjo zai shigo zai ce “Mista Katsina.

Ta kai fagen ina zama da Obasanjo lokacin kowa bai shiga gidansa, duk wanda yake Abeokuta, duk wai dan Ogwade-Ogwado ka tambaye su, saboda na yi zaman babban Wakilin gidan rediyon FRCN a Abeokuta, ni na bude ofishin Abeokuta, ni na bude na Akure, na yi aiki a Ibadan, na yi aiki a Legas, shekarata 15 a wannan dan tsakanin. Don haka na san Obasanjo ba sanin shanu ba.”

Amma me ya yi zafi haka, har ya zama yana adawa da sake zarcewar Obasanjo? Ga abin da ya bayyana wa Aliyu Saleh a wata hira da ta hada su da shi a Kaduna.

SHIGA OFISHIN SIYASA BA GADO BANE

In dai abin nan gaskiya ne cewa ana gyaran tsarin mulki domin a yi tazarce ne, kowa ya san wannan ba bisa ka’ida yake ba, saboda maganar shiga ofishin siyasa jama’a ne suke zabe, kuma a sanina ba a yi wata kuri’ar raba gardama ba a kasar nan wacce aka tambayi jama’a a kan cewa suna so a canza tsarin mulki, ko ba sa so. Na biyunsu wadanda suke kan mulki din nan sun san abin da ya kamata a yi, sun san ya kamata idan sun gama lokutan da ya kamata su zauna a tsarin mulki su bari. Idan suka bari su shirya yadda za a yi zabe su kasance su a matsayinsu ma ’yan ba ruwanmu ne dangane da wannan zaben. Duk wanda jama’a suka kawo shi ne mafi a’ala. Na uku shi ne shin ita siyasa da ofishin siyasa gado ne, da mahaifinka zai mutu a ce dole sai an ba ka? Wannan wani abu ne na jama’a, kuma kowa yana da hakki a kansa. Me ya sa tun tuni ba a gyara tsarin mulkin kasar nan ba domin kyautata wadansu al’amura sai lokacin da ake so a yi ta-zarce? Wannan dan takaitaccen bayanin da na yi ya kamata duk mai hankali ya fahimci me ake nufi.

BA A SAMU ZAMAN LAFIYA BA

Idan ra’ayinka ne cewa kasar nan ana da zaman lafiya, ni ba ra’ayina bane. A duk lokacin da yunwa, fatara, zullumi da tashin hankali suke tare da mutane, babu maganar zaman lafiya. Lafiya ma ba ta gitto ba, ballantana zamanta. Yau duk abin da ka fi karfi ya fi karfinka. Yau babu wanda - da mai shi da marar shi, da mai sarauta da talaka- da zai ce maka ya kwanta ya yi barci yadda ya kamata, hankalinsa a kwance. Sannan hatta abin da za a sa a baka yana gagarar jama’a. Babu aikin yi, in ka ce ba ka ba mutum ba, to ka sa shi hanyar da zai nema. Amma ba a yi tanadin wannan ba. Ina al’amarin kirki yake a Nijeriya? Ka fada min abu guda wanda yake na kirki ne da aka yi in banda zambatar jama’a da ake yi? Wadanne ayyuka aka yi? A fada min? Ayyukan da mutanen kauye za su ciko motoci su ce suna so a yi masu hanya, a dauki Naira daya rak a yi masu hanya, a ce Naira miliyan aka kashe? Shi ne aiki? Mun san fa duk abin da ake yi. Hatta hanyar da aka yi maku a kyauyenku ba ta yin wata biyu ko wata uku ta lalace. An riga an gama. Amma idan ka ga kudin da aka ce an kashe a kanta kai kanka za ka yi mamaki. Idan za a rarraba wa duk mutanen karkararku wadannan kudaden da aka ce an kashe za su wadata su samu hannun jari da za su yi wata sana’ar. Amma mutum daya ya zo, ko wasu mutane, sun yi hanya, shi kenan shekara ta lalace, badi kuma sai a sake dibar wasu kudin a je a sake gyaran wannan hanyar. Shi ne abin kirki? Shi ne ci gaba?

DA KARFI AKA DANKARA MANA OBASANJO

Mutanen da suka yi wannan din (suka dauko Obasanjo suka kawo mana shi) su suke gallaza mana azaba yanzu, saboda me? A matsayinku na ’yan Arewa wai mutum bai son ya ba da ransa saboda wani, amma dukkanmu duk wanda ya shafe shekara 30 da haihuwa ya san cewa Sardauna ya ba da rayuwarsa ne saboda amfanin jama’a. Mu yau ba ma iya tawakkalin mu bayar da rayuwarmu domin na baya da mu su gaji abin arziki. Abin da muka sani yanzu an koya wa mutane sata, an koya masu zamba, duk abin da Allah ba ya so mutane sun raja’a a kansa. Idan siyasa kake yi, na ga ka shiga wani mugun matsayi, kana cikin kukumi, me zai hana mu hada hannu ni da kai mu samu mu ceto kawunanmu, sai ya ce nawa za ka ba shi? Mutumin da ya san ciwon kansa kenan?

