Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1133 ISSN 1595-4474


Rahotannimu

 UN
Kai gwamnatin Siriya kotun duniya:
Faransa ta sha kunya
Hukumar tsaro ta Majalisar dinkin duniya mai wakilan kasashe 40, ta yi wani zama a ranar Alhamis 22-05-2014, na kada kuri'a a kan kai gwamnatin Siriya da kuma 'yan ta'addan kasar da ke yakar kasar, gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya...
Wuyan mai
Za mu hada hannu da gwamnati don magance matsalar man fetur
- Mataimakin Shugaban kungiyar ‘IPMAN’ ta kasa

A kwanakin baya ne uwar kungiyar dillalan man fetur ta kasa, wato IPMAN, ta gudanar da zaben manyan jami’anta na kasa a birnin tarayyar Abuja, inda aka zabi shugabaninta da za su rike mukamai na kasa a kungiyar...

 NAFDAC
Hukumar ‘NAFDAC’ na muhimmantar da rayuwar al’umma
In ji Shugaban Hukumar a jihar Neja

Shugaban Hukumar kula da ingancin magunguna da kayan abinci, NAFDAC, a jihar Neja, Mista Dadi Nantim Mullah ya bayyana yadda Hukumar ke ayyukanta don muhimmantar da rayuwar al’umma, lokacin da yake zantawa da Wakilinmu a ofishinsa da ke Sakatariyar gwamnatin Tarayya da ke Minna, a makon jiya...

Sauran rahotanni


Jawabai da Karatun Shaikh Ibrahim Zakzaky (H): Zakzaky (H)


Bidiyo (H)

Hoton Bidiyo:

Jawabin Sayyid Zakzaky (H) ranar maulidin Sayyada Zahra (SA) a Zariya


Albishirinku

Almizan
Android
Duk mai na'ura ko waya da ke da "Android" yanzu zai iya karanta AlMizan ta na'uran ko wayar tasa.

Mun samar da wannan ne don ku masu karatunmu ku sami saukin duba AlMizan a duk inda kuke, a ko yaushe ta hanyar "Android". Maza ka garzaya "Play Store" a wayar taka ka nemi AlMizan ka sa a wayar taka.


Free counters!



Labaran Harka Islamiyyah

 Fudiyya Zaria Fudiyya Zariya ta yi bikin yaye dalibai 77
A ranar Asabar din nan da ta gabata ne, Madrasatul Fudiyya Zariya ta yi bikin yaye dalibai a bangaren manya da kananan makarantun sakandire, yayin da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya zama babban bako a wajen taron...

Tunatarwa:

Zakzaky (H)

Tare da Sayyid Zakzaky

Dole a saki su Haruna Abbas

Wannan wani bangare ne na jawabin Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) a taron Yaumus Shuhada na ranar Asabar 25 ga Rajab, 1435 a filin Polo kusa da Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya. Ammar Muhammad Rajab ya rubuta mana.

IN DA KOWA ZAI BA DA HAKKIN SHUHADA

Sakamakon ’yan uwa suna gyara kaburburan Shahidai har wasu ma sun fara koyo. To, amma inda mutum zai je sauran duniyar musulmi zai ga cewa, wannan abu ne zaunanne. Ana kyautata makwantan mutane, ana kuma tunawa da su ta nan. To, Shuhada’u ‘khasatan’ da ma dukkan sauran wadanda suka mutu. Amma ‘khasatan’ Shuhada suna da wannan hakkin.

Sannan kuma suna da hakki na kula da iyalansu, ainihin abin da suka bari baya - matansu da ’ya’yansu da iyayensu. Har wala yau, wannan yana dan dada sanyaya rai. Ya dan kwantar da hankalin mutum, ya rika tunawa da nasa. Da zafi mun sani. Da zafi! Da zafi, amma kuma zai dan sa shi ya yi tunanin cewa, ran dansa, bai tafi a kawai ba, insha Allah...




Ra'ayin Almizan

Wakilanmu
Almizan
Sharri Kayan Kwalba!

Babban labarin mujallar Tell News Magazine na ran 17 ga Yun, 2013 No. 24 da aka yi wa kanu: Sabuwar matsalar tsaro: Rawar Gabas ta tsakiya” (New Security Threat: The Middle East Connection), abin damuwa ne. Wani wai shi ANAYOCHUKWU AGBO ne ya rattaba wannan ‘tatsuniyar” da ...muke magana a kai. A takaicen takaitawa, bangaren makalar tasa da aka yi kokarin nuna cewa Harkar Musulunci a Nijeriya da kuma Shugabanta abin girmamawa, ’yan tashin hankali ne masu mummunar manufa, ya nuna yadda marubucin yake dan baranda, wanda bai san abin da yake magana a kai ba...