SAI MUN KOYI CEWA BA MU YARDA BA

Rashin basira ce ya sa aka dauko Obasanjo, idan ka gan ni nan, ni yanzu Bahaushe, mutumin Katsina ba za ka ce nine Arewa ba, har in kuma na zo na ce maka ni ne Arewa, kuma ka yarda da ni, to kai ne wawa, domin me? Sai dai ya zama ina daya daga cikin mutanen da suke a Arewa ne. Don haka idan har wasu ’yan tsiraru suka zo suka yi maganar cewa sune Arewa, kuma mutane suka zura masu ido, don haka duk abin da suka yi sai dai kuma a zura masu idon. Amma a lokacin da mun tashi mun ce ba mu yarda ba, da abin bai kai ga haka ba.

Amma da yake babu wanda yake so ya wahala don na baya gare shi ya ji dadi, shi kenan sai abubuwan suke ci gaba da tafiya a haka. Ko dauri da abawa mutunenmu ba su so, sun gwammace su ci gaba da zama cikin ukuba a kullum. Wannan shi ne dalilin. Dukkan mutanen da suka ce Obasanjo ya fito ya yi mulki a fadin kasar nan, ba mutum daya da zai iya kawo akwatin kofar gidansa. Dukkansu wadanda suke zagaye da Obasanjon suke wannan kamfen na kawo shi ne da kuma wannan na maganar ta-zarce din da cewa ana kaunar sa da cewa abubuwan da yake yi daidai suke. A fada min mutum daya da zai iya kawo akwatin kofar gidansa. Wannan ya tabbatar da cewa mutane ba su tare da shi, ba kaunarsa suke yi ba. Amma saboda wani munafinci da ya fito yake cewa ga abin da yake so, idan Obasanjo ya yi kaza sai a ce daidai ne, shi ne ya sa aka yi shiru aka kyale shi yake ci gaba da abin da yake yi.

OBASANJO BAI CANZA DAGA YADDA NA SAN SHI BA

Bari na gaya maka wani abu, akwai wani mawaki da yake cewa; “mai hali ba ya barin halinsa, ko za a kashe shi,” ya ce, “ran da kuwa mai hali ya bar halinsa, to ba halinsa ba ne.” Obasanjo tun fil’azal haka yake, har ya zuwa yau bai canza ba. Halinsa tun na da din har yanzu shi ne. Na daya, Obasanjo ba imani gare shi ba, ka fada wa kowa, ni na fadi haka. Maketaci ne, wanda ka ga dai jinsin jama’arsa sun nuna masa rashin kauna, kai ka tabbatar da cewa ba mutumin kirki bane. Me ya sa Yarabawan da ke a Kudu maso yamman ba su fito da Obasanjo ba a matsayin dan takararsu, sai mutanen Arewa? Su ma don ba su san shi bane.

Idan kana so sai na fada maka asalin dalilin da ya sa Obasanjo ya bar Ijemo a cikin Abeokuta ya koma Otta. Domin hatta gidan da yake zaune a Ijemo akwai mutanen da suka zo suka ce gonar mahaifinsu ce, sai ya kwace duk bolon na ginin da ya yi ya bar masu wurin, aka yi ta tafka shari’a. Ni na sha zuwa kotu saboda wannan shari’ar, mafarin da ya tashi kenan ya koma Otta. Bangaren Legas na Otta a nan ya fara sayen ’yar gayaina aka yi abu kamar na gona, yana sayen wannan gonar ya hada da wannan, ya sayi wannan ya hada da wannan har aka yi gonar Otta. Ina daya daga cikin mutanen da suka fara shiga gonar Otta.

Ina fada maka yawo kafa da kafa muna yi da Obasanjo. Mutumin da jama’arsa ba sa kaunarsa, wani daga waje ne zai je ya kaunace shi, ya fifita shi ya kuma karbu? A karo na farko AD ai duk sun ci jihohinsu, amma da suka ga al’amarin mutanen Arewa wadanda suke da rinjaye suke tafiyar da harkokin kasar nan. Ba mu da wani abu, tattalin arzikinmu ba a gare mu yake ba a nan Arewa, babu abin da muke da shi, ba a dauke mu a bakin komai ba, in ba almajirai ba, bahilai. Fada wa kowa abin da aka dauke mu kenan, duk lokacin da ake so a yi amfani da mu akan zo a yi amfani da karfin da muke da shi a dauka a yi amfani da shi a samu biyan bukata.

Mutanen Yarabawa abin da suka nuna shi ne mutumin Arewa ya jawo masu Obasanjo ya kawo masu, bari su bi Yarima su sha kida. Suka ce bari su bayar da goyon baya ya zama Shugaban kasa. Yau an wayi gari kashi biyu bisa uku na dukkan wani la’alla Manaja ne, ko Darakata, ko Minista, ko babban Sakatare, ko wani babban mukami a gwamnatin Tarayya Bayarabe ne, abin da suka kasance kenan. Don haka yau in mutumin Illela (karshen Arewa) idan ya zama Shugaban kasa, idan ya zo ya fara canza wadannan al’amura domin yana so ya daidaita al’amura babu abin da za a ce sai kabilanci.

Ai ’yan Arewan suna nan aka yi haka. Kuri’a duk wani mai neman mukamin Shugaban kasa ta ’yan Arewa yake bukata, shi ya sa Obasanjo ya ci saboda kuri’ar daga Arewa ta zo. Ka ga bu mu da komai kenan, in ban da siyasa, shugabanci shi kadai aka ajiye wa Arewa, kuma ba don Allah aka ba Arewa wannan shugabancin ba. Saboda mutumnin Arewa shi yake iya karrama bako, amma sauran kabilun kasar nan babu wanda zai kaunace ka, kansa ya sani.

BAN GA AMFANIN JIHOHIN AREWA BA

Mutumin Arewa bisa tawakkali ga Allah sai ya ce kowa nasa ne, ko da kuwa makiyinsa ne, zai dauke shi. Kuma a kwana a tashi wata rana sai ya ce wannan mutumin kirki ne, ya zo ya tafi da shi. A nan Arewa ba mu da kiristoci? Ko dukkanmu Musulmi ne? Ba mu da wasu kabilun da muke zaune da su? Amma saboda imani da muka yi na rungumar juna, wa ya taba jin bakinmu in banda yau da ake so a rarraba mu? Arewa tana dunkule muna ji muna gani aka raba ta ta koma gida hudu, aka sake kasa ta ta koma gida tara, aka mai da ita 12, yau ta koma 19. Cikin 19 ma aka karkasa su zuwa Kananan Hukumomi.

ABIN DA NAKE JI IDAN NA GA OBASANJO

A matsayina na Musulmi ina da imanin da ba zan iya kashe kaina ba don ganin takaici. Don haka na dangana wannan abin a matsayin wata kadara ce daga Ubangiji na tsaya ina kallon ta, sai ran da Allah ya dauki raina. Amma abin takaici ba zai taba karewa ba, illa a ce ni nan a matsayina na dan Adam wanda sauran mutanen Arewa ba su samu biyan bukata, ya zama wajibi ko ta halin kaka mu kau da mutanen da suke yi mana wannan munafurcin a nan Arewa. Don ba su da amfani, ba su san kowa ba daga kawunansu sai ’ya’yansu.

Yanzu ba kaunar ’ya’yan suke ba saboda sata suke su tara dukiya, suna ganin asarar idan sun mutum su bar wa wadannan ’ya’yan, su kuma ’ya’yan suna Allah-Allah uban nasu ya mutu su gada. Don haka idan ma bai mutum ba, daya daga cikin ’ya’yan suke neman su kashe shi. Wadannan mutane ina amfaninsu a cikin jinsin jama’a? Dole mutanen Arewa su dawo su san su mutanen Arewa ne, kuma yadda aka mayar da shi mutumin banza marar amfani ya dawo gida ya zauna daga shi sai kansa. Ya zauna ya yi tunanin ya zama bai san kowa ba daga kansa sai Arewan.

BA ZAN GOYI BAYAN TA-ZARCE BA

Yaya zan yi na goyi bayan abin da ba ya kan ka’ida. Ko Husainina ne na haihuwa ya ce zai yi wannan (neman Obasanjo ya zarce) ba yarda zan yi da shi ba. Ba haka al’amura suke tafiya ba. Ba haka yawan jama’a da suke zaune suka tsara ba. Ya za a yi mutum daya ya zauna ya yi wannan? Gyara tsarin mulki da za a yi, ba don kowa za a yi ba sai don Obasanjo, shi din me? Yadda mahaifiyarsa ta durkusa ta haife shi, haka aka durkusa aka haifi kowa, hasali ma akwai mutanen da ma da suka fi shi martabar haihuwa. Mutum ya ce a ba da goyon baya saboda a zauna lafiya. Meye zaman lafiya? Babu sauran zaman lafiya a kasar nan, babu wanda yake cikin wadata, in ka ji mutum yana ce maka a zauna lafiya, ya tara ne. Don haka don a ce bangare kaza da na kaza sun ba da hadin kai don a zauna lafiya, to a ware mana! Shi kadai ya taba yin Shugaban kasa? Tun kafin a haife shi ake yin shugabancin kasa! Shi din me!? A matsayin wa?

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International