Daga Gidan Annabta

Tare da Abubakar Abdullahi Almizan

Salati
Ayyukan ban kwana da watan Rajab

SALLAR DAREN ASHIRIN DA HUDU NA RAJAB

Salla raka’a 40, kowace raka’a Fatiha 1, Amanarrasulu 1, Kulhuwallahu 1. Allah zai rubuta wa wanda ya yi wannan Sallar ladar kyawawan ayyuka 1000, Ya kuma goge masa laifuka 1000, Ya daukaka darajarsa sau 1000.

SALLAR DARE NA ASHIRIN DA BIYAR

Salla raka’a 20, kowace raka’a Fatiha 1, Amanar-rasulu…1, Kulhuwallahu 1. Wanda ya yi wannan Sallar, Allah zai tsare shi daga kowace irin musifa. Kuma Allah zai azurta shi da kubuta daga sharrukan duniya da lahira...


Katun

Mutane ke tuttudowa su ji daga bakin da ke fadin gaskiya
Katun
Ba da bindiga muke tara mutane ba


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

    GAYYATA ZUWA BIKIN NISFU SHA'ABAN
    Imam KhomeiniAna sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi bukukuwan NISFU SHA'ABAN na bana wanda za a gudanar kamar haka:

    Rana:
    Juma'a 15 ga Sha'aban 1435

    Lokaci:
    Yamma zuwa dare

    Mai Jawabi: Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

    Wuri:
    Hussainiyyah Bakiyatullah Akwai walimar bukin Nisfu Sha'aban bayan sallolin Magriba da Isha'i.

    Rana:
    Asabar 16 ga Sha'aban 1435
    Jawabin Yaumul Taklif da sallah da yara

    Lokaci:
    Safe zuwa rana

    Mai Jawabi: Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

    Wuri:
    Hussainiyyah Bakiyatullah

    Rana:
    Asabar 16 ga Sha'aban 1435

    Lokaci:
    Yamma zuwa dare

    Gagarumin majalisin mawaka wanda Alh Mustapha Umar Baba Gadon Kaya jai jagoranta

    Wuri:
    Hussainiyyah Bakiyatullah

    Rana:
    Lahadi 17 ga Sha'aban 1435

    Lokaci:
    Safe

    Gasar fareti da Harisawa zasu gabatar
    Mai karbar fareti: Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
    Akwai walimar bukin Nisfu Sha'aban bayan sallolin Magriba da Isha'i.

    Wuri:
    Filin Polo gefen Hussainiyyah Bakiyatullah
    Allah ya ba da ikon halarta


    Labarai cikin hotuna

    Hotunan yaye daliban makarantar Fudiyyah Zaria na bana

    • Saukar Karatu na Fudiyyah ZariaShaikh Zakzaky yana jawabi a wurin bukin
    • Saukar Karatu na Fudiyyah ZariaShaikh Zakzaky da Malam Abdulhamid Bello
    • Saukar Karatu na Fudiyyah ZariaMalam da dalibai a wurin saukar
    • Saukar Karatu na Fudiyyah ZariaYan uwa a wurin bukin
    • Saukar Karatu na Fudiyyah ZariaYanka alkaki a wurin bukin
    • Saukar Karatu na Fudiyyah ZariaSashen yan uwa da suka halarta
    • Saukar Karatu na Fudiyyah ZariaSashen 'Yan Fudiyya mata
    • Saukar Karatu na Fudiyyah ZariaYaran Fudiyyah
    • Saukar Karatu na Fudiyyah ZariaSashen yan uwa maza
    • Saukar Karatu na Fudiyyah ZariaSashen yan uwa mata
    • Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria
    • Saukar Karatu na Fudiyyah ZariaWasu sashen dalibai
    • Saukar Karatu na Fudiyyah ZariaMalaman fudiyyah da wasu dalibai
    Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria1 Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria2 Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria3 Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria4 Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria5 Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria6 Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria7 Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria8 Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria9 Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria10 Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria11 Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria12 Saukar Karatu na Fudiyyah Zaria13
    html5 slider by WOWSlider.com v5.3


Ra'ayoyinku na baya-bayan nan zai bayyana nan gaba kadan...

Tambihi:

Muhammad Sulaiman

Tare da Malam Muhammad Sulaiman Kaduna

Munasabobin watan Sha’aban
Watan Sha’aban shi ne wata na takwas a jerin lissafi na watannin Musulunci 12. Haka nan kuma yana da munasabobi daban-daban. Watan Sha’aban yana da khususiyya na cewa dukkan munasabobin da ke ciki na wiladar (Haihuwar) Ma’asumin ne, ba na wafatinsu ba. Wato babu wani daga cikin Imaman Ahlul-baiti, wanda ruwaya ta zo da rasuwarsa cikin watan